*BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad*HASKE WRITERS ASSO...*
SITTIN DA TAKWAS
SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298*BANYI EDITING BA*🥺
Shigowar Irfan yana kuka, ya fargar da Bongel nisan tunanin da ta tafi, ta tashi zaune, ta jawo sa jikinta tana tambayar "Me ya same shi?", "Dada ce tace na shirya a kaini gida", Yaron ya fad'a yana k'ara sautin kukan sa, Ajiyar zuciya ta sauke tace "Kaje gida kaji gobe sai ka dawo", Kafad'a ya mak'e yace "A'ah ni dai tare zamu je dake", Kansa ta shafa tace "Ka zama good boy mai jin magana kaji, yanzu kaje driver ya kai ka gida, gobe sai Daddy ya dawo da kai", Kai yayi nodding rai a jagule, k'aramar leda mai cike da chocolates ta d'auko ta basa, ya karb'a da cewa "Thank you" ya fita, Bongel tabi bayan yaron da kallo cike da tausayi.******************
Rauda kwata kwata bata san da dawowar Haidar ba, sai faman duba agogo take ganin lokacin dawowar sa ya wuce, tayi dukkan shiry na tarbar sa yau ba, dan ta d'auki k'udurin mallake zuciyar sa cikin satin nan, Shigowar Irfan yasa ta mik'e da sauri tana k'ara gyara rigarta ta hanyar bayyanar da dukiyar fulaninta ta sama, Ganin har Irfan ya shigo falon babu Haidar, Tace "Kai ina baban ka?", "Nima ban sani ba", "Kaga dan' iskan yaro mara kunya, ni zaka cewa baka sani ba", Ta k'arasa tana jawo shi da k'arfi, "Ai na d'auka rashin kunya zaka mun, kaje yar' iskar can ta zuga ka", Ta k'arasa tana sakin sa yayi baya zai fad'i, Haidar ya rik'e sa yaron kuka ya saki jin sa jikin baban sa, Mugun kallo yake jifan Rauda dashi wanda yasa hanjin cikinta kad'awa, Cikin rawar murya tace "Uhmm da...ma....", "Enough" Ya fad'a cikin karaji yana d'aga mata hannu,
"Na dad'e da sanin bakya so da tausayin yaron nan, kamar kin manta matsayin sa gare ki, da dangantar dake tsakanin ki da mahaifiyar sa, ko ba Hafsat idan son da kike mun na gaskiya yaci ace Irfan yaci daraja", "Wallahi ba haka bane My dear", Rauda ta fad'a tana marairaice murya, "Bana son jin duk wani bayani da zai fito bakin ki, sai dai ina baki gargad'i ya zama rana ta farko ta k'arshe da zaki k'ara aikata haka gare shi", Ya ja hannun Irfan zuwa d'akin sa, Zuciyarsa tayi rauni tuni irin kulawar da yake samu irin Bongel wacce basu had'a zumuncin komai ba, jini ko d'aya bai tsaga tsakanin su ba, Irfan ya katse tunanin sa da cewa "Meyasa Anty ta koma gidan Dada, please ta dawo nan", Hannun sa ya d'aura kan Irfan yace "Kar ka damu kaji zata dawo", Yaron tsalle murna ya soma, yayin da Haidar ya lumshe idon sa yana tunanin furucin nasa, wanda ya fito kai tsaye daga zuciyar sa.
*********************
Hamma Siddiku yana isa gida, wurin Nene ya fara nufa, tana d'aki kishingid'e suna hira da Ramla cikin nishad'i, ya soma kwara sallama daga bak'in k'ofa, daga muryar tasa suka san ba lafiya ba, Nene mayafinta dake gefe ta yafa, Ta fito waje, Hamma Siddiku bai tsaya tunanin komai ba yace "Kin mana bak'ar haihuwa, haihuwar mugun iri da tsiya, banda tsiya da rashin tarbiya irin na Bongel, aurenta ya mutu amma ta koma ta lik'e gidan surukai, tsabar bad'al da fitsari a gaban idona ta rungume Haidar bayan akwai tsakanin su", "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Nana ke nanata wa, "Addu'ar ki ta banza, bayan ke kika d'aure mata gindin iskanci, bokon da kuka saka ta ai shi kad'ai ya isa lalacewar tarbiyan yaro, shiyasa duka yarana babu wanda zai yi wallahi", Nene bata fasa ambaton Allah ba, Yace "Ki shirya dawowarta gobe, da d'aurin ta da Hisham k'anin mijinta wani sati", A razane Nene ta kalle tace "K'aninsa kuma Hisham", "Ehi shi zata aura wani sati mai zuwa", "Haba Siddiku wannan kwamacala har ina, yaya ya saki, k'ani ya aura", "Bana son maganar kinji, yarinya nine ubanta ni ke da iko da ita, idan kuma rashin ta ido zaki mun toh bismillah", Jin haka Nene tayi shiru tana ambaton sunayen Allah yayin da dukkan gabb'an jikinta suka mutu,
