*BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad*HASKE WRITERS ASSO..*
SHAFI NA BIYU
ASALINSU
Aliyu Ard'o shine mahaifinsu Bongel, asalinsa d'an garin katsina ne k'aramar hukumar malumfashi, bafullatani ne gaba da bayansa, Mahaifiyarsa Hafsa shi kad'ai ta haifa, Allah ya mata rasuwa, bayan ta rasu ya sake aure, ya auri Hanne ta haifa masa yara biyu maza Bala da Siddiku, Hanne bata k'aunar Aliyu duba da yadda mahaifinsu ke son shi, yake tausayin sa saboda rashin uwa, haka suma su siddiku suka tashi da k'iyayyar sa, duk da Bala na dan' b'oye tasa k'iyayyar, Mahaifinsu ba mai k'arfi bane, manomi ne, da suka isa aure, ya musu k'aramin gini na k'asa, kowannen su yace ya fitar da mata, Aliyu ya fara samun mata,Nene zuwa tallar nono daga rigarsu, suka k'ulla soyayya, bayan shekara d'aya Bala da Sidddiku sukayi aure suma, Bala ya auri fatsuma, Siddiku ya auri Dije, matansu haka suma suka d'arsawa ransu tsananin kishin Nene, duk da irin mugun hali da suke nuna mata, bata bi ta kansu, Bongel ce yar'su ta farko wacce taci sunan kakarta Hafsa, Bappa ya saka mata Bongel saboda kyawunta, kaf yaran gidan babu wanda ya kaita kyau, fari da gashi, Bala nada yara hud'u Hamza, Lawal, Sa'ade, Habiba, Hamma Siddiku nada uku Hassan da Husaini, Saudat, Duka yaran gidan babu wanda ya samu ilimin boko sai Bongel, Bappa nada burin ganin yaran sa sun samu ilimi, sai dai rashi da talauci yasa Bongel kad'ai ya samu sakawa, Siddiku da Bala basu damu a saka yaransu ba a cewar su a boko yaro ke lalacewa, ba irin k'ananun maganganun da basuyi ba kan saka ta makaranta, Bappa ya toshe kunnen sa.
***************
Bongel sun soma zana jarabawar WAEC wacce sam bata wasa da karatu, duk jarabawar data shiga bata jimawa take fitowa saboda sauk'in da take mata, yau ma maths sukayi kusan kowa ka kalla cizon biro yake saboda wahalar da jarabawar tayi, wasu na raba ido ko zasu samu satar amsa, sab'anin Bongel da kanta ke duk'e kan takardarta tana faman calculation, lokaci kad'an ya d'auketa ta kammala ta fito,
Zama tayi bakin hall d'in tana jiran fitowar Asiya, istigafari ta soma kar tayi zaman banza, kusan awa d'aya da zamanta kafin Asiya ta fito, "Bongel nikam wacce irin baiwa ce Allah ya baki, yadda jarabawar nan tayi wahala amma kika kammala da wuri", Murmushi tayi tace "Allah dai ya bamu sa'a", Asiya ta amsa "Amin", Bongel ta mik'e suka tafi hostel.
A kullum safiya da tunanin Bappa, Bongel take tashi haka dashi take bacci, bakinta baya gajiya da rok'ar masa rahamar ubangiji.
Sati shida suka d'auka suka kammala jarabawa, a cikin sati shidan suka zana jamb, wanda Bongel tafi kowa samun sakamako mai kyau a cikin d'aliban makarantar, d'ari uku da sha biyar ta samu, Tayi murna sosai haka duk wani masoyinta ya taya ta murna,
Ranar da suka kammala jarabawa aka sallami kowa gidan iyayen sa, sai sakamako ya fito su dawo su karb'a, kowa ka gani fuska d'auke da farin ciki, ana ta faman rubuce rubuce a rigunan juna, da karb'ar numbobi, sab'anin Bongel data koma gefe tana zaune kan akwatin ta, wannan shine karon farko da bata zumud'in zuwa gida, lokutan baya tun ana saura sati d'aya hutu take soma had'a kayanta tsabar zumud'i, ba wanda tafi muradin gani kamar Bappa dan tarba ta musamman take samu daga gare sa, a ranar raba dare suke suna hira gaba d'ayan su, tana basu labarin makaranta da abubuwan da suka faru,
Ta jima zaune tana jiran zuwan Hamma Bala shiru, har kowa ya fara watsewa, tun fara makarantar bata tab'a kai lokaci kamar haka ba'a zo d'aukarta ba, addu'a ta soma Allah yasa lafiya,
Har kowa ya watse ya barta ita kad'ai, Jikinta ya k'ara yin sanyi tana ji a ranta ba lafiya ba, ta yanke shawarar samun machine ya kaita gida, ba tare da b'ata lokaci ba ta samu machine, ya fad'i kud'in da zata basa, Tace "Idan mun isa gida zan shiga ciki na karb'o maka", Harara ya watsa mata yace "Kinga idan baki da kud'in na tafi abuna", "Wallahi muna zuwa zan shiga na d'auko na baka", "Na sha d'aukar irinku kuna guduwa, dan haka ki nemi wani" Yaja babur d'insa ba tare da ya jira cewar ta ba, Tabi bayansa da kallo cike da takaici,
