LAST FREE PAGES

1.1K 21 4
                                    

*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*ANYA BAIWA CE?*

             Na

*AMEERA ADAM*
          

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

   LAST FREE PAGE 10

      Jiki a sanyaye Sarki Aminullah ya ƙara leƙawa harabar gurin amma babu ita babu alamarta, gyara tsayuwa ya yi ya furta, "Rayzuta? Wace me tsaurin idon Baiwa  ce har za ta shigo cikin fadata ta ɗauke abinda zansa a baki na, ina masu gadin bakin ƙofar?" Sai a lokacin ya tuno da dogarawan gurin yana dubawa gefe da gefe ya hangosu a kwkkwance da alama babu me motsi a cikinsu. Tsoro ne ya fara kama shi da sauri ya ƙarasa gurin ya fara tattaɓasu yana kiran sunayensu, daga cen gefe Harisu ne ya fara motsawa yana jin muryar Mai Martaba ya miƙe a zabure yana rissina masa. Sarki Aminullah ya taka a hankali ya matsa gurin Harisu yace.

    "Harisu me ya faru daku haka? Harisu ɗan jim yayi kamar me nazari sannan yace. "Allah ya taimakeka na tuna, muna tsaye wata Baiwa me sanye da kayan bayi ta ƙaraso gurinmu kai tsaye ta tunkari ƙofar shiga turakarta, muna ƙoƙarin hanata ta hankaɗe mu gefe nidai daga haka ban ƙara sanin abinda yake faruwa ba." Ajiyar zuciya Sarki Aminullah ya sauke ya waiga gefe da gefe sannan ya ƙarasa gurin Harisu har sai da ya kai dabda kunnensa  sannan yace. "Harisu ka bamu hankalinka nan bama san shiririta ko shirme, musan ka  bincika muna a cikin bayi mata wacece RAYZUTA? musa san ayi binciken cikin sirri ko ƴan uwanka dogarawa banasan su samu wannnan labarin, idan har labarin ya fita ranka zaiyi mummunan ɓaci" Harisu cikin girmamawa ya rissina yace. "In sha Allah zan ayi yadda kace Mai martaba Allah ya ƙara nisan kwana da jinkiri mai amfani" Sarki Aminullah takawa yayi ya koma cikin turakarsa. Harisu ne ya dinga bin ƴan uwansa yana yayyafa musu ruwa sannan suka miƙe kowanne yana mamakin abin da ya faru.

     Rayzuta kai tsaye tana barin gurin bata tsaya ko ina ba sai hanyar dajin nan wajen bishiyoyin kukar nan guda biyu, tana zuwa ta nemi guri ta zauna tana ƙarewa ƙwaryar fura da nonon kallo. A hankali ta dinga sa ɗan yatsanta tana tsince gubar da ke cikin furar, tana nan zaune ta hanyo wasu ayarin mutane suna tunkaro ta a hankali ta fara ja da baya suna ƙara tunkarota, tana niyyar yunƙurin guduwa suka cimmata da sauri suka fara zagaye suna faɗin wasu irin kalmomi da bata fahimtarsu, russunawa suke alamun girmamawa suna ci gaba da zagaye ta wani namiji ta gani ya ƙaraso gurinta har lokacin bata gane fuskar ko waye ba, zuwa yayi ya tsaya a kusa da ita yana murmushi tare da shafa fuskarta bata yi aune ba taji ya haɗa bakinta na shi sai a lokacin ta ga fuskarsa, suna cikin wannan yanayin taji an fisgi hannunta da ƙarfin gaske. A tsorace suka juya ita da matashin da ke rungume da ita cikin mamaki haɗe da tsoro, cikin izza ya ƙarasa gurin ta ya fisgi hannunta ya fara ƙoƙarin  rungumeta da ƙarfin tsiya tana gocewa. Matashin yana  ganin haka ya ƙaraso da gudu zai janyeta da sauri wancen matashin ya zaro wuƙa ya yanke shi a hannu. Hannu ta fara miƙa masa alamar ya ceci rayuwarta shima ya fara ƙoƙarin miƙa mata hannu dukda jinin da ke zuba a hannunsa. Ɗagowa tayi cikin kukan ta ce. "Furzan karka bari yayi nasara akanka kafin sanin ko waye shi dan Allah ka ceceni daga gurinsa, idan ba haka ba zan kashe kaina gwara na mutu da rayuwa da wannan" da sauri matashin ya miƙa hannunsa da niyyar cetonta amma wancen ya ƙara saka masa wuƙa a tafin hannunsa, a hankali ya sulale ƙasa ya faɗi jini na fita daga jikinsa.

      Ana cikin haka Suka hango wani ya ƙaraso gurin ya fisgi hannunta ta ƙarfin tsiya ya wuce da ita cen cikin surƙuƙin dajin ba tare da waɗancen samarin sun iya aiwatar da wani abu ba, sai ma ganin wani ayarin tayi sun rufe Furzan da duka, tana riƙe a hannunsa ta fara ƙwala ihu tana cewa. "Furzaaaaan! Furzaaaaan dan Allah kazo ka ceci rayuwa ta."

ANYA BAIWA CE?Where stories live. Discover now