FREE PAGE 5

638 16 0
                                    

*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*ANYA BAIWA CE?*

             Na

*AMEERA ADAM*
          

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

FREE PAGE 5

   
   Fulani Maryama zuciyarta fes wani shu'umin murmushi tayi har ya bayyana a fili ta ce. "Marka ai ɗana jarumi ne kamar yadda ɗan uwansa salman yake" Jakadiya ce ta fita ta yiwa Sarki albishiri Marka ta fara ƙoƙarin gyara Fulani Zaliha. Har aka gama yiwa Jaririn Fulani Zaliha wanka bai daina tsanyara kuka ba, tana gamawa ta gyarashi sannan ta ce. "Fulani barka da arziki bari na ƙarasa ciki na bar yarima yana bacci kar ya tashi ki samu ki ci abinci ki kwanta ki huta." Fulani Zaliha ta ce. "To na gode Yaya Allah ya huta gajiya" Fulani Maryama ta wuce sashenta.

     Kafin wani lokaci tuni haihuwar Fulani Zaliha ta zaga cikin gidan masarautar, sanƙira bi yake ko ina yana shelar sanar da ƙaruwar da Mai martaba ya samu , cikin lokacin ƙanƙani cikin garin Kano ta samu sakon haihuwar da aka yiwa Sarkin Kano Aminullahi.

    Jaririn Fulani Zaliha tun ranar da aka haifeshi yayi wannan kukan bai ƙara wani kuka da ƙarfi yadda wani zai iya ji ba, Fulani Zaliha bata kawo komai ba saboda wannan ce haihuwarta ta farko kuma bata taɓa kawowa ranta komai ba, tafi alaƙanta haka da yaro ne shi mara rigima saboda wasu jariran basu cika rigima ba. Matan cikin masarauta da sauran bayi tsegungumi sukeyi akan Fulani Maryama na rashin nuna matsanancin kishinta akan ɗan Fulani Zaliha duk da yadda  kowa yasan Fulani Maryama da matsanancin kishi. Fulani Zaliha ba ta shan wahalar rainon Jaririnta dukda akwai masu kula dashi amma sam bashi da rigima. Tun daga ranar kuma Fulani bata ƙara takawa ta leƙa saahen Fulani Zaliha ba har sai da yayi kwana uku, da wata yammacin ranar ta shirya cikin shiga ta alfarma irin ta jiƙaƙƙun matan sarakuna, tafe take cikin takun ƙasaita da taƙama kamar ba zata taka ƙasa ba. Ga duk wanda yayi arba da Fulani Maryama kallo ɗaya zai mata ya tabbatar  da ita ɗin tabbas jinin masarauta ce gaba da baya, duk yadda ka kai ga kallan ƙurulla zai yi wuya ku haɗa ido da ita batare da janye idanuwanka ba kuma duk sanka da ka fahimci a wane yanayi take zaiyi wuya ka fahimci halin da take ciki. Tana tafe kunyangarta na biye da ita da Salman a hannu har suka ƙarasa sashen Fulani Zaliha, lokacin da ta shiga sashen Fulani Zaliha na zaune tayi kwalliyar ta fito shar da ita ga wani kyau da ta ƙarayi irin na masu jego, Fulani Maryama zama tayi kan lallausar shimfiɗar Fulani Zaliha baiwar ta tsaya daga rumfa.Da fara'arta Fulani Zaliha ta ce, "Barka da shigowa Yaya da fatan kin wuni lafiya ya kwanan Yarima" Fulani Maryama wani murmushi tayi mai wuyar fasaltuwa ta ce. "Lafiya kalau masu jego ya kwanan ɗannawa" Fulani Zaliha kunya taji bata amsa ba ta ƙwalawa baiwarta kira tana bata umarnin kawo Jaririn, a fakaice Fulani Maryama take ƙarewa Fulani Zaliha kallo tana ƙara jin wata irin tsanarta a zuciyarta.

   Lokacin da aka kawo mata Jaririn karɓar sa tayi tana murmushi sai dai ƙasan zuciyarta har wani zafi take ji saboda yadda taga kamaninsa dana Mai martaba na ƙara fitowa, a fili ta shafa fuskarsa ta ce. "A jinjira baƙwan duniya yana rigima kuwa?" Fulani Zaliha ta ce, "Tun kukan farko da yayi bai ƙarayi ba bashi da rigima" Fulani Maryama na shirin yin magana taga hawaye na gangarowa daga idanuwansa, buɗe baki yakeyi yana ɗan juya kansa wanda yake nuna yunwa yake ji, Fulani Maryama murmushi tayi me sauti ta ce. "Ai dama bazai yi ba indai ya biyo gida kinsan Yarima ma haka nayi goyonsa, ungoshi naga kamar yunwa yake ji" a kunyace Fulani Zaliha ta karɓeshi miƙewa Fulani Maryama tayi tayi mata sallama zata wuce har ta je bakin ƙofa ta juyo ta ce. "Sai fa kinsa ido akansa saboda ɓoyayyun maƙiya duk yadda kika kai ga ganosu sai kin gaza a masarautar nan dan haka ki bi sannu" murmushi Fulani Zaliha tayi ta ce, "In sha Allah Yaya kinsan zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi" Fulani Zaliha zuciyarta ɗaya ta faɗi haka ita kuwa Fulani Maryama juyowa tayi amma sai ta wayence da murmushi ɗauke a fuskarta ta ce. "Kinyi gaskiya kuma nasan da haka amma duk da haka tsugunne bata ƙare miki ba amma fa shawara ce na baki." tana kaiwa nan ta fice daga ɗakin.

  Tun daga ranar Fulani Maryama bata ƙara shiga sashen Fulani Zaliha ba, kuma zuciyarta fes ta fita daga ɗakin saboda yadda da dukkan alama haƙanta ya cimma ruwa. Shirye-shirye ake ta gudanarwa na shagalin suna daga sassan ɓangarori na cikin masarautar. Ranar suna Mai martaba ya raɗawa Jariri sunan Saifullah suna kiransa da Saif, anyi shagali sosai ɓaki daga garuruwa suka kawo ziyara wajen taya Mai Martaba murnar samu Ɗa namiji a karo na biyu.

     Anyi taron suna angama lafiya kuma daga ɓangaren Mejego da jaririnta suna cikin ƙoshin lafiya. Bayan wata uku Mai Martaba ne zaune a fada shi da Waziri, ga duk wanda ya dubi yanayim Mai Martaba zai fahimci tsantsar damuwar da yake ciki, amma da yake namiji ne jajirtacce farat ɗaya bazaka fahimci ainihin yanayin da yake cikin ba. Waziri ya ɗuƙar da kai cikin sigar girmamawa yace. "Allah ya taimaki takawa ya ƙarawa Sarki lafiya, Muna zaune aka aika da saƙon kiranmu" Sarki Aminullah ya jinjina kai sannan ya ce.

    "Waziri wani abu yana damunmu kuma babu wanda muka aminta da mu tattauna dashi sai kai" Waziri ya ɗago yace. "Wannan haka haka yake" Sarki yace. "Mun lura da yaron wajen Zaliha kamar bashi da wadatacciyar lafiya, kuma na lura da yanayin Mahaifiyarsa ita kanta ta fahimci haka sai da tana shakkun sanar dani. Waziri ina san maganar nan ta zama sirrin saboda kunnuwa da idanun Fada suna bibiyar halin da ake ciki, banasan a fuskanci halin da yaron nan yake ciki inasan ka nemo min mai magani a sirrance ta yadda babu wanda zai fahimci halin da ake ciki."

  Waziri ya numfasa yace. "Allah ƙadiran alamanyasha'u gaskiya akwai matsala babba dukda kasancewar ba shine Yarima ba, amma sirrantawar yana da matuƙar fa'ida. A cen garin Zaria akwai wani mai magani dana sani yana bada magunguna sosai, dan haka insha Allah zan shirya naje na karɓo maganin sai a jarraba da ikon Allah za'a dace." Mai Martaba yace. "Waziri me zai hana ya gayyato mana mai magnin ina ganin kamar hakan zaifi" Waziri yace, "Duk yadda kace haka za'a aiwatar da kai da kaya duk mallakar wuya ne" Mai Martaba yace. "A shirya tafiya gobe aje a gayyato mana shi" Waziri ya amsa daga nan ya fice daga fadar."

    Da daddare Fulani Zaliha ce zaune a turakar Sarki ta zuba uban tagumi, Sarki Aminullahi ya kalleta yace."Me yake damunki Zaliha" idanunta ne suka ciko da ƙwalla  muryarta na rawa ta ce. "Mai martaba Saif ne nake lura da yanayinsa bashi da ƙosasshiyar lafiya, na lura fa ko gani kamar ba ya yi, gashi har yanzu kansa baya tsaiwa hatta irin gwarancin yarannan banji yana yi ba, abu ɗaya kawai nasan yanayi idan na kira sunansa zan ga yana ɗan motsawa." Fulani Zaliha na kawo nan a zancenta ta rushe da kuka. Rungumeta yayi ajikinsa tsam kamar wani zai ƙwaceta ya fara rarrashinta, yana buga bayanta harta lafa da kukan sannan yace. "Ina lura da halin da kike ciki kuma na fahimci duk abinda kika gayamun, dan haka na aika a kira mai magani a sirrance inasan ki zama jaruma karki bari magauta su ga kukanki, Insha Allah Saif zai samu lafiya ki kwantar da hankalinki." Haka dai Sarki yayi da lallashin Fulani Zaliha har ta sauko ta daina kuka.

    Bayan kwana biyu Mai magani suka ƙarasa ta ƙofar baya suka ƙaraso ɗakin sirri wacce take bayan gari, Saif na hannun Mai martaba mai maganin ya shigo hannunsa ɗauke da wata jakar fata ta magunguna, yana zuwa ya ƙurawa Saif kallo nan take ya fara tsanyara wani irin kuka, jinjina kai yayi ya ce. "Tabbas ancutar da shi da guba mai tsanani sai dai zan iya taimaka muku da yardar Allah koda kuwa bazai warke gabaɗaya ba." Mai maganin kwance jakarsa ya farayi nan take ya dafe ƙirjinsa ya fara wani irin kakari kafin wani lokaci ya yanke jiki ya faɗi ƙasa matacce.

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

ANYA BAIWA CE?Where stories live. Discover now