HUZA'IYYA F.P.10

1 1 0
                                    

*💦HUZA'IYYA💦**




*LABARI/RUBUTAWA*
*KHADIJA S.SAMINU*
*(ƳAR GATAN MAMA)*


            *MARUBUCIYAR...*

   Rayuwar mu.
   A Wani Gida.
   Maganin kar ayi..!
   Rana dubu...
   Wata Duniya.
              nd now...*💦HUZA'IYYA💦.*


*NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYA GA ƊAUKACIN ƳAN ƘUNGIYAR YI DOMIN ALLAH KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YAJA DA RANKU YA ƘARA MUKU FASAHA DA ƘOƘARIN ILIMANTAR DA AL'UMMA,INA GAISUWA A GAREKU*

NA KUƊINE MAI BUƘATA TAYIMIN MAGANA 07047530638.


LAST FREE P.10.

✨✨✨
            Ko da naje danƙareriyar waya ya bani ƙirar Samsung fara kar mai azabar kyawu wadda ganin farko ta ratsa ko wane ɓangare na jiki na,godiya na shiga yi masa tare da nuna masa farin cikina sosai aikwa yaita murmusawa yana kaɗa kai kafin yamin sallama ya tafi dan ya kwanta nima nayi cikin gidan cike da farin ciki.Wata dabara ce ta faɗomin arai aikwa nan da nan na ɗaga rigata na saka kwalin wayar ajikina zani na ya riƙe gam sannan na haɗe fuskata na koma Huza'iyyata mara walwala na shiga ina sussunne kai ban ankaraba naji maganar Hajiya na faɗin...

"Miƙomin nan baƙar munafuka wadda tagaji baƙin halin sunkui da kai irin na uwarta wadda dangin arziƙima bata da saida ɗan uwana ya lulluɓa mata bargon suttura ya liƙamana,kuma ki zayyanemin me kike cemasa"

Cike da karaya naje na durƙusa agabanta tare da ciro wayar na miƙa mata wanda se asannan na gane ashe batasan ya bani ba kawai faɗatayi dan ta bugi cikina aikwa tayi nasara ta bugaɗin fan haka ta karɓa tana ta surfa masifa da bala'i da masifa tare da sakin wayar aƙasa,na tsorata da sakin wayar dan haka nakai hannu zantare ta ɗaukeni da mari ɓangaren dama da hagu na dafe kuncina ina zubar da hawayen da ya sake ɓata mata rai ta tashi ta rufeni da duka tare da faɗin aigwanda ma nafara fitaɗin na nemo miji ta aurar dani danko tana yawo tsirara bazata bari ɗanta ya aureni ba.

Yayyafi ne ya tasheni daga tsakar gidan saboda tana gama dukana ta haye sama ƴaƴanta kowa yayi makwancinsa nikuma na sunkuya ina kukana ahaka ɓarawon bacci yayi gaba dani seda naji ruwa ajikina na tashi a firgice tare da ɗaukar wayar tawa da har an fasamin ita hatta murfinta ya fashe bansan sanda nakuma fashewa da wani sabon kukan ba.

Ganin daren yayi na ɗauro alwala nayi nafilfili na roƙi Ubangijina buƙatuna sannan naje na gyara wajen kwanciyata na kwanta tare da saka tsowon layina awayar da sabon da Yaya Fu'ad ya bani yau,aikwa kamar jira suke na saka saƙuna sukahau shigowa na Mtn da na mutane wanda nake da tabbacin samari ne,kayan makaranta ta na ɗauka nasanya iron na gogesu luf dasu na ɗakko da Shamsiyya na goge dan nasan ba ƙaramin aikin Hajiya bane tace da tsowon na Shamsiyya zani itakuma taje da nawan dan haka na goge.Bayan na kammala ne na sake addu'a na kwanta bacci ya ɗauke ni ban farkaba se asaalatu.

Ko da safiya tayi kafin su tashi nayi wanke-wanke nayi shara yayinda na ɗora ruwan wanka,se da na shirya tsaf sannan suka firfito suma suka shirya Yaya Fu'ad yazo muka tafi da shi.

Babu wasu manyan sururai aka karɓeni aka kaini babban aji na ƴan hadda ba ajinsu Shamsiyya ba dan ita a yadda naji bata da ƙoƙari shiyasa aka maidata baya,banji daɗi ba amma haka na zauna a jinmu malamai mabanbanta suna shigowa sunayi mana karatu kuma babu laifi ana fahinta sosai nidai sai farin ciki nake.

Wata a ajinmu mai suna *RAHMATUL'AYNI* Ita ce take ta shisshigemin yayin sa nima naji lokaci ɗaya ta shiga ta shiga raina aikwa mukaita hira dukda ni banfiye biyemata ba amma ahaka munsaba cikin lokaci ƙanƙani yanda sauran ƴan ajin se mamaki sukeyi dan ba kowa take yiwa magana ba acewarsu dan taganni kyakkyawa nafita kyau ne.

Sosai nake fahimtar karatu yayinda kusan kullum nafita kafin nadawo senayi samari kuma cikinsu se an sami wanda zai biyo ni gida,haka-haka harna haɗu da wani mai suna *SAGIR* wanda zaiyi sa'an Yaya *FU'AD*.....





ƳAR GATAN MAMA✍🏻.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 16, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

✨HUZA'IYYA✨Where stories live. Discover now