FREE PAGE 6

625 14 0
                                    

*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*ANYA BAIWA CE?*

             Na

*AMEERA ADAM*
          

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

FREE PAGE 6

     Hankali a tashe Waziri da Mai martaba suka kalli juna ganin abinda ya faru da mai magani, ƙanin Mai maganin da ke gefe da sauri ya faɗa kan ɗan uwansa yana kuka, Mai Martaba cikin al'ajabi haɗe da tashin hankali ya kalli Waziri yace. "Waziri a ji da bawan Allahn  nan bamasan a tara mana jama'a,  ashirya tafiya ƙasar Zazzau a sirrance batare da wasu sun sani ba, zan aiko da takarda akaiwa da iyalansa tare da kyautuka masu yawa." Yana gama faɗa ya juya ya fita ta ƙofar baya cikin jimami" Lokacin da Mai martaba ya ƙarasa cikin turakarsa dare yayi sosai babu komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabbobi, Fulani Zaliha na tsaye sai safa da marwa take yi da ka ga yanayinta zaka fahimci tana cikin damuwa, tana jin motsin Mai Martaba da sauri ta ƙarasa ta tarbeshi gabanta sai faɗuwa yake tunaninta ɗaya wacce amsa Mai martaba zai bata.

  Ganin Mai martaba tayi ya shigo cikin shigar da yayi ta ɓadda kama, sanye yake da kayan bayi fuskarsa naɗe da rawani sai Saif dake rungume a ƙirjinsa, har kusan gware sukayi da Fulani Zaliha ta ɗan ja da baya tana kallan yanayinsa, a hankali ya taka kan lallausar shinfiɗarsa ya zauna yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Fulani Zaliha zama tayi a gefensa ta ƙarɓi Saif dake hannun Sarki Aminullah yana shan ɗan yatsansa, kallan ɗan nata take zuciya a karye ta ce. "Allah ya taimakeka har dace ba ko?" Sarki Aminullah yace. "Mai maganin Allah yayi masa rasuwa" a hargitse ta ɗago tana kallansa bakinta na rawa ta ce.

   "Mai Martaba ɗazu kace Mai maganin yana ɗakin sirri yana jiranka" Sarki Aminullah yace. "Zaliha lamarin Ubangiji yafi gaban komai, yana gabda haɗa magunguna Allah ya karɓi rayuwarsa." Fulani Zaliha ta jinjina kai ta ce. "Allah ya fimu sanin dalilin faruwar haka. Amma gani nake larurar Saif anya babu sihiri a ciki?" Kallan da Sarki Aminullah ya yi mata ne yasa ta haɗiye wani yawu tana sunkuyar da kai ƙasa ta ce.

  "Allah ya huci zuciyar  Takawa a gafarceni ban faɗi haka saboda ɓacin ranka ba" Sarki Aminullah yace. "Zaliha karna ƙara jin makamanciyar irin wannan maganar daga bakinki, kina nufin yafi ƙarfin Ubangiji ya jarrabceshi da wani ciwo ne? Karki bari shaiɗan yayi tasiri a zuciyarki har ya kaiga kin fara zargin abinda ba haka bane" Fulani Zaliha kukan da take ɓoyewa ne ya ƙwace mata, wani irin kuka take me tsuma zuciya Mai martaba jin kukanta yake har cikin zuciyarsa, takowa yayi a hankali ya karɓi Saif ya kwantar da shi sannan ya rungumeta yana lallashinta, sai da ya ga ta tsagaita da kukan sannan yace.

   "Zaliha dole na gaya miki gaskiya koda bazata miki daɗi ba saboda gujewa faɗawa ga halaka, zato a musulunci haramin koda ya kasance gaskiya abinda nake so da ke ki cigaba da kai kukanki gurun Ubangiji, shi zai magance mana duk abinda yake damunki, karki nufi kowa da sharri sai kiga Allah ya kare ki duk wanda ma ya nufe ki da shi koda yana nasara wata rana mugun abinsa zai koma kansa saboda ramin ƙarya ƙurarre ne. Allah ya fimu sanin dai-dai amma ni bana zargin akwai wanda zai iya cutar da abinda kika haifa a cikin masarautar nan, ki riƙi ibada kamar yadda nasanki da ita Allah zai kawo mana waraka cikin ƙudurarsa." Fulani Zaliha goge hawaye tayi tana gyaɗa kai Sarki Aminullah ya cigaba da kwantar mata da hankali.

    Fulani Maryama banda zarya babu abinda take yi a soron baya cikin shigarta ta baɗɗa kama, motsin tafiya taji da sauri ta matsa cen kusurwar bango ta maƙale kamar ba kowa a gurin. Shigowa yayi yana ɗan dube-dube murya ƙasa-ƙasa yace. "Allah ya taimakeki" da sauri Fulani Maryama ta fito ta ce, "Ya ake ciki Ɓoyayyiyar Fuska?" Mutumin yayi murmushi mai sauti yace. "Allah ya taimakeki tabbas kin tabbata murucin kan dutse baki fito ba sai da kika shirya, tuni ya riga da ya mutu har lahira" Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce. "Lallai ka tabbata lumbu-lumbu wutar ƙaiƙayi" Mutumin da take kira da ɓoyayyiyar fuska yace. "Ya gara ta kanyi da dutse..." Fulani Maryama tayi dariya mai tsauti ta ce. "Sai kallo, kallonma daga nesa" suka bushe da dariya lokaci ɗaya, Fulani Maryama ta sunkuyo ta ce. "Kasan idanun Masarauta na lura da shige da fice sai wani lokaci idan mun ƙara haɗuwa" tana faɗar haka ta juya fice ta ƙofar baya.

    Tun daga ranar Mai martaba  ya cigaba da neman masu magani amma wani abun damuwa duk wanda aka ɗauko sai dai ya faɗi take ya mutu, wani kuma a ranar da aka shirya za'a gurinsa za'a je a samu labarin ya mutu ko kuma ya kwanta matsananciyar jinya. Tun Mai martaba bai fara damuwa ba har abun ya fara damunsa, daga ɓangaren Fulani Zaliha duk ta rame saboda damuwa. Sarki Aminullahi tun yana neman masu magunguna a ɓoye har ya fara nema a fili, masu magunguna daga sassan garuruwa suke zuwa domin kawo nasu maganin amma babu nasara, nasara ɗaya aka samu masu Maganin sun daina mutuwa sai dai idan sunzo babu wani canji da ake samu daga jikin Saif. Haka aka dinga tsegungumi a cikin masarautar musamman yadda mutane suka lura da yadda Sarki Aminullahi ya ɗora soyayya akan Saif. Hakan ba ƙaramin ɓatawa Fulani Maryama rai yayi ba da sauran Matan Sarki Aminullah, sai dai su basu wani damu sosai ba dan sun san har abada babu shi babu karagar mulki.

   Haka aka cigaba da tafiya har Saif ya shekara guda a duniya amma ko zama bayayi, hatta kwanciya sai Mahaifiyarsa ta juyashi, Fulani Zaliha ta riga da ta tabbatar da Saif baya gani sai dai ji da kunne tana yi masa magana take fara jujjuyawa, har zuwa wannan lokacin Sarki Aminullah bai ƙosa da nemawa Saif magani ba amma babu wata nasara ko cigaba da ake samu.

   Jakadiya ce ɗurƙushe gaban Fulani ta ce. "Barka da hutawa giwar mata uwar Yarima hasken talakawa, an aika kina nemana" Fulani Maryama cikin Isa da ƙasaita ta ce. "Yau zamu kaiwa Marduska ziyara" A firgice Jakadiya ta ɗago tana kallan Fulani Maryama amma ta kasa furta koda kalma ɗaya ne" Fulani Maryama ta cigaba da cewa.

   "A yanzu nake san zuwa basai anjima ba" bata saurare ta ba ta wuce cikin ɗaki ta ɗauko Yarima Salma ta miƙa mata tace. "Zamu je domin biyan buƙatata ina ƙara jan kunnenki Jakadiya bakinki ƙanin ƙafarki ina tausaya miki azabar da zan aiwatar miki muddin sirrina ya fito daga bakinki" wuri ta miƙa mata sannan ta fara ambatar kalmomin da Boka Mardusk ya bata ta dinga ambata aduk lokacin da take san ziyartarsa.

     Durƙushe suke gaban Boka Marduska ya kalleta sannan ya wage ƙaton bakinsa yana ɓaɓɓaka dariya bakyan gani sannan ya ce. "Maryama buƙatarki ta biya" Kin fito da ƙudurun a juyar da hankalin Sarki daga kan Zaliha da Ɗanta Saif ko?" Fulani Maryama ta gyaɗa kai Boka Marduska yace. "Wannan dai ta biya sai dai wata buƙatar kuma" Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce. "Tsafi ya dafa ka daɗe kayi ƙarko irin na dabino, hatsabibancinka ya dauwama har ƙarshen duniya" tana rufe baki ta ɗire masa jakar kuɗin da ta taho dasu sannan suka miƙe zasu tafi har sunje bakin Ƙofa yace. "Sai dai kiyi haƙuri Maryama wannan karan makusancinki zamu ɗauka a tukwicinmu lamarin bazai miki daɗi ba." Yana rufe baki ya ɓace daga gurin gabaɗaya.

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

ANYA BAIWA CE?Where stories live. Discover now