67

1.6K 131 23
                                    

*BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

*HASKE WRITERS ASSO...*

SITTIN DA BAKWAI

SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298

Dada a rud'e ta d'auko ruwa tana mik'awa Bongel wacce sam ta rasa natsuwarta, ta karb'a ta d'iba a hannu tana shafa masa a fuska, Haidar yaja dogon numfashi, a hankali ya bud'e idonsa ya sauke cikin na Bongel wanda ta zuba masa nata sexy eyes d'in, Kasa tashi yayi daga kan jikinta, itama bata yi yunk'urin janye sa daga jikinta ba, face kallo da suke jifar juna dashi,

"La ilaha illallahu! yau ina ganin fitsara, a gaban idona tsabar fitsara, tabbas boko ba abunda ya koya miki sai karuwanci, yarinya kamar ba jinin fillo ba", Maganar Hamma Siddiku ya ankarar da Bongel, tayi saurin ture Haidar daga jikinta, tana k'ok'arin mik'ewa, Hannu yasa ya jawota ta fad'o jikinsa, ya matse ta gam a k'irjinsa, mugun kunya taji ta lullub'e ta ta rufe idonta gam, Dada shigewa tayi d'aki ganin abun yafi k'arfin ta,

"Tabbas babu kunya a tare da kai Haidar, a gaban idona, banda ma iskanci da saki tsakanin ku kake rungumarta", Cewar Hamma Siddiku cikin masifa, Haidar murmushi mai ciwo yayi yace "Ban saki matata ba, haka bazan tab'a sakin ta ba, ka koma ka sanar da wanda ya aiko ka, Hafsah ta haramta ga kowane da' namiji sai ni", Bongel zantukan Haidar tamkar a mafarki take jin su, sai dai kunyar Hamma Siddiku yasa ta kasa bud'e idonta balle ta aiwatar da wani abu, tamkar k'asa ta bud'e ta shiga haka take ji,

Hamma Siddiku yace "Na fahimci a lamuran ka akwai rainin hankali ciki, ka maida saki ba bakin komai ba, ka saki yarinya a lokacin da kake so, ka mayar da ita lokacin da kake so, kayi na farko, toh wannan karon idan ma mayar da ita kayi wallahi sai kun rabu", Mamaki shimfid'e kan fuskar Haidar yakai duban sa ga Hamma Siddiku yace "Ina jin baka fahimci komai ba ne, amma saki bai tab'a shiga tsakanina da Hafsah ba", "K'arya kake wallahi, lokacin bikin saude ba sakin nata kayi ba ta koma, kuka yi rufa rufa ka mayar da ita, toh a tafin hannuna kuke", Haidar murmushi yayi jin zancen tamkar almara, Hamma Siddiku yace "Kana murmushi tun ina da masaniyar komai, tun a lokacin Hisham ya sanar dani", Bongel a razane ta d'ago tana kai dubanta ga Hamma Siddiku, kenan Hisham ya sanar dasu lokacin sakinta aka yi, idan bata manta ba babu wanda yaga lokacin da Haidar ya bata takarda sai Rauda, Taya Hisham ya sani, hakan na nufin Rauda ta sanar dashi, Take zancen zuci yayin da taji kanta ya mugun d'aurewa,

Haidar wani sabon tashin hankali yaji ya k'ara kama sa, k'asan zuciyar sa na zafi tamkar ana hura masa garwashin wuta, dukkan wasu hujjoji sun tabbatar Hisham auren Bongel yake son yi, tunanin maganganun da ya rik'a samun sa kan Bongel yake, A ko da yaushe yana nuna masa son daidaita su da Bongel, idan hakane meyasa yanzu yake son auren ta, hakan na nufin ba da gaske yake ba, Zafin zuciyarsa yaji ta k'aru, ya runtse idonsa gam har lokacin Bongel na rungume jikinsa ya kasa sakinta,

Hamma Siddiku yace "Zaka sake ta mu tafi ko kuwa, ke kuma munafuka kin wani k'ak'abe jikin sa", "Kayi hak'uri zuwa gobe zan sa a kawota", Haidar ya fad'a cikin sanyin murya, Jin haka Bongel tayi saurin janye jikinta daga nasa, cikin zuciyarta tana jin zafin furucin nasa kenan ya shirya rabuwa da ita, ya barwa Hisham, Hamma Siddiku yace "Ka tabbatar ta dawo goben, dan aurensu da Hisham wani sati", Ya juya ya fice ba tare da ya jira amsar su ba,

Bongel d'aki ta shige, Haidar yabi bayanta da kallo zuciyarsa na huci, yayin da ya juya ya fice daga falon, ya nufi motar sa, sam ya manta tare yake da Irfan, wanda kuka yasa masa ya kawo sa, suna shigowa yaga yara yabi su sashen Inna(kishiyar Dada, nasan kun manta da ita), Haidar tsintar kansa yayi da d'aura kansa kan sitiyari ya kasa tuk'i, ya rasa me yake ji a ransa, ya kasa yarda Hisham ke son auren Bongel, wanda hakan ke nuni da cewa bai hak'ura da ita ba, yana son ta, bai duba cewar yayan sa ya aure ta ba yake son auren ta, wane irin kwamacala yake son yi, meke gudana cikin zuciyar sa, kwanaki kad'an da rabuwar auren su yake son auren ta, "Laifin ka ne tun farko da ka auri budurwar k'anin ka, wacce suka tab'a had'a shimfid'a", Zuciyarsa ta fad'a, Hannu biyu yasa ya dafe kansa da k'arfi, yayin da zuciyar sa ke barazanr tarwatsewa tana amsar wani mummunan gashi, Kansa yayi saurin girgizawa da cewa "No No something is wrong somwhere", Sabon tunani ya sake fad'o masa, "Meyasa lokacin auren Saude Hisham ya sanar da Hamma Siddiku ya saki Bongel, bayan ko kusa ba haka bane, maganar rabuwa a lokacin bata shiga tsakanin su ba, balle saki, "Ya Hayyu Ya Qayyum" ya furta ganin ya kasa hasaso komai, Yaja motarsa yana fita daga gidan.

BONGEL(COMPLETED)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang