33

1K 84 20
                                    

*BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

*HASKE WRITERS ASSO...*

TALATIN DA UKU

Bongel harkokin gabanta take, sam bata sawa kanta damuwar k'arin auren Haidar ba, a ganinta me zai dameta bayan ba zaman auren suke ba, kawai suna amsa sunan mata da miji ne amma babu wata alama ta cewar su ma'auratan ne, Ta maida hankali sosai wurin makarantar ta, Littafi ne a gabanta tana duba lecture da suka yi jiya, Kiran Asiya ya shigo wayarta, ta amsa tare da yin sallama, Asiya ta amsa ta d'ora da cewa "Yanzu nake jin labarin Haidar aure zai k'ara", Bongel tayi murmushi tamkar tana gabanta ta tace "Eh hakane", "Wallahi hankalina ya tashi matuk'a, auren ku duka duka yaushe da zai k'ara wani", Bongel tace "Babu komai Allah ya k'addaru faruwar hakan, sai dai muce Allah yasa alkhairi", Asiya tace "Hakane, Amin dama damuwata kece tunda baki da damuwa da hakan, hankalina ya kwanta", "Gobe ki shigo mun da textbook d'in ki na econometrics" Ta fad'a tana son kawar da zancen, Asiya tace "Toh", Sukayi sallama ta kashe wayar.

***************************

"Mum kinga rigar dana zab'a zan saka a dinner" Cewar Rauda cike da zumud'i tana nunawa Hajiya Mariya, Ta karb'i wayar ta duba tace "Wow zata miki kyau kuwa", Rauda tayi tsalle tace "Har na hango ni ciki", Hajiya Mariya tayi dariya, Kafin ta nisa tace "Har yau ban ga Haidar yazo gidan nan, sab'anin lokacin da yake neman auren Hafsah kusan kullum
sai yazo", Rauda ta turo baki tace "Wai yana busy ayyuka ne ke masa yawa", "Komai aikin sa ya kamata ya samu lokacin zuwa", "Zan mishi magana" Cewar Rauda, Ta juya wurin Humairah tana nuna mata sauran abubuwan da ta zab'a na bikin.

************************

Haidar ta b'angaren sa ba wani shiri yake ba, kud'in lefe ma basu yayi yace suyi da kansu, auren zab'in sa ne da ra'ayin sa, sai dai deep down baya farin ciki dashi, aure ne wanda bambamcin sa dana Bongel kad'an ne, amma ganin shine kad'ai hanyar rabuwa da ita yasa yake k'arfafa ma kansa gwiwar yin sa, yana ji a ransa gara auren Rauda akan Bongel, kuma ko ba ya son Rauda yanzu with time zai fara son ta, he will try ta zama yadda yake son matar sa ta kasance,

Zaune yake a balcony na d'akin sa, iska mai dad'i na kad'a sa, yana shan dalgano coffee, kiran Rauda ya shigo, yayi receiving, "Hello My dear", "Na'am" Ya amsa, "Please kazo gida yau, kullum Mum na complain baka tab'a zuwa ba", "I will see" Ya fad'a, "Please please try kazo" Ta fad'a tana bubbuga k'afa kamar yana ganin ta, Shagwab'ar tata haushi take basa amma ya zai yi tunda shi ya jajubo ta, "It's ok zan zo" Ya fad'a yana kashe wayar tare da d'an dafe kansa.

***************************

"Ya kamata ka tausayawa yarinyar nan ka duba irin soyayyar da take maka" Cewar Kassim, Hisham dake  kwance kan doguwar kujera, Ya tashi zaune yace "Sau nawa zan fad'a maka ka daina mun zancen Ihsan", "Dole na maka Hisham kaine mutum na farko daka soma saninta matsayin ya' mace, kai ka shayar da ita zumar soyayya yanzu kuma ka juya mata baya", "Sanin kan ke ne bana serious dating, duka yan' matan da nake kulawa kawai just for fun ne, ayi sha'ani a wuce wurin, babu wacce nayi ma alk'awarin aure", Kassim ya jinjina kai yace "Hakane amma ka duba lamarin Ihsan, ta mutu a son ka", "Kaga Kassim babu wacce zan iya aure sai Bongel", "Bongel" Kassim ya maimaita, "Yes ita", "Tana matsayin matar yayan naka", "Lokaci kad'an na d'ibarwa auren su zata dawo gare ni", "Da zan baka shawara ka hak'ura da ita kawai", "Sai kuma ban ce ka bani ba" Hisham ya fad'a yana mik'ewa ya bar Kasim wurin, a ganin sa duk wanda ba shawarar yadda zai samu Bongel zai basa ba, toh ba masoyin sa ba ne.

****************************

Abba ya kira Haidar kan maganar gidan da zai ajiye Rauda, Ya russunar da kai yace "Abba gida d'aya nake son had'a su", "Me zai hana ka rabasu kasan sha'ani na mata da kishi, ina ganin rabuwar tasu shine yafi", Haidar yayi k'asa da murya yace "Had'in kansu nake tunani saboda yaran da zasu haifa nan gaba kada su taso kansu a rabe", Abba ya jinjina kai yace "Kayi tunani mai kyau, Allah ya basu zaman lafiya da fahimtar juna", Ya amsa da "Amin", K'asan zuciyar sa sam ba haka bane, yana son had'asu gidan d'aya ne dan hakan na cikin shirin sa.

BONGEL(COMPLETED)Where stories live. Discover now