*BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad*HASKE WRITERS ASSO...*
HAMSIN DA BIYAR
SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298Haidar ya jima yana muk'urk'usa kafin ya soma jin sha'awar na raguwa a hankali, tsaki yayi cike da takaicin kansa, Ya lumshe idonsa zantukan Bongel na masa yawo a kunne da k'walk'wala " "A ko da yaushe kai ke kawo kanka d'akina, ban tab'a samunka d'akin ka na buk'ace ka ba, hakan kad'ai ya isa shaidar wacece ni, ko a cikin mu wa ke taimakon wani", Nazarin zantukan yake a hankali yayin da zuciyarsa ke jefa masa wani sabon tunani, gaskiya ta fad'a bata tab'a kai kanta garesa ba, haka duk abubuwan da yake shi kad'ai ke yi, ba tare da ta basa goyon baya ba, ko nuna wata alamar cewa a buk'ace take, yadda Rauda ke tafiyar dashi yayin mu'amalar su ko kusa ba haka Bongel ke yi, kwata kwata babu wata alamar dake nuna cewa tana enjoying, Yake zancen zuci shi kad'ai, Kansa yaji ya sara, yayin da tunanin sa ya cunkushe wuri d'aya, Zuciyarsa na son hasko masa wani tunani yana k'ok'arin dakatar da ita,
Shigowar Rauda ya katse tunanin sa, Tazo daf dashi tana cewa "My dear ashe ka dawo", Kai ya gyad'a mata alamar eh, "Ina kitchen muna ta faman girki da Intisar", "Ok" ya fad'a a dak'ile dan sam baya jin dad'in ransa, "Muje kaci abinci ko", "Ba yanzu ba" Ya fad'a yana mik'ewa ya shiga toilet, ya cire kayansa ya sakar ma kansa ruwan shower, Rauda kuwa baki ta tab'e tace "Kome ke damunsa oho", Ta zauna bakin gado tana danna wayarta.
********************
Alhaji Sani rai a matuk'ar b'ace ya dawo gida, ko gaisuwar ma'aikatan sa bai amsa ba, Hajiya Mariya kallo d'aya ta masa tasan ba lafiya ba, Babbar rigar sa ya cire ya cillar gefe, yana zama kan kujera da k'arfi, Cikin nuna damuwa da kulawa Hajiya Mariya tace "Lafiya dai Alhaji", "Ina fa lafiya dan' banzan yaron nan aka ba filayen, wallahi yana shigar mun hanci da yawa, shi ke katange ni ga dukkan burika na, ya zamar mun k'adangaren bakin tulu", Nauyayyen ajiyar zuciya ta sauke fuskarta na nuni da zallar bak'in ciki tace "Tabbas Haidar ya zamar mana ciwon ido, lokaci yayi da ya kamata mu kawo k'arshen komai", "Nima na soma tunanin haka, dan idan bamuyi wasa ba muna ji muna gani zamu tashi a tutar babu", Hajiya Mariya mik'ewa tayi tace "Ina zuwa Alhaji",
D'akinta ta shiga ta d'auki wayarta ta kira Rauda, wayar na hannunta tana chatting, tayi receiving, "Mummy ina wuni?", "Lafiya lau", "Ke kad'ai ce ko kina tare da wani", "Ni kad'ai ce Mummy", "Magunguna dana kawo miki kina amfani dasu kuwa", Sai a lokacin ta tuna ma dan tun ranar farko bata k'ara ba, Baki ta turo tamkar tana gabanta tace "Ranar farko dana saka a abinci saura k'iris asirina ya tonu, turaren ma cewa yayi ina warin yan' bori kar na k'ara amfani dashi, shiyasa na ban k'ara ba", "Ashe baki da hankali da wayo" Hajiya Mariya ta fad'a a tsawace, "Toh ai ni mum....", "Dallah can rufe mun baki shashasha wallahi wurin sakarcin ki kina ji kina gani zaki rasa Haidar", Hawaye ta soma tace "Ki daina cewa zan rasa shi Mummy", "Matuk'ar baki maida hankalin ki wallahi zaki rasa kawai, sakarya kawai", Ta kashe wayar cike da takaici,
Rauda wayar ta cilar kan gado tace "Wallahi ni ba wani magani da zanyi amfani dashi, haka kawai ya rik'a cewa ina warin yan' bori, nasan hanyoyin da zan bi na fitar da ita gidan nan, da mallakar Haidar ni kad'ai, Mummy zaki san ba sakarya bace ni, da kanki zaki jinjina mun" Ta k'arasa da yin shu'umin murmushi.
**********************
Haidar kwana yayi tunani d'aya na Bongel, yayi tsaki yafi a k'irga dan takaicin kansa na tunanin ta, duk iya k'ok'arin sa na yakice tunanin abun yaci tura, haka yayi ta sak'a da warwara har safe.
