FREE PAGE 4

681 15 1
                                    

*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*ANYA BAIWA CE?*

             Na

*AMEERA ADAM*
          

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

FREE PAGE 4

     Fulani taɓe baki tayi ta ce, " Yayi miki kyau ai kowa rai ya yiwa daɗi baya mai shi ba, magana ta ƙarshe da zan gaya miki, kiji ki ƙi ji ki gani ki ƙi gani, zaki iya tafiya " tana gama faɗar haka ta juya ta shige ciki ta bar Jakadiya a tsaye.

       Jakadiya bin bayanta tayi da harara sannan ta juyo ta fi ce daga sashen Fulani Maryama ta wuce cen sashen su.

      Washe gari tun Asubar fari Lantana ta ƙaraso ɗakin Jakadiya hankali tashe tana kwala mata kira tana bubbuga ƙofar, kasancewar bacci bai ishi Jakadiya ba taji haushin tashin da Lantana ta yi mata, cikin masifa ta fara magana, " Ke Lantan wannan kiran mafarautan da kike mun da farar asubahi na lafiya ne? Sai kace naci na wani ban biya ba, Mtsswwww jaraba kai ko yaushe baka da hutu " ta ƙarasa faɗa tana zare sakatar ƙofar.

     Lantana haushi ne ya fara kamata cikin tsiwa ta ce, " Ke Jakadiya kullin cikin yiwa mutane jaraba kike to kizo kiga abunda Sahura take yi muma farkawa mukayi muka ga tana wani irin abu " gaban Jakadiya ne ya yanke ya faɗi da sauri tayi gaba Lantana na biye da ita.

       Suna shiga suka  samu idanun Sahura sun kakkafe jikinta sai wani irin karkarwa yake bakinta na fitar da dafara, Kuka Jakadiya ta fashe dashi tana rungumo Sahura dake cikin wani hali, lokaci ɗaya taji Sahura na shaƙuwa jikinta ya sandare daga nan numfashin ta ya ɗauke.

       Jakadiya rungume Sahura tayi tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya, sai da tayi mai isarta cikin jimamin rashin jikarta ta fara magana, " Shikenan ni Kubura bani da kowa Sahura ke kaɗai kika rage mun yanxu kema babu ke kin mutu kin barni kaico mutuwa baki mun adalci ba, babu Ƴaƴa babu Jika, Allah ya jiƙanki Sahura "  haka Jakadiya ta dinga surutai da ƙyar aka raba ta da gawar jikarta, ba ƙaramin tausayi Jakadiya ta bawa mutane ba musamman yanda kowa yasan irin ƙaunar da ke tsakaninta da jikar ta ta ɗaya tilo, kafin wani lokaci tuni mutuwar Sahura ta ƙaraɗe cikin gidan, bayan ansallaci Sahura mutane suka shiga sintirin zuwa yiwa Jakadiya gaisuwa.

         Jakadiya ce durƙushe a ɗakin Fulani Maryama har zuwa lokacin hawaye ne kwance a fuskarta, Fulani ce ta fara mata magana, " Jakadiya ya ƙarin haƙuri? " Jakadiya goge kwallar idonta tayi sannan ta ce, " Da godiya Ranki shi daɗe "

      " To Allah jiƙan musulmi, ga wannan ayi sadaka da shi " wata jaka ce ta miƙowa Jakadiya, Jakadiya da tsanar Fulani ta ɗarsu a zuciyarta ji tai kamar bazata karɓa ba, amma gudun kar Fulani Maryama ta ganota yasa ta miƙa hannu biyu ta karɓa tana zabga godiya, zuciyarta a dagule ta fito daga sashen Fulani Maryama.

     Jakadiya haka ta shafe kwanaki bakwai cir bata cin abincin sadakar da akeyi, da yake ma tana cikin jimamin mutuwar ko yunwar bata cika damunta ba inma taji yunwa sai dai ta nemi gasara ta dama kunu ko tayi farau-farau, a duk duniya yanxu babu wacce Jakadiya ta tsana take jin haushin ta sama da Fulani Maryama dan gani take ta sanadin ta ne ta rasa Ƴar jikallenta guda.

  Bayan kwana biyu Fulani Maryama sai saƙa da warwara take a cikin zuciyarta, tana tuna maganganun da Boka ya sanar mata fargabar abin da zai biyo baya.Ta kaɗu sosai da yadda karon farko Boka ya bankaɗo wani muhimmin ɓoyayyen sirrinta, amma data tuna irin tuggun da zata shirya sai ta mayar da komai ba komai ba, ta zubawa sarautar Allah ido tayi da jiran tsammanin lokacin haihuwar Fulani Zaliha. Domin a nan ne zata aiwatar da dukkan ƙudurinta.

   Bayan kwana biyu Mai Martaba na zaune a turakarsa Fulani Maryama na gefe a zaune, ta kalleshi sai dai gabaɗaya baya cikin walwala cikin kissa ta ce. "Mai Martaba  wannan yanayin sam bai kamace ka ba, Allah ƙara lafiya da nisan kwana shugaba kamar kai wannan yanayin bai dace da kai ba, Bango madafar bayi idan har zaka dinga shiga cikin damuwa, to mu da sauran talakawanka ya zamu kasance." Mai martaba cikin damuwa yace. "Wallahi ina yawan yin  mummunan mafarki akan ƙanwarki Zaliha ina yawan mafarki mara kyau akan cikinta" gaban Fulani Maryama ya faɗi ɓaci rai ya sauka a zuciyarta amma da yake ta iya duniyanci sai ta aro damuwa ta yafa a fuskarta ta ce. "Haba taƙamar bayi adalin Sarki mai adalci, ai zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi, ka kwantar da hankalinka Fulani Zaliha zata sauka lafiya tunda alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, nidai a iya sanina Fulani Zaliha tana cikin ƙoshin lafiya kuma zata haife mana ƙanin Yarima lafiya" farinciki ne ƙarara ya bayyana a fuskar Me martaba, janyo hannunta yayi ya sumbaceta yace.

   "Allah ya yi miki albarka Maryama ke ɗin ta daban ce saboda haka kike ƙara birgeni, naji daɗin yadda kika riƙi ƴan uwanki da zuciya ɗaya kuma kika riƙe girman da Allah ya ɗora miki, hakan ne yake sa nake tunanin ko bayan raina zuri'ata zata haɗa kanta." Murmushi  Fulani Maryama tayi ta ce. "Dole ƙanwar naƙi wa ya isa ya ja da abin da Mai Martaba yake so, ai duk abin da ka nuna kana so har bada ina ƙaunarsa"Mai Martaba daɗi yaji sosai yadda take bashi kulawa akan sauran matansa. Cikin zuciyarta Fulani Maryam ta ce. "Da ikon Allah bazai zo duniya lafiya ba mu zuba mu gani"

        *BAYAN WATA UKU*

        Fulani Zaliha ce durƙushe tana naƙuda, gefenta Marka ce sai Jakadiya dake riƙe da ita, daga bakin zaure Shamaki ne yake sallama, da sauri Jakadiya ta fita gurinsa, ƙwarya ce da rubutu aciki ya miƙa mata yana faɗin, " Gashi Takawa ya ce a bata ta sha ashafe cikin da shi " karɓa Jakadiya tayi ta koma ciki ta ɗago kan Fulani Zaliha da ta haɗa uban gumi, a wahalce ta sha bayan ta gama sha aka Shafe cikin da sauran.

     Bankaɗa labulen ɗakin akayi ko sallama babu, Jakadiya na ɗago kai tana shirin masifa suka haɗa ido da Fulani Maryama fuskar nan tata babu annuri, wani tunani Fulani Maryama tayi lokaci ɗaya ta sauya yanayin ta cikin ruɗewa ta ce, " Jakadiya ashe Fulani na kan gwiwa amma ba'a turo ansanar mun ba sai yanxu labari ya je mun " Jakadiya cikin rawar murya ta ce, " Ai wato...Nima zuwa na kenan, na fito zanje wajenki Takawa ya ayko da rubutu "

     Marmushin Markirci Fulani Maryama tayi ta ce, " Bari nazo na riƙeta kije ki kawon garwashi yanxun nan ga ragowar turaren da akamun lokacin naƙudar Yarima " Suna haɗa ido Fulani ta watsawa Jakadiya mugun kallo ba shiri Jakadiya ta fice.
 
    Fulani na shiga ta riƙe Fulani Zaliha tana mata sannu.

      Jakadiya na kawo wuta Fulani Maryama ta kunce turaren wajen boka ta barbaɗa, ba'a jima Jariri ya faɗo yana tsanyara kuka, Fulani Zuwaira da Fulani Bilkisu na kawo kai suka ji kukan jariri, da sauri Fulani Bilkisu ta ce, " Lallai mun shigo a sa'a Barka da arziki " suna shigowa kowa yayi turus saboda ganin Abunda Fulani Zulaiha ta haifo, sai dai kowannen su haɗiye abinda ke ransa yayi gudun kar afuskanci halin da Suke ciki.

           Bayan an yanke mabiyar angyara gun ruwa aka kawo na wankan jariri. Kasancewar Fulani Maryama ita yaro ya faɗo a hannunta ita aka bawa ruwan, fakar idanun su tayi ta damƙi garin gurin boka haɗe da ƙafar jaririn ta sa acikin ruwan wankan.

      Lokacin da garin maganin ya garwaye jikin sa wani irin kuka ya fashe da shi, amma babu wanda ya kawo komai sai ma tsokarsa da Marka ta ke cikin waƙa tana faɗin, " Ka zama Jarumin maza karka zama rago mana matsoraci bashi zama gwani, jinin Aminullahi yafi ƙarfin wasa kyawun ɗan ƙwarai ya gaji ubansa"

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

ANYA BAIWA CE?Kde žijí příběhy. Začni objevovat