FREE PAGE 7

642 12 4
                                    

*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*ANYA BAIWA CE?*

             Na

*AMEERA ADAM*
          

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

   FREE PAGE 7

      Wani abu ne ya tsargawa Fulani Maryama tun daga tafin ƙafarta har tsakiyar kanta nan take jikinta yayi sanyi, a sanyaye ta kalli Jakadiya murya a raunace ta ce. "Jakadiya ina jin tsoron wanda Boka Marduska zai ɗauka, tsoro nake kar wani mummunan abu ya faru da Yarima Salman" Jakadiya cikin zuciyarta ta ce. "Ya rabbi samawati kasa jinin Salman ne tukuwicin da Boka zai ɗauka, yooo dama duk wanda ya sayi rariya ai yasan zata zubda ruwa" jin Jakadiya tayi shiru yasa Fulani Maryama ta ce.

   "Jakadiya magana nake fa kina ji na" Jakadiya ta sauya fasalin fuskarta zuwa yanayin damuwa ta ce. "Allah ya taimakeki ba dan kar kalamaina za suyi kaushi ba da nace ki gaggauta yin istigifari saboda Salman Kainuwa ne dashen Allah, domin Jelar raƙumi tayi nesa da ƙasa babu wanda ya isa ya cutar da Salman da yardar Allah shine Sarki me jiran gado." Fulani Maryama ajiyar zuciya ta ce. "Jakadiya shiyasa duk cikin masarauta babu wacce nake ƙauna kamar ke saboda ke kike kwantar mun da hankali a duk lokacin dana tsinci kaina a wani hali" tana gama faɗar haka ta fara karanta kalaman data saba sannan suka koma masarautarsu.

    Washegari da asubar fari saƙo ya iso musu daga Masarautar Gombe na  rasuwar Mahaifin Fulani Maryama wanda shi kaɗai ya rage mata a duniya, Dattijon arziƙi ne shekarunsa Tamanin da bakwai. Jam'ar ƙasar Gombe ba ƙaramin jimami sukayi ba na rashin adalin Sarkinsu marigayi Sarki Abdullahi bn Abdurrahman, lokacin da Mai martaba Sarki Aminullah ya samu wannan saƙon ba ƙaramin jimami yayi ba, tunaninsa ɗaya yadda zai sanarwa da Fulani Maryama rashin mahaifinta musamman da ya tuna yadda take matuƙar ƙaunarsa.
     Fulani Maryama tun da gari ya waye ta ga Salma cikin ƙoshin lafiya damuwarta ta lafa amma a daren ranar ko baccin kirki batayi ba, saboda fargabar abinda zai faru batasan waye Boka zai ɗauka daga cikin ahalinta ba. Tana zaune Yarima Salman na ta ƴan wasanninsa Jakadiya ta shigo da sallama, ga wanda zai ƙarewa Jakadiya kallon tsaf zai fahimci tana cikin farinciki tana shiga ta sauya fasalin fuskarta cikin damuwa ta durƙusa ta ce. "Barka da kyakkyawar safiya uwar gijiyata Mai martaba ya umarceni da sanar dake yana jiranki a turakarsa." Buɗe ido Fulani Maryama tayi da mamakin kiran da Sarki yake mata ta ce. "Jakadiya kinji sabon labari ne?" Jakadiya a zuciyarta ta ce. "Mugun labari ma kuwa amma idan kinje kyaji da kanki" a fili Jakadiya ta ce. "Ranki shi daɗe babu wani sabon labari da ya iso fada a wayewar garin nan"

   Fulani Maryama miƙewa tayi gabanta na faɗuwa ta wuce har taje bakin ƙofa ta juyo ta ce. "Ki kira Binto ta kula mun da Yarima ina dawowa" Fulani Maryama bata jira cewar Jakadiya ba ta fice. Jakadiya ta bi bayanta da wulaƙantaccen kallo a hankali ta ce. "Fulani Maryam kenan ai duk wanda ya sayi tsintsiya yasan zatayi shara da sannu zaki fara girbar abinda kika shuka" ta ƙarasa gaban Yarima Salman ta waiga hagu da dama sannan ta dungure masa kai ta ce. "Kai kuma Falalu sai zare idanu kake kana fala-fala da kunnuwa, ko waɗannan fatalin kunnuwan naka ya isa a gane basu da alaƙa da Mai martaba." tana jin ya fara kuka ta ɗauke shi tana cewa. "Yarima babban gwarzo badai ƙyuya kake ba ke Bintoto zo maza Fulani Maryama ta tafi gurin takawa" bata rufe baki ba sai ga Baiwar ta shigo da sauri, Jakadiya cikin masifa ta ce. "Ke dalla ki dinga nutsuwa yarinya sai rawar kai kamar taci sadakar miji." Jakadiya dangwara mata Yarima tayi ta miƙe ta ce. "To gashinan ki kula da shi dama aikinki ne ni kinga wucewa ta"

     Fulani Maryama zaune ta samu Sarki bayan ta gaisheshi ya amsa sannan yace. "Maryama kinsan dukkan mu daga gurin Ubangiji muke kuma gurinsa zamu koma, yarda da ƙaddara me kyau da marar kyau wajibi ne ga duk musulmin ƙwarai kuma duk wanda kikaji anwayi gari da mutuwarsa to Ubangiji ya fi mu ƙaunarsa shiyasa ya ɗauke bawansa." Fulani Maryama ta gyaɗa kai  jiki a sanyaye Sarki Aminullah ya cigaba da cewa."A ɗazu aka aiko ɗan aike daga ƙasar Gombe cewa Allah ya yiwa Mai martaba rasuwa, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa Ubangiji ya kyauta namu zuwan" Tun Sarki Aminullah bai rufe baki ba Fulani Maryama ta rushe da matsanancin kuka, ana cikin haka sauran Matan sarki suka ƙaraso ganin yanayin da Fulani Maryama take ciki ya sanyaya jikinsu. Zama sukayi cikin ladabi suka gaida shi sannan ya ci gaba da cewa.

ANYA BAIWA CE?Where stories live. Discover now