28

1K 63 7
                                    

*BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

  *HASKE WRITERS ASSO...*

ASHIRIN DA TAKWAS

_MUDEX, SURAYYA, ELBEELAH SHAFIN NA YAU NAKU NE😻🥰_

Bongel jin fad'uwar sa, ta kai dubanta, ta gansa zaune dirshan a k'asa cikin ruwa, hannu tasa tana gumtse dariyar da ta taho mata, Haidar jin alamun dariya ya kai duban sa gareta, ya k'ara had'e rai, yana jin ya matuk'ar muzanta, zuciyar sa ta harzuk'a ganin kayan sa sun jik'e, Mik'ewa yayi cikin karaji yace "Bagidajiyar ina ce ke, da zaki cika ruwa haka a mopping", Bongel duk da ta tsorata ta dake cikin sanyin murya tace "Naji kace kamar ba'a sa ruwa ba", Tsaki yayi yace "Illiterate" Ya wuce d'aki cikin tsananin b'acin rai, Kalmar illiterate ke yawo a k'wak'walwar Bongel, ba k'aramin b'ata mata rai tayi ba, tuna daga bakin wa ya fito yasa zuciyarta tace "Kada ki manta daga bakin wa ya fito, mutumin da yafi kowa tsanar ki a duniya, mutumin da baki da k'ima had'i da daraja a idon sa, zai iya fad'ar abunda yafi haka", Hakan yasa ta sassauta b'acin ran, tana jin zaman su inuwa d'aya ba mai yiwuwa ba ne.

**************************

Haidar yayi tsaki yafi a k'irga, yana jin kamar ya sameta ya mata shegen duka, kayan ya sauya wanda basu kai kyan wanda ya cire ba, ya wuce office rai a jagule, a ransa yana jin ya zama dole ya gaggauta fitar da ita rayuwar sa,

  Kusan tare sukayi parking mota tare da Alhaji Sani, Haidar ya fara fitowa, kana Alhaji Sani, Haidar ya gaishe sa, ya amsa yana mamakin sauyawar Haidar d'in, gaisuwar da ya masa yau tasha bambama da ta kwanakin baya, tamkar lokacin da Hafsah na raye, kafin rashin jituwa ta soma shiga tsakanin su,

  "Ya zama dole na canza tsakanina dashi, ina son  fita rayuwata cikin k'ank'anin lokaci" Haidar ya fad'a a ransa yana shiga company.

***********************

Bongel yau ta aikatu, ko'ina na gidan sai da ta gyara tsaf, ta saka turaren wuta mai dad'i, Irfan ta fara yi wa wanka ta shirya sa, kana tayi itama, ta shirya cikin material lace, tayi kyau duk da babu kwalliya a fuskarta natural beauty, sai da ta huta kafin ta shiga kitchen d'aura girkin rana, Cikin awa d'aya ta kammala komai, ta jera kan dinning table, ta d'ibarwa Ammi farfesun kaza,

   Mayafinta da kalar sa tayi daudai da kayan ta saka, ta d'auki kular ta kama hannun Irfan zuwa gidan Ammi, Tun fitowar ta har ta shige wurin Ammi akan idon Hisham wanda ya fito zuwa company ganinta yasa ya koma,

    Cikin ladabi ta gaishe da Ammi, ta amsa tana tambayar lafiyarta, Tace lafiya lau take, "Dan' gidan Aunty" Ammi ta fad'a tana shafa kan Irfan, da yazo ya manne jikin ta,

   Kular ta ajiye gaban Ammi, "Amarya da yin girki, ai hutawa ya kamata kiyi tunda ga masu aiki", Murmushi tayi a zuciyarta tace "Ina ma Haidar ya d'auko kirkin iyayen sa, amma sam albasa bata yi halin ruwa ba", Sallamar Hisham ya katse mata zancen zuci,

    "Ahh baka tafi ba" Cewar Ammi, dan bai jima da fita ba yace mata zai je office, "Eh fasawa nayi, kaina naji ya d'an ciwo", "Sannu magani ya kamata ka sha, ka kwanta", "Na sha magani" Ya fad'a, "Allah ya bada lafiya" Ta fad'a ta juya tana kiran yar'aikin ta, ta kawo mata plate da spoon,

  Hisham k'asa yayi da murya ta yadda Bongel kad'ai zata ji yace "Ba zan samu gaisuwa ba", Tayi shiru tamkar bata ji sa ba, Ya k'ara da cewa "Kinyi kyau sosai, kwalliyar ta burgeni", Tashi tayi tana k'ok'arin canza wuri, Daidai lokacin Ammi ta juyo tace "Lafiya dai Hafsah", Tayi murmushi tace "Ba komai" Ta dawo kusa da Ammi, Hisham yayi murmushin da shi kad'a yasan manufar sa,

   Ammi ta zuba farfesun kaza tana ci, tana yaba dad'in da yayi, Hisham hannu yasa ya d'auki d'aya, ya soma ci yace "Delicious wannan dad'i haka gaskiya daga yau can zan koma cin abinci", Ammi ta harare sa tace "Wanda ka saba ci shi zaka cigaba da ci", "Kai Ammi kinsan girkin amare da dad'i", "Toh kai ma kayi auren mana", Yace "Na kusa Ammi, lokaci kad'an ya rage masoyiyata ta dawo gare ni", Ammi da mamaki ta kalle sa tace "Toh ina taje?", Yayi murmushi yace "Auren dole aka mata", Ammi tayi dariya tace "Kace dai latecomer ya maka overtaking", "Allah Ammi bata son sa", "Toh Allah ya kyauta" Cewar Ammi tana kawar da zancen, Hisham da biyu yake maganar yana son soma isar da sak'on sa tun yanzu, Bongel sam zantukan nasa basu mata dad'i ba, duk da tana son rabuwa da Haidar amma bata jin zata auri Hisham, mai duniya zata d'auke ta, zargi zai shiga cikin zukata da yawa, haka ma bata sha'awar auren Hisham yanzu, Mik'ewa tayi tacewa Ammi zata tafi, Ammi tace "Ba zaki zauna mutu hira ba Hafsah", Kanta ta k'ara sunkuyar cikin ladabi tace "Wani aiki zan k'arasa" bata jin zata iya k'ara minti biyar a wurin, irin kallon da Hisham ke mata yasa duk ta takura, "Toh nagode sosai, Allah ya miki albarka", Ta amsa da "Amin", Irfan ya taso ya rik'e hannun ta, "Au kai ma ba zaka zauna ba", Kafad'a ya mak'e, "Shikenan a gayas", Hisham sam bai ji dad'in tashin nata ba, bai jima ba shima ya wuce office dama zaman ta yake.

BONGEL(COMPLETED)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora