HUZA'IYYA .F.P.8

0 1 0
                                    

*💦HUZA'IYYA💦**




*LABARI/RUBUTAWA*
*KHADIJA S.SAMINU*
*(ƳAR GATAN MAMA)*


            *MARUBUCIYAR...*

   Rayuwar mu.
   A Wani Gida.
   Maganin kar ayi..!
   Rana dubu...
   Wata Duniya.
              nd now...*💦HUZA'IYYA💦.*


*NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYA GA ƊAUKACIN ƳAN ƘUNGIYAR YI DOMIN ALLAH KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YAJA DA RANKU YA ƘARA MUKU FASAHA DA ƘOƘARIN ILIMANTAR DA AL'UMMA,INA GAISUWA A GAREKU**


FREE P.8.


........Duk wani masoyi na ya shiga cikin matsanancin tashin hankali babu kamar Mama ta dannikam banma san meke faruwa ba dan tuni na fita a hayyaci na.Ba komai ke faruwa ba illa maganar rushewar zancen aure na da *MU'AZZAM* Ƴan uwan mahaifiyarsa dama ita kanta ne suka cika gidan namu da har ƴan biki dangin Mama Aisha sunfara hallara acikinshi,ta inda suka shiga batanan suke fita ba bala'i da masifa kamar akansu aka sauke shi saboda yadda suke kumfar baki suna yinsa, kowaccensu da kalar shigar rashin mutuncin da tayi,daga mai ɗamara sai mai kallabi akan goshi tana ta surfa tijara son ranta Mamata sai basu haƙuri take yi amma ko gezau basu yi ba.Banson me ya faru ba kawai se ganinsu muka yi Mahaifiyar tasa na faɗin su ƴan dangi ne ɗanta bazai auri ƴar-ƴar sadakar yalla ba,wai sun sami labarin Mahaifiyata bata da dangi ba'asan daga inda Mahaifina ta samo ta ba,ita bazata bari tana raye ɗanta ya auri ƴar tsintacciyar mage ba.
 
Munanan kalmomi babu irin wanda basu faɗa ba akaina da Mahaifiyata wanda suka sanya nakasa komai nai zaman dirshan ina zubar hawayen da bansan yazo ba.Mama ce ta ke ta roƙonsu akan suyi haƙuri amma sunƙi sema ci mata mutunci da suke yi son ransu wanda hakan yasa nayi ƙarfin halin miƙewa na fara tafiya ba tare da ina banbance akan me nake tafiyar ba,'shin kan ƙafafu na nake ko kuma tashi sama nayi?'haka naita tunani har na isa inda ta ke najanyeta muka yi ɗaki sannan na rungumeta na fashe da wani irin kuka mai cin rai yayin da tayi ƙoƙarinta wajan kwantarmin da hankali,ko da na tabbatar da sun gama kwashe kayan lefensu tas sunfita daga gidan se hankalina ya kuma tashi duk nabi na gigice.

Bayan Mamata da taushe ni tayimin nasiha ne na samu na ɗansha ruwan lipton naɗan watsa ruwa sannan na ɗauki wayata na kira *Mu'azzam* dan inji ko da saninsa akayi hakan amma ga mamakina se naji wayar akashe,dolena na haƙura na rabu da shi zuciyata tana wani irin tafasa ahaka bacci ɓarawo ta dinga fuzgata.

A haka kwanakin biki suka wuce ba'ayi ba yayinda waɗanda suka zo suka koma gidajensu nikuma na sake shiga wata damuwar dukda Mama tana iya ƙoƙarinta akaina dan haka bana sakewa na nuna mata ina damuwa saina shiga kaɗaici sannan abin yake dawomin,kuma har wannan lokacin ina kiran wayarsa bata shiga hardai nafara sanya tunani araina kodai daman yaudarata ya shirya yi oho masa.

Tunanin hakan yasa nafara ƙoƙarin cireshi araina dukda nasan mawuyacin abu ne na iya cireshin amma haka nake ƙoƙarin cireshin dan na samarwa kaina da Mamata mafita dan na fuskanci damuwar da nake ciki ta sanya tana ganin ko ta gaza wajan riƙeni ne.

@@@@

Bayan an kwana biyu da wannan magana kwatsam muka wayi gari da wasu baƙi suna shigowa da kaya gidan,abin ya bamu mamaki amma se muka ga *HAJIYA LAMI* tare da su,nan dai Mama ta kasa yin shiru ta tambaya sannan yayin da ta bata amsa da cewar *MAMA HAUSU* ta siyar gida tunda gidan ɗanta ne dan haka ungulu ta koma gidan tsamiya sannan ta bada ni tunda ba jininta bace ni kuma ba gado na aka bar mata ba balle tafaɗi wani abin,tunda muke da Mama bantaɓa ganin faɗanta ba se ranar suka yi tayi ita da Hajiya Lami inda aƙarshedai suka koreta kora ta hulaƙanci tare da bata tumunin takabarta.

suka raka ta da baƙaƙen magangamu marasa daɗin sauraro daga ni har ita kuka muke yi amma haka muka rabu badon ranmu yaso ba.Nan dai aka shiga ɗebe kayanmu ana fita da su kayan ɗakin Mama Hajiya LAMI tasa aka zubamata su aɗakinta yayin da ta siyar da nata dan ba kalar tsadarsu ɗaya ba,nawa kayan ɗakin kuma aka zuba aɗakin ƴaƴanta ƴan mata yayin da ni kuma aka sauke ni a wani ɗaki ɗan kuyat wanda idan agidanmu ba yadda za'ayi na zauna a cikinshi dan ko store ɗinmu yayi huɗunshi amma ahaka aka ajjeni a ciki amatsayin wajan da zanci gaba da rayuwata.

@@@@

          Rayuwa taci gaba da gangaramin a haka cikin kaɗaici da tunanin Ummana wadda ko a waya bana samunta saboda tun ranar da na dira Hajiya ta karɓe wayata wai acewarta ba zaman game nazo yiba so ta ke na koyi ayyukan gida dan tasan gidanmu sangarta bata bari an koyamin ba dan haka ita zata koyamin yanzu,hakan yasa bani da waya ko ƙarama bani da hanyar ganin ƙawayena ko zuwa wani wajan bcoz islamiyya ma ta hanani zuwa wani malami ke zuwa gidan kullum yana yimin karatu yayin da sauran yaranta suke zuwa makaranta su sawo su taddani agida,ganin da gaske ta ke bazan fita naje wajan wani ba yasa na dangana na fauwalawa Ubangiji duka lamurana dan shi kaɗai zai iya agazamin.

Kullum da safe idan na tashi zanje na ɗorawa ƴaƴanta manyansu da ƙananunsu ruwan wanka sannan na haɗamusu abin kari dama wanda zasu tafi da shi sannan na haɗa wanke-wanke nayi shi,bayan nagama zanbi ko wane ɗaki na gidan na shareshi na gogeshi tas dan idan nayi baifita ba saina sake wataranma ahaɗamin da tsinannen duka wanda gobe bazan so aƙamin irinshi ba,bayan wannan baƙar wahala da nasha zata dinga ƙirƙiro ayyuka marasa ma'ana tana bani kuma dole na nayi bazan samu na karya ba se abin karin yayi sanyi ƙalau idan nagama aiki akan kari naci na ƙoshi idan kuma nayi ganda azabtare ranar ko abincin rana nayiwa kaina.....

Free pages sun kusa ƙarewa ki hanzarta kibiya kuɗinki domin jin yadda ƙaddarar *HUZA'IYYA* ta kasance.








ƳAR GATAN MAMA✍🏻.

✨HUZA'IYYA✨Where stories live. Discover now