*BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad*HASKE WRITERS ASSO...*
SABA'IN DA BIYAR
SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298Haidar zaman dirshan yayi ofishin na MTN, basu d'auki lokaci ba suka gano masa location na Bongel tana cikin garin katsina unguwar Gra, Tunanin farko da yazo masa a rai shine wata sani a garin katsina, tana da wasu yan' uwa masu hali ne, D'aya daga cikin ma'aikatan ya katse tunanin sa da cewa "24 street house number 107", Idanu ya zaro jin address na gidan Anty mami, kasa yarda yayi zuciyarsa na basa tabbacin yayi mistake na number, yana kyautata zaton number Anty mami ya bayar ko cikin yaranta, "Please ko zan k'ara ganin number" Ya fad'a, "Yes gata" Cewar ma'aikacin, Haidar ya duba yaga tabbas numberta ce babu kuskure, Ajiyar zuciya ya sauke, Ransa na ayyaana masa kenan shiri ne sukayi da Dada, idan ba haka ba me zai kaita gidan Anty Mami, Yayi musu alkhairi mai yawa kana ya tafi.
*******************
Bongel tun dawowarta makaranta take bacci, bata tashi ba sai ana kiran sallar la'asar, ruwa ta watsa ta saka doguwar riga mara nauyi mai gajeren hannu, tayi parking gashinta, ta saka hula mai neat, gashin ya kwanto ta gaban goshinta ya k'ara mata kyau, vaseline ta shafa kan lips d'inta da bata son ganin sun bushe, ta fesa turare kala biyu marasa k'arfi,
Bata tarar da kowa falon sama ba, haka yasa ta sauka k'asa, Nan ta tarar dasu kowa ya baje, wasu na kallo, wasu na danna waya, Kusa da Intisar ta zauna, Ta dubeta da murmushi tace "Anty sarkin bacci, tun dawowarki school bamu had'u ba", Tayi dariya tace "Wallahi kinsan stress na makaranta", "Hakane, nasa an miki pancake naga shekaranjiy kinci sosai", "Nagode Maman baby" Cewar Bongel yadda taga Intisar na son babyn tun kafin yazo duniya yasa take ce mata haka, "Bara na d'auko miki", Ta fad'a tana mik'ewa, Ta shiga kitchen ta d'auko ta bata,
Bongel plate d'in ta ajiye gabanta tana ci, tana kallo,
****************
Haidar tun da ya tunkaro k'ofar shiga gabansa ke fad'uwa, yayin da rauni da karaya had'i da fargaba suka ziyarci zuciyarsa, idan Bongel bata nan, bai san wata hanya na nemanta ba, bai san ina zai ganta ba, fatan sa da addu'arta ya sameta anan d'in, Jiki babu kuzari ya murd'a handle na k'ofar ya shiga,
K'amshin turaren da tasan mutum d'aya dashi, ta soma ji a hancinta, Haidar kad'ai ta sani da k'amshin, tun zuwanta gidan bata tab'a jin kowa dashi ba balle tayi tunanin wani ne, tsoro da fargaba taji lokaci d'aya sun kamata, kar dai ace shine, tunaninta ya katse jin muryar Farha nacewa "Yaya Haidar ina wuni", Miyau ta had'iya mai k'arfi wanda ya wuce tare da pancake dake bakinta bata shirya ba, "Waya sanar dashi tana nan, ko kuma kawai ziyara ya kawo musu, meyasa ma ta sauko k'asa, bata zauna d'aki abun ta ba" Take zancen zuci,
Sam bai lura da ita ba, kasancewar tana can kujerar k'arshe, haka bai tsammaci ganin nata a falon ba, Intisar data gaishe sa, ya amsa da kai dubansa wurin, Idonsa ya sauka kanta, Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da furta "Hafsah", Har cikin k'wak'walwar kanta sunan nata ya amsa, "Na'am ina wuni?" Ta fad'a ba tare da ta dubesa ba, banda su intisar dake wurin bazata amsa ba, Kasa amsawa yayi sai ido ya kafeta dashi, ganin yadda ta k'ara masa masifar kyau, yana jin tamkar ya rungumota jikinsa ya samu sassaucin abunda yake ji, Meyasa tun tana gidanshi bai gane baiwar da Allah yayi masa, sai a yanzu da take neman sub'uce masa, ya tabbata banda cikinsa dake jikinta, da tuni Dada ta tursasa shi ya bata takardar ta,
