09

1.1K 76 14
                                    

*BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

  *HASKE WRITERS ASSO...*

SHAFI NA TARA

SAFIYAR LITININ

  Yau an tashi da sanyi sosai, garin yayi hazo, daga Bongel har Asiya sanyi yasa sun kasa tashi, bacci mai nauyi ya d'auke su, bayan idar da sallar asuba,

   "Yau ba zakuje makaranta bane, kuka kwanta kuna ta bacci" Bongel cikin bacci taji muryar Mama, Firgigit ta tashi da ambaton sunan Allah, da sauri ta jawo wayar Asiya ta duba lokaci bakwai da rabi, Salati tayi ta sanar da ubangiji tuna yau suna da lecture Haidar, "Zamu je mama, bacci ne ya d'auke mu", Mama ta girgiza kai tace "Tashi Asiya ku shirya ku tafi",

   "Asiya ki tashi, mun makara zuwa school", Mik'a tayi tana murza idonta, Bongel da sauri ta shiga band'aki tayi brush ta wanke fuskarta ta fito bata tsaya wanka ba, tana fitowa Asiya ta shiga itama da sauri ta fito, Bongel nik'ab ta saka dan bata son Haidar ya ganeta, kasancewar yau ma ita mai laifi ce,

  "Allah yasa ya barmu mu shiga" Cewar Asiya, Bongel tace "Amin Ya Hayyu Ya Qayyum" a zuciyarta tana jin yana da matuk'ar wahala.

***************************************

Cikin shirinsa na k'ananun kaya ya fito, yana gyara zaman necktie d'in sa, kayan sun amshi jikinsa sosai, sun masa kyau, ya fito sak boss d'in sa, kallo d'aya zaka masa kasan babu wasa a lamarin sa,

   Hisham ya shigo yana cewa "Yaya Haidar sai munyi sauri, sun kira yanzu sun fito airport", Haidar ya kalli agogon dake d'aure a hannun sa yace "Lokaci ya tafi sosai ashe, muje", Hisham ya juya suna fita tare, Mota d'aya suka shiga zuwa company,

  Sun riga turawan zuwa, wanda suka zo daga london kan business da zasu yi tare dasu Haidar,

  Duk wani mai share a company ya taru a babban d'akin( Meeting hall), Alhaji Sani maigoro sai cika yake yana batsewa, yazo musu da wani sabon salo duk abunda akace sai ya nuna a'ah ko da kowa abun na k'aruwar company ne wanda da ba haka yake ba, ra'ayinsu yana tafiya iri d'aya ne,

  "I think baku shirya ba, zamu tafi mu" Cewar d'aya daga cikin turawan da yaren turanci, Haidar yayi saurin cewa "No mun shirya, decision d'inmu shi za'a d'auka, bana jin bambamcin ra'ayin mutum d'aya zai sa a fasa", Sauran turawan suka ce "Hakane" aka soma tattauna yadda za'a gudanar da kasuwancin, Alhaji Sani maigoro sai faman hararar Haidar yake kamar idonsa zasu fad'o, Haidar bai bi ta kansa ba, balle yasan yana yi, hankalinsa ya tafi kan yadda zasu k'ara bunk'asa kasuwancin su.

**************************************

Bongel da Asiya a tare suka sauke ajiyar zuciya ganin Haidar bai zo ba, "Alhamdulillah Allah ya so mu da rahama", Asiya ta fad'a, Bongel tace "Wallahi Alhamdulillah", Suka shiga ajin, Basu samu seat d'in gaba ba kamar kullum sai na tsakiya, handout d'insu suka fiddo suna karatu, har 8:30 bai zo ba, Bongel a zuciyarta addu'a take Allah yasa kar yazo, bata son ganin shi, dole ce kawai tasa dan yana malamin ta.

*************************************

Awa d'aya ya d'auke su suna meeting d'in, kowa ya watse, Haidar ya fito da sauri zuwa school, ya bud'e murfin motar sa da zumar shiga yaji an tab'o sa ta baya, yana juyowa yaga Alhaji Sani maigoro,


"Haidar Abbas Maishanu har kayi girman da zance abu kace ba haka ba, tsaurin idon naka ya kawo kaina kenan, toh bari kaji ko ubanka bai isa ba, ubanka kansa ba tsarin yi na bane", Haidar zuciyarsa ta soma tafarfasa yana jin mugun b'acin rai na taso masa, Alhaji Sani ya cigaba da cewa "Dan haka ka kiyaye, ko ub....", Haidar ya katse da cewa "Enough! Kar kasa na manta matsayin ka na surukina", bai had'a iyayensa da kowa ba, baya jure yaji ana zagin su, Yana fad'ar haka bai jira cewar Alhaji Sani ba ya  shige mota dan zai iya aikata abunda babu wanda zai je dad'in sa, yaja motar da k'arfi, yana tada k'ura.

BONGEL(COMPLETED)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt