29

1K 106 8
                                    

*BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

*HASKE WRITERS ASSO...*

ASHIRIN DA TARA

_SAFIRA BALA LABARAN, SA'ADATU M YA'U,  MAMAN IDRIS SHAFIN YAU NAKU NE_

Rauda kowacce kusurwa ta falon take bi da kallo, tana yamutsa fuska, kafin ta maido duban ta ga Bongel tace "Nasan baki san ko ni wacece ba", Bongel tayi guntun murmushi tace "K'warai ban sani ba", Rauda ta k'ara gyara zama tace "Masoyiya kuma matar da Haidar zai aura", Bongel sam maganar bata dake ta ba sai ma cewa da tayi "Allah sarki, sannu ko, sai dai baya gida ko bai sanar dake ba ne", Raudah gani tayi Bongel tama raina mata hankali tace "Ina da damar zuwa gidan nan ko yana nan ko baya nan", Asiya ta kama baki tace "Toohh Ikon Allah, mace da biyo saurayi gida", A harzuk'e Rauda tace "Ke stay within ur limit, ko wallahi ki gwammace kid'a da karatu", Asiya tsaki taja tace "Banda asara ka biyo namiji har gidan auren sa", Kalman ta sauka kan kunnen Haidar dake shigowa,

   Rauda ta soma ganin sa, ai tuni ta fashe da kuka, Haidar hannu d'aya ya saka aljihu yana bin kowaccen su da wani shegen kallo, Asiya tuni tasha jinin jikinta dan kwarjinin da ya mata, Bongel gefe d'aya take kallo ba tare da ta nuna alamar tasan da tsayuwar sa ba, duk da k'amshin turaren sa ya sanar mata da zuwan sa,

   Rauda tana kuka tace "Yaya Haidar bazan k'ara zuwa gidan ka ba, matar ka da k'awarta na ta zagina suna kirana karuwa na biyo sa....." Da hannu ya dakatar da ita alamar ya isa, Tsayuwar sa ya gyara da cewa "Dama ance laifi tudu take naka ka hango na wani, haka gwano baya jin warin jikin sa, idan kana aikata abu sai kayi tunanin kowa ma hakane" Ya k'ara gyara murya da cewa "Ni na buk'aci zuwan Rauda", Asiya sam bata fuskanci zantukan nasa ba, zuwan Rauda kad'ai zata iya cewa ta fahimta, mamakin makircin Rauda ne ma ya cikata, yayin da Bongel tuni ta fahimci me yake nufi, ranta taji ya b'aci yadda kullum yake munana zato a kanta, Cikin sanyin murya tace "Yana da kyau a rik'a kyautata zato, da tsananta bincike kafin yanke hukunci", Tana fad'ar haka ta wuce d'aki, Haidar yabi bayanta da kallo cikin tsananin mamakin furucin ta, wane zato zai kyautata a kanta bayan duka shaidu sun bayyana, ba zata tab'a wanke kanta a wurin sa ba ya tabbatarwa kansa tare da yin siririn tsaki, Asiya tuni ta rufawa Bongel baya,

Ya juya kan Rauda dake sharar hawaye yace "It's ok", Hawayen munafuncin ta share, Kujerar kusa da ita ya zauna yace "Kin kira muna meeting that's why nace kizo gida ki jirani", Rauda cikin kissa d kisisina tace "Dama kullum sai nayi mafarkin muyi aure Allah, shine nace why not kayi ma su Daddy magana a sa rana very soon", Haidar yaja numfashi a ransa yana mamakin yadda Rauda sam bata da aji, yana son mace mai aji, wacce tasan k'ima da darajar kanta, amma ya ya iya, ta hanyar Rauda kad'ai zai samu fitar da Bongel rayuwar sa, A zahiri yace  "Kar ki damu ba da jimawa ba", "Da gaske my dear" Ta fad'a cikin tsantsar farin ciki, Yayi mata nodding kai, Ta  washe baki ta yadda ta kasa b'oye farin ciki, Haidar ya tashi yace zai shiga d'aki, Rauda itama ta tafi da k'udurin ganin bayan Bongel, ba zata tab'a yarda tayi zaman kishi da ita ba, ganin ta yau ya k'ara mata k'iyayyar ta.

************************

"Ni fah ban fuskanci zantukan ki da na Haidar ba" Asiya ta fad'a, Bongel tace "Share kawai", "Shikenan kunfi kusa mata da miji", Bongel tayi murmushi, Asiya bata jima ba, ta tafi.

*********************

Jikin Hajiya Mariya ta fad'a tace "Mummy Yaya Haidar yace zai turo a saka mana rana", "Ke Rauda bana son wasa", "Wallahi Mummy da gaske nake", Hajiya mariya cike da farin ciki tace "Kai naji dad'in jin wanne zance, Allah ya nuna mana", Raudah ta amsa da "Amin, Mummy gagarumin biki za'a mun wanda yafi na Yaya Hafsa", "Baki da damuwa", Raudah tayi murmushin farkin ciki, tana son high life komai tafi son na k'arya, "Bara na tashi na sanar da Alhaji wannan abun farin ciki", Hajiya Mariya ta fad'a tana mik'ewa.

BONGEL(COMPLETED)Where stories live. Discover now