HUZA'IYYA F.P.5

1 1 0
                                    

*💦HUZA'IYYA💦**




*LABARI/RUBUTAWA*
*KHADIJA S.SAMINU*
*(ƳAR GATAN MAMA)*


            *MARUBUCIYAR...*

   Rayuwar mu.
   A Wani Gida.
   Maganin kar ayi..!
   Rana dubu...
   Wata Duniya.
              nd now...
*💦HUZA'IYYA💦.*


*NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYA GA ƊAUKACIN ƳAN ƘUNGIYAR YI DOMIN ALLAH KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YAJA DA RANKU YA ƘARA MUKU FASAHA DA ƘOƘARIN ILIMANTAR DA AL'UMMA,INA GAISUWA A GAREKU*

FREE P.5.

     Tunda suka taso suke fuskantar ƙalubale su da mahaifiyarsu wanda yawanci daga wajan kishiyoyin babarsu ne,se da suka girma wata rana tafiya ta kama Alhaji Bello lasancewar bayajin daɗin jikinsa se ya tura su Musa Habibu da Iliyasu su wakilce shi banda Ibrahim acewarshi bai mallaki hankalinsa ba,tafiyarsu ke da wuya sunje lafiya ahanyarsu ta dawo sukayi accident gaba ɗayansu suka mutu dan har wasu sassan na jikinsu sun bar jikkunansu danshi Musa ma ba'aga ƙafarshi ɗaya ba haka aka kaishi anata koke-koke inda wasu kuma wannan mutuwa tayi musu mugun duba da yadda mafi rinjayen dukiyar ALHAJI BELLO ta tattare a wajansu,haka aka gama jimamin mutuwarsu aka koma rayuwa kamar baya sedai tunani na lokuta da baza'a rasa ba.To fa tunda Alhaji Bello ya rasa yaransa uku se yake ganin kamar shi ya kashesu da hannunsa tunda sanadinsa ne,haka zai zauna yaita tunani inda Hausu ta ke iya ƙoƙarinta wajan taga ta kwantarmasa da hankali amma abin ya faskara.Tundaga wannan lokaci ya ɗauki son duniya ya ɗora akan Ibrahim wanda yake ganin bashi da kamarsa awannan lokacin.Duk wasu manyan kadarorinsa ya ɗauka ya bashi inda ya dage wajan nuna masa dabarun kasuwanci da duk wata harƙalla,haka kuwa Allah ya ɗaukaki Ibrahim har ya zama acikin garin *KATSINA* anaji dashi kowa ya buɗe baki LAJI IBRAHIM saboda mutumne mai son jama'a ga kyauta like baison abinsa.

Bayan wasu shekaru wani Alhaji yazo ziyarar danginsa inda yaga *HABI* Lami yace shifa yaga mata,dan haka yaita naci har seda aka aura masa ita ya tawo da ita cikin garin *KANON DABO TUMBIN GIWA*  

              Gareku ƴan ƙetaren kano🤣
*(KO DAME KAZO ANFIKA KANO TA MAI RABO CE MAMAN MASOYI KINYI GASKIYA TABBAS MUNGANI MUN KARANTA DUK WANDA YA BAR DUNIYA BAI ZIYARCI KANO AJAJANTA MASA🤣WASU MA AKAN SON MAZAJENSU SU BARSU SU ZIYARCI KANO HAR KAYAN ƊAKINSU SUKE SAIDAWA SU BASU SU ƘARA AURE😎 Hheheehehe UMMU FU'AD KANO FA DABAN CE MU DA MUKE CIKINTA MUKASAN HAKAN😁ALLAH KA TEMAKI ƳAN ƘETARE SU XIYARCI KANO RANSU YAYMUSU DAƊI...lol...😆)*

Tunda ya aureta ta zama cikakkiyar ƴar kano farin ciki ya lulluɓe rayuwarta hatta annurin fuskarta ya canza dan ba wani kyau gareta ba amma da zuwanta *KANO* saiga ɓoyayyen kyawu ya fito itama tana dawowa sedai sunanta na LAMI ne bai ɓuyaba...lol🤣🤭.

Tafi-tafi har Lami ta haifi ɗanta namiji yayanta Ibrahim baiyi aureba sedai anata fama da shi yace shi saiya samo *FARA ƳAR DUMA-DUMA* tukunna zai aura,wata rana tafiya ta kamashi zuwa garin *MISRA* inda ya sauka awani gida da suke da matuƙar karamci da mutunta ɗan adam,tunda yake gidan safe rana dare se anbashi abinci mai rai da lafiya,wata kyakkyawar budurwa ce ke kawo masa abinci wadda kullum idan ya tashi sai yayi wanka ya fesa turare mai ƙamshi saboda ya birgeta amma idan ta shigo kullum kanta a sunkuye bai taɓa haɗa ido da ita ba sedai yaita satar kallonta amma ita tana ajjewa zata juya ta risina ta masa sallama ta tafi.Muryarta kamar sarewa saboda daɗi,idan tayi sallama har wata duniya yake tafiya wadda baya dawowa sai yaji tana gaisheshi se yahau inda-inda,shidai yasan bashi da in'ina amma indai yayi tozali da ita sai ya zama tuburarren mai in'ina shi kansa har mamakin kansa yake yi yadda akayi yazama haka.

Kwanakin tafiyarsa suna ta matsowa amma ko sunanta bai sani ba dan haka yau ya ƙuduri aniyar lallai ko zai mutu yau se ya sani dan haka yaci ado yayi kyau da shi.Tana zuwa ya kalleta kanta aƙasa cikin in'inarsa yace...

"Am dan Allah ya..ya..ne su sunan ki"

Seda ta ɗanyi jim kaɗan saboda hausar tasa wai "Su sunan ki" to miye kuma su sunan ki? ta tambayi kanta,oh ko sunana yake nufi?dan dai ta tabbatar se ta ɗan ɗagp kanta taɗan kalleshi tare da cewa...

"ISMEY?" Ai gabaki ɗayanshi ya sandare dan tunda yake bai taɓa kyakkyawar mace aduniya kamarta ba danshi duk ƙasasen da yaje na kyawawan mata baiga tamkarta ba,daƙyar ya samu ya daidaita kansa yace daƙyar.."Eh nufi haka nake"

Saida tayi wani sassanyan murmushi wanda ya sake fiddoda zallar kyawun da Ubangiji ya zubawa fuskarta sannan tayi hanyar waje tana faɗin...

*"ƘURAINABU LAMIN"*

Koda ta fita ya daɗe yana maimaita sunan tare da addu'ar Allahsa rabonsa ce ita. Haka ya komo garin katsina cikin farin cikin amincewa da auransa da tayi,ko da yakoma yafaɗi yar garin da yakeso da komai da komai nata se Alhaji Bello yace ai indai kuɗi suna faɗa aji to se ɗansa ya aureta saboda ta faɗamasa aƙidar gidansu  ba'a bawa talaka aurensu kuma mutum ɗaya ta taɓa aurar bahaushe agidansu ita ce yayarta *MADINA* itama kuma anyi tata ɓurza kafin abashi ita saboda aunfison subawa asalin balarabe iyalinsu.

Ba'a ɗauki lokaci ba akaje nema masa auran *BAƘURAISHIYA*  wadda suke mata *SHUKHRAH*  sunsha baƙar wahala kafin su yarda su bashi ita tare da mata nasiha akan duk inda taje karta manta asalinta kuma karta bar tarbiyar da akayi mata.Haka kuwa kawota cikin garin kano dake kasuwancinsa yafi ƙarfi akanon aka ajjeta atamfatsetsen gida aljannar duniya,tunda dangin Ibrahim sukazo sukaga gidansa tsanar *ƘURAINABU(SHUKHRAH)* Ta dira azuƙatansu ba kamar Hajiya Lami danjitayi duk niya babu wadda ta tsana kamarta,hakama *MAMA HAUSU* ganin yadda Ibrahim yake ririta Shukhrah yasanya tabi ta tsaneta ko sunanta batason ji balle ganinta...





        *KUYI HAƘURI DA NI NIKAM BAZAN IYA DOGON TYPING BA BANJIN DAƊI WLLH,FREE PAGES SUN KUSA ƘAREWA PAH*




*ƳAR GATAN MAMA✍🏻*

✨HUZA'IYYA✨Where stories live. Discover now