HUZA'IYYA. F.P.4

1 1 0
                                    


*💦HUZA'IYYA💦**




*LABARI/RUBUTAWA*
*KHADIJA S.SAMINU*
*(ƳAR GATAN MAMA)*


            *MARUBUCIYAR...*

   Rayuwar mu.
   A Wani Gida.
   Maganin kar ayi..!
   Rana dubu...
   Wata Duniya.
              nd now...
*💦HUZA'IYYA💦.*


*NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYA GA ƊAUKACIN ƳAN ƘUNGIYAR YI DOMIN ALLAH KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YAJA DA RANKU YA ƘARA MUKU FASAHA DA ƘOƘARIN ILIMANTAR DA AL'UMMA,INA GAISUWA A GAREKU**

FREE P.4.

"Shalele ina Huza'iyyar ta ke na ganka kai ɗaya haka?"

"Na kaita yafi dacewa ta zauna inda za'a bata kyakkyawar kulawar da zata haife abinda ke cikinta lafiya itama ta samu ingantacciyar lafiyar"

Ya bata amsa ba tare da ya kalli inda ta ke ba sema ƙarasa shiga cikin da yayi yana harhaɗa kayan Huza'iyya na sakawa dama wanda zata buƙata.Yana cikin hakan ne ya tsinkayi muryar Hajiyar na faɗin...

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Fu'ad me kake shirin aikatawa haka,ina ka taɓajin an auri mace da ciki da zaka ɗauketa kaje ka ajjeta a wani guri daban sani ba? da kayi haƙuri ka tsaya ni da kaina zan aurama ita ba seka saɓama shari'a da al'ada ba,ina kakai ƴar mutane wai"

Ta ƙarasa maganar fuskarta ɗauke da bayyanannen ɓacin rai cikin ɗaga murya.Shima Fu'ad cikin nasa hargagin ya katseta wajan ɗaga mata hannu tare da cewa...

"Kinga Hajiya ki kwantar da hankalinki ƙwayoyin da nake sha basu gusarmin da tunani ba ina gane abu me kyau da akasinsa shiyasa har na gano azabar da take sha agidan nan ta hanyar ɓoyayyun masoyanta shiyasama kika ganni gabanki,kuma ki sani ba aurenta zanje nayi ba kamar yadda tunaninki ya baki zan reneta ne na kula da ita idan lokaci yayi babu mahaluƙin da ya isa ya rabani da ita koda kuwa kecee"

Yana gama faɗar haka yasa kai ya fice ɗauke da babbar akwatin Huza'iyya,inda ita kuma tahau sababi ta inda ta shiga batanan ta ke fita ba kamar wata zautacciya tahau faɗin...

"Wallahi Fu'ad baka isa ba! Na ce baka isaba ka auri Huza'iyya tazo a sirikata ba dukda kuwa jinina ce gwanda ka auri ƴar iska da ka aureta dan bazan ɗebi ƴaƴanta a matsayin jikokina ba wannan alwashi  na ne,indai ƙafata tana taka ƙasa bazan taɓa bari wannan abu ya kasance ba ko zanyi yawo tsirara sena rabaka da wannan fitinanniyar.Yoh tun yanzuma tana jiyaka kana bijiremin inaga ka aureta sam! Bazai yuwu ba,sanadinta ka tsallake ka rabu damu yanzu ka dawo sanadinta kai wannan yarinya jinin uwarta akwai maita acikinshi dan gaskiya ba iya sha a nono tayi ba wannan harda jininma haka yake amma mu zuba"

Haka taita surutai tana bige-bigen kujera har seda Auta ta lallaɓata da banbaki sannan ta haƙura ta tafi ta kwanta,amma ko da ta kwanta ba mafarkin da take yi sedai taga wai ga Fu'ad tare da Huza'iyya suna ta farin ciki,ta farka ita kanta batasan adadi ba ahaka har gari ya waye mata.

@@@@

Ko da fitarsa se ya nufi ɓangarensa yayi kwanciyarsa ransa fes jinsa yake kamar yau uwarsa ta haifeshi saboda yanda yake jinsa sakayau babu nauyin komai,bashi da burin da ya wuce mallakar Huza'iyya a matsayin abokiyar rayuwarsa tun bai mallaki hankalin kansa ba har ya mallaka amma ƙaddarori da mahaifiyarsa  suka dage suka rabashi da ita ta hanyar aurar da ita,baya da wani baƙin ciki se ya tuna maza har huɗu Huza'iyya ta aura se yaji duk ransa yabi ya ɓaci kamar ya rufe kansa da duka ko yaji daɗi,amma a wannan sakatin yayiwa kansa alƙawarin babu abinda zai hanashi aurenta.Haka har bacci ya ɗauke shi yana hango fuskarta mai maɗaukakin kyawu dama halayyarta me birgewa**HUZA'IYYA! Fara ce tas kamar a tsaga jini ya fito,tana da dara-daran idanuwa wanda suke ashanye dan duk wanda yayi tozali dasu bayason ɗauke idonsa daga kansu,hancinta zirere dogo mai matuƙar kyau da birgewa,bakinta ɗan kuyat ƙarami leɓɓanta jajaye masu azabar kyau yanda idan tana magana baka iya ɗauke kai daga kallonsu,wuyanta yana da ɗan tsayi dai-dai,dai-dai inda fatarta ta ke wani shinning kamar jaririya,ko'ina acike take taf kamar ita tayi kanta dan shape idan ana ragewa asanwa wasu se Huza'iyya ta rage nata,a taƙaicen taƙaicewa dai ta haɗu ta haɗe shiyasa maza suke rububi akanta saboda kyanta da kuma sassanyan halinta,tashi yayi firgigit tsakar dare yahau dube-dube dan abarcinsa ganinsa yayi gashi ga Huza'iyya suna faɗawa juna kalaman soyayya masu wuyar mantawa**cike da takaicin fuskantar mafarkine ya tashi ya gyara kwanciyarsa wani bacci ya sake awon gaba da shi bai sake farkawa se bayan assalatu dan ko jam'i bai samu ba daban yayi tasa mutane na kallonshi da mamakin ya dawo zuwa masallaci wasu na ta masa addu'ar ɗorewarsa a haka.

***1 week later***

Hajiya Lami tana cikin matsananciyar damuwa da rashin sanin inda Huza'iyya ta ke gashi ta kaɗa ta raya Fu'ad ya sanar mata yaƙiyin hakan dukda kwa har kukan kissa ta sakamai tana ya temaketa amanarta ce amma ya rabu da ita ƙarshema ya tsallake yabar ƙasar bayan yaje ya bawa Deen isassun kuɗi fiye da wanda za'a buƙata wajan hidimar Huza'iyya dan bayason ko kaɗan ya ɗoramishi nauyi,haka tabi ta zurawa sarautar Allah ido dan ta miƙawa komai gareshi a wannan lamarin nasu,takanas ta shirya tayiwa gidan Deen abokin Fu'ad bazata domin taji ko yasan inda Huza'iyya ta ke?amma ga mamakinta se shima yahau sallallami    yana faɗin lallai Fu'ad baida tunani zai kirashi ya tambayeshi,ko da ya kirashi ma ko ɗaga wayar baiyi ba tana kallo nan yake sanar da ita aishi ya daɗe baya samunsa a waya morethan four months rabon da su gaisa da shi.Haka ta kwaso jiki ra dawo a sanyaye da tunanin ko dai da yarinyarnan ya guduma oho...

@@@@

Rumaisa ce ta haɗowa Huza'iyya ruwan lipton ta kawo mata saboda kwana biyu bata wani iyacin abincin kirki se ɗilli-ɗilli wani ma idan taci bazai zauna ba zai dawo.Ko da ɗaga cup ɗin zatasha kawai seta saki ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi wanda kana kallon yadda ta ke kukan zaka fuskanci wani abu ta tuna ya sanyata wannan kukan....

Seda ta barta tayi mai isarta sannan ta matsa daf da ita ta sanya hannuwanta tana share mata hawayen fuskarta tare da girgizamata kai itama hawayen nabin kumatunta tace...

" Huza'iyya me ya sakaki kuka?"
"Babu komai ƴar uwata"
Ta faɗa tana ƙaƙalo murmushin da iyakarshi kan fuskarta.Rumaisa  ta sake dubanta tare da dafata sannan tace...

"Huza'iyya ya kamata ace zuwa yanzu kin yarda da ni kinfaɗamin ko wace ce ke bamu sani ba ko akwai abinda Allah ya ɓoye tsakaninmu da jinki nake yi kamar ƴar uwata ta jini tun sanda ake cewa muna yanayi da ke nakejin haka araina,ki faɗamin damuwarki Huza'iyya banda maganin matsalarki amma zan iya zama silar temakonki ta wani ɓangaren"

Share hawayenta tayi ta dubi Rumaisa sannan tace...

"Ba komai ya sani kuka ba se tuna sanda nadawo gidan Hajiya da yaron cikinnan inakan ganganiyar kwaɗayi,haka nake tunkarar Hajiya dukda tsoronta da ya gama cika ni da kuma ganin cewa ita kaɗai gareni wadda zan nuna anarsayin dangin mahaifina yasa kɓna ɗauketa da girma a cikin zuciyata,bansan dangin mahaifiyata ba ita kaɗai na sani itama ta tafi ta barni sanda nake buƙatarta da ace nasan ko daɗaya adangin mahaifiyata da tuni na daɗe da barin rayuwar ƙunci na koma cikinsu nasan dole su zasu ƙauna ceni saboda zumuncin Allah.Akwai lokacin da naji babu abinda nakeson ci se kilishi lokacin aurena na farko,amma da mijina ya fuskanci hakan se ya siyo yazo gaba na ya zauna ya cinye ya saka takardar a shara inda nikuma nabita na ɗakko na dinga lasheta ina kuka danji nake inbanci ba zan iya rasa rayuwata,shayi kuwa idan nahaɗasho zansa sedai ya  watsamin a jikina sedai na saka baki ina lasar tufafina saboda matuƙar buƙat"

Takai ƙarshe tana sakin kuka,inda ta gyara zamanta tare da faɗin bara na baki cikakken tarihin rayuwata dan se kinfi fahimta.Itama Rumaisa gyara zamanta tayi dan ta ƙagu taji labarin Huza'iyyah.

**LABARIN HUZA'IYYA**

          Da farko da sunana HUZA'IYYA IBRAHIM ME FATA ni haifaffiyar garin kano ce,an haife ni a cikin unguwar **GORON DUTSE** A bayan **WRECA** cikin layin  **ALHAJI IBRAHIM MAI FATA**.

Baba na gawurtaccen ɗan kasuwa ne ɗan asalin garin **KATSINA** ne Mahaifinsa **ALHAJI BELLO MAI FATA** Yana da mata huɗu kuma kakarmu ita ce ta huɗun,ya daɗe yana neman haihuwa bai samu ba inda aƙarshe bayan ya aureta ta haifi yara har biyar huɗu maza ɗaya mace. **MAMA HAUSU** ta samu tsangwama da zallar tsana wajan haifar yarannan biyar **MUSA,HABIBU,ILIYASU DA IBRAHIM BABANA SAI KUMA ƘANWARSA HABIBA WADDA SUKE CEMATA LAMI**...




**BAZAN CEMUKU KOMAI BA AKAN LABARINA SEDAI INA SANAR DAKU TAFIYARSA TAYI DABAN DA SAURA DAN HAKA KAR AYI BABU KE KO KAI KI HANZARTA KI SIYESHI KIJI KOMAI DAKE CIKINSHI DAN HMM! NADAIYI SHIRU KAWAI AMMA KARKI BARI AYI BABU KE**



**ƳAR GATAN MAMA✍🏻**

✨HUZA'IYYA✨Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu