HUZA'IYYA.F.P.3.

2 1 0
                                    


FREE P.3.

       Ya ƙarasa maganar cikin ƙaraji tare da sanya ragowar guntun sigarin hannunsa ya hau zuƙa kamar bazai bari ba,idanunsa sunyi ja kamar garwashin wuta ɓacin rai duk ya bayyana a ilahirin fuskarsa banda kallon Hajiyar babu abinda yake yi,shessheƙar Huza'iyya ce ta dawo da shi cikin hankalinsa tare da isa inda ta ke ya sunkuceta yayi waje da ita batare da ya kalli Hajiyar ba sata amotarshi yayi mata key yabar harabar gidan.

Turus Hajiya LAMI ta tsaya tana mamakin to yaushe ma yazo garin "Wato Huza'iyya ta fini matsayi awajansa da har zaishigo yaimin wannan ɗibar albarkar akanta? to wallahi se na yi maganinsu su duka bama kamar ita munafukar da bansan me tayiwa tilon yaro na abin alfaharina yau se ta gwanmaci aɗauki rayuwarta da ƙuncin da zan sakata" Haka Hajiyar taita sababinta kafin taja sagaggun ƙafafuwanta da taji sunyi mata nauyi tashige gidan tana ta buga tsaki.

@@@@
    Koda ya fita bai zame da ita ko'ina ba se asibitin HUDA dake kan titin Nassarawa GRA wanda manyan masuji da kuɗi ne  kaɗai suke iya shigarsa,ba tare da wani ɓata lokaci ba aka karɓeta tare da bata temakon gaggawa dan zuwa lokacin har ta suma saboda ba ƙaramar wahala tasha ba.Ficewa  yayi daga ɗakin ya ɗau wayarsa tare da kiran abokinsa DEEN ya kwashe komai ya faɗamasa tare da neman alfarmar ya sanar da matarshi yana neman alfarmar kai Huza'iyya gidan na kwana biyu yanason hankalinta ya kwanta.Ba'a ɗauki wani lokaci ba sega DEEN shi da matarsa RUMAISA sun iso amotar Rumaisan.Cike da farin ciki FU'AD ya ƙarasa wajan motar yasa hannu ya buɗe ɓangaren DEEN tare da miƙa masa hannu yana faɗin...

"Lallaine abokina kace harka iso baka jiramu ba"

Murmushi yayi tare da ƙarasa fitowa yana maidamasa martani da faɗin...

" Ah haba Fu'ad! Ya za'ai ka nemi alfarma awajena ka rasa? ai tare da ita muke tafe ta azazzaleni muzo mu tafi da Huza'iyya kasan suna ɗasawa da mutuniyar taka Hhhh!"

DEEN ya ƙarasa maganar yana dariya.Bayan sun gaisa da Rumaisa ne suka      ɗunguma sukayi ɗakin da Huza'iyya ta ke.Ko da suka shiga ta ɗan samu nutsuwa kuma likitan ya sanar da su cewa ba haihuwa bace ba juyine kuma yakanyi  haka lokaci zuwa lokaci mace ta ɗauka haihuwa zatayi dan wasu ma sunajin wahalarsa fiye da lokacin haihuwar,sannan kuma ya basu umarni akan lallai aringa bata kyakkyawar kulawa dan tana buƙatar a kula da itan.Basu zauna ba suka mata sannu sannan suka shiga motarsu itama ta shiga motar Fu'ad bisa umarninsa.

Bayan sun ɗauki hanya ne ya ke sake yimata sannu tare da sanar da ita gidansu Deen zata zauna har ta samu ta sauka lafiya,sannan ya karɓi wayarta ya saka lambobin  ƴan gidan dukansu a black list harta Hajiya tasa kaɗai ya bari free sannan ya bata wayarta.Ko da suka je gidan babu yadda baiyi da ita ba akan ta faɗamasa abubuwan da ta ke fuskanta agidan amma ta dage babu komai wanda hakan ya sake rura wutar soyayyarta a zuciyarsa dan yanason mace mai sirri dukda yana tabbacin bazata iya faɗar laifin mahaifiyarsa a gaban idonsa ba.

Bayan sun isa ya jima agidan suna hira shi da Deen yana sake yi masa godiya seda zai tafi Deen ya rakashi waje tare da dafa kafaɗarshi yana faɗin...

"Am abokina ina maka fatan alkairi akan Huza'iyya sannan ina daɗa roƙonka akan ka kuma rage shaye-shayen waɗannan abubuwan marasa amfani babu abinda zasu yimaka sedai su cutar dakai,kuma idan ka cutu kasan dai bazata aureka da nakasa ba ko?"

Ya ƙarasa maganar yana kashe masa ido ɗaya tare da dukan kafaɗarshi. Murmushi Fu'ad yayi tare da gyara tsayuwarsa jikin motarsa ya kalli Deen yace...

"Abokina har kullum ina alfahari da kai dan inada tabbacin so na kakeyi da zuciyarka ɗaya,nagode sosai kuma banda abinka ai rashinta ne yake birkitani amma yanzu zankafa na tsare se na mallaketa na zame mata bangon jingina wanda zatayi alfahari da ni,karka damu na rage shaye-shaye 60% kaga kuwa da yuwuwar suma ragowar na watsar da su"

Ahakadai suka ɗan tattauna maganganu masu muhimmanci tare da masa gargaɗi akan karyabar ƙofar da kowa zaisan Huza'iyya tana gidan,babu wata gardama ya amince sannan suka yi sallama ya tafi shikuma ya juya cikin gidan nasa.

Ko da ya dawo tuni Rumaisa ta nunawa Huza'iyya ɗakin da zata zauna wanda yake komai na more rayuwa a cikinsa,hakan yasanya Huza'iyya farin ciki inda ƙarƙashin zuciyarta kuma ta ke fargabar haɗuwarta da Hajiya da tunanin me zai biyo baya,ta daɗe tana tunani kafin tayi alwala ta zauna tayi sallolinta sannan ta kwanta awaje mai kyau wanda har ƙwallah ya sakata dan rabonta da kwanciya mai dali tunda ta baro gidan Alhaji ta dawo gida.

@@@@
     Koda Fu'ad ya dawo  bai zarce ɓangarensa ba se ya shiga gidan inda ya tarar da Hajiya tana zaune aparlon tana tunanin ina suke yaushe zasu dawo amma ga mamakinta se ta ganshi shi kaɗai wanda hakan yasa ta zabura ta miƙe tare da ce masa...




*ƳAR GATAN MAMA✍🏻.*

✨HUZA'IYYA✨Where stories live. Discover now