HUZA'IYYA.F.P.2.

2 2 0
                                    


FREE P.2.


      Cikin dauriya da juriya irin tata ta idar da sallarta wadda ta yita a nutse sannan taja ta zauna tana kai kukanta ga mai kowa mai komai lillahil wahidil ƙahhar! Ta jima tana addu'o'in harta fara manta wasu daga cikin halin da take ciki saboda yadda ta nutsu hankalinta gaba ɗaya ya tafi wajan Ubangijinta wanda ta ke da tabbacin shi kaɗaine zai iya kawo mata sauƙi,sake ɗaga hannunta tayi sama tare da cewa...

"Allahu Ahad Rabbi kai nake kira akowane bugun numfashi da kake bawa ƙirjina ikon fitarwa.Ya Rabbi ka dubeni duba irin naka kaji ƙaina ka tallafi maraici na dan arziƙin Masoyinka Muhammadu,Allah bani da madafa ko bangon jingina kaikaɗaine zaka iya tallafawa rayuwata ka kawo mata ɗauki asanda ka..."

"Ke Uwar limamai ajje banzan hannun nan naki kizo kiyimin wankin da na sakaki tunkafin na saɓamiki sannan kije kihaɗa huta ki kaɗa miyar kuka bazan bawa almajirai gayan tuwo ba buƙata ta taƙi tafiya karki yarda na kuma miki magana"

HAJIYA LAMI ta faɗa daga bakin ƙofa sannan ta juya a zuciye kamar wadda akaiwa ƙwacen kuɗi...lol...

Yunƙurawa Huza'iyya tayi  da salati abakinta tayi wajen bayan ta haɗo wankin auta se ga Hajiya da kayanta kala biyu ta watso su ta saman bene tare da umarnin itama ta wanke mata su.Ƙwallar da take ɓoyewa ce ta samu damar gangarowa kan tudun kumatunta,hannunta tasaka ta fara gogewa inda taji ƙafarta na karkarwa wanda hakan ya tilasta mata tsugunnawa awajan tana matsar ƙwallar.

Tsawon mintina biyar Hajiya na tsaye tana kallonta inda ƙarshe ta fara sakkowa daga benen ganin tsugunon nata so yake yi ya zarcemata zuwa zama tazo ta ja kujera ɗaya daga cikin kujerun da ke jere ta zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ɗora idonta kan screenɗin wayarta tana sakin wani shu'umin murmushi wanda har Huza'iyya da ke gefe tana iya juyota.

Roba OK ta ɗauka tare da tarata jikin famfo da niyyar ta tari ruwan taji muryar Hajiyar na faɗin...

"Ke dalla can gafara! Banason iskanci kije duro ki ɗiba kiyi amfani da shi banson ganda,idan kuma kikayi wasa rijiya zaki fita ki ɗebo inyaso ki mutu saboda ciwon jiki tunda kanki aka fara ciki da haihuwa ko ko ince zawarciii"

"Tom Hajiya kiyi haƙuri"

"Haƙurin uban me zanyi kuma,ke ba daban haƙurin nawa ba ai wallahi ko zaman gidannan se ya gagareki dan ni bazai yuwu abarmin amanarki tunda ƙuruciya ba ki girma na aura miki maza har huɗu ki ƙi zama ki rabu dasu nikuma naci gaba da riƙeki ba,ai yanzu ki wuce munzalin ruƙo sedai kema kije ki nemi kuɗi kiyi yara su dingamiki hidima bawai kidawo gida ba.
    Ni yanzu ma magana muke da wani Alhaji BALALA yaga photonki yana so namai alƙawari idan kin haihu zan aura masa k..."

"Aure kuma Hajiya?"

Ta faɗa afirgice kamar wadda ƙadangare yahau wa jiki.

Dariya Hajiya Lami ta sanya kafin ta kada baki tace....

"Oho!! Wato ke yanzu wuyanki haryai kaurin na faɗi magana ki tambaye ni to wallahi ki shiga hankalinki da ni ki hanzarta wankewa Auta kayanta da nawan idan ankawo wuta cikin dare ki tashi ki gogemata"

"Amma Hajiy..."

Ai bata rufe bakinta ba taji saukar wani wawan mari a fuskarta wanda se da ganinta naɗan lokaci ya ɗauke. Bata sake magana ba ta ɗibi ruwan duk da yadda takejin alamun jikinta tana da tabbacin bazata kai ƙarshen wankinnan ba se wani abu ya sameta saboda ko'ina na jikinta da kalar ciwon da yake mata.

Zaman dirshan tayi tana cuɗa kayan hannunta kamar tana taɓa wuta dan wahala,daƙyar ta ke cuɗawa sanda tazo kan na Hajiyar saboda irin less ɗinnanne mai masifar nauyi ga dutsuna jitake kaɓar su fasa mata hannun.Cikinta ne yayi wani irin juyi wanda tundaga tsakar kanta har yatsunta taji kamar za'a zare mata rai,wani wahalallen nishi take fitarwa tare da riƙe robar wankin kamar zata rabata biyu ta dage iya ƙarfinta take faɗin "Hajiya ki temakamin karna mutu cikinaaa"

Ko gezau hajiya batayi ba charting ɗinta takeyi cikin kwanciyar hankali kamar batasan me ke faruwa da Huza'iyyar ba.

Karan sigari ce a hannunsa ya shigo yana zuƙa idanunsa sunyi jawur kamar garwashin wuta yana daga waje yaji kukan Huza'iyya ya shigo ko sallamama shi baiyi ba yama manta ya ake yinta. Hajiya Lami na ganinshi ta miƙe tsaye tare da dire wayarta kan kujerar tana faɗin...

"Ɗana mai sharen hawayena ashe kana unguwar oyoyo.."

Wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata wadda seda ilahirin jikinta ya ɗauki rawa tayi baya saboda sanin halin ɗan nata.

"Rufamin bakinki nan banson wata magana,yarinyarnan da tsowon ciki me ya haɗata da kaya haka me takeyi da suuu?"

Ya ƙarasa maganar cikin ƙaraji tare da sanya ragowar guntun sigarin hannunsa yahau zuƙa kamar bazai bari ba...






ƳAR GATAN MAMA✍🏻.

✨HUZA'IYYA✨Where stories live. Discover now