HUZA'IYYAH. F.P.7

0 1 0
                                    

*💦HUZA'IYYA💦**




*LABARI/RUBUTAWA*
*KHADIJA S.SAMINU*
*(ƳAR GATAN MAMA)*


            *MARUBUCIYAR...*

   Rayuwar mu.
   A Wani Gida.
   Maganin kar ayi..!
   Rana dubu...
   Wata Duniya.
              nd now...
*💦HUZA'IYYA💦.*


*NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYA GA ƊAUKACIN ƳAN ƘUNGIYAR YI DOMIN ALLAH KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YAJA DA RANKU YA ƘARA MUKU FASAHA DA ƘOƘARIN ILIMANTAR DA AL'UMMA,INA GAISUWA A GAREKU*

FREE P.7.



Baba na yana da wata huɗu da rasuwa Allah ya jarabci Mahaifinsa *ALHAJI BELLO*  da wata rashin lafiya komai sedai ayi masa,wanda wannan lokacin yayi dai-dai da lokacin da zamuyi final exam.Nayi kukan rashin Mahaifina saboda alƙawarirrikan da ya yimini idan na kammala secondary school,yana daga cikin burinsa naci gaba da karatu na zama babbar likita nima na tallafawa *ƘASATA* da *AL'UMMA TA* amma sedai kash! Mutuwa mai yankan ƙauna ta raba ni da shi,ganin yanayi na ya fara canzawa ina yawaita tunanin Mahaifi na yasa Mamata *AISHA* ta kwantar mini da hankali da kalamai masu daɗi tare da jaddadamin na kwantar da hankali na babu abinda zai hanani se ikon Allah.Hakan ya kwantar mini da hankali sosai jin zanci gaba da karatu burina zai cika.

Bayan kwana biyu kasancewar muna zaman jiran result yasa samari na na makaranta dama na unguwa da kuma wanda bansansu ba suka dinga tururruwar zuwa gidanmu,tun ina share su har nake kulasu bisa tilastawar Mamata acewarta ai na isa auren dan haka korar masoya ba nawa bane na nutsu nasan me ke min ciwo,haka zata zauna taita wayarmin da kai akan mu'amala da samari dama ƙawaye,bata jin kunyata sam wajan faɗamin komai game da soyayya sedai ma wani sa'ilin ni nakejin kunyarta na kasa kallonta itakuma taita basarwa.Mafiya yawan lokuta idan nayi baƙo bata bari na na fita saina sanya tafkeken hijabi mai kauri saboda Allah yayimin kyawun sura komai nawa abin kallo ne agurin mata ma ƴan uwa na balle maza,tun ana faɗamin yanayin girman halittuna ina musawa har ni kaina na dawo ina ɓoyewa saboda banson yawan magana,haka-haka dai har Allah ya haɗa jini na da wani mai suna *MU'AZZAM* Yana da kyawu da kyawawan halaye daɗin daɗawa kuma sunansa yanamin daɗi kasancewar sunan mahaifi na ne,wata iriyar soyayya ce ta shiga tsakaninmu wadda se an tona kafin asamu irinta,munyiwa kanmu alƙawarirrika masu yawa wanda muke da burin cikasu idan muka mallaki junanmu.

Ni kaina bazan iya faɗamiki irin son da nakewa MU'AZZAM ba,saboda wani irin so nake yi masa wanda shi ma nake da tabbacin yana yimin son da ko kansa banajin yana yiwa,bai wani yi zaman ƙasar nan sosai ba kasancewar a ƙasar waje yayi karatunshi har ya kammala tukunna ya dawo,dan haka idan mace ta kalleshi se ta kuma kallonshi dan ƙawayena so tari suna yaba kyansa dukda ba ganinshi suka yiba amma yadda nake zayyana musu shi kowacce acikinsu mafarkin samun irinshi suke yi yayinda wasu shiɗinma suke mafarkin samu.

Bazan manta da *HUSNA* ba wadda muke sa'anni da ita,katangar gidanmu na gugan ta gidansu haka muke,sau tari nakan ga ta shigo aduk sanda Mu'azzam yazo se tazo cikin kyakkyawar shiga duk  da bawani kuɗi garesu ba amma tana da kaya masu tsada kasancewar tana sona ita da sauran mutan gidansu yasa sanda Babana da yana da rai yake yawan yi mata ɗinki wasuma iri ɗaya yake yimana,nakan yi mamakin ganinta amma se nake sharewa har seda shi da kansa yake cemin nayiwa ƙawata magana shi bayason tana shisshigemasa,ban kuma tsinkewa da lamarinta ba se da yazo yanamin godiya wai turaren da na aika masa yayi masa daɗi sosai,koda na tambayeshi wa na aiko se yacemin Husna.

Nayi mamaki sosai amma se na share bannuna masa ba nayi murmushi muka cigaba da hira,bayan ɗan lokaci iyayensa suka zo gidanmu suka haɗu da ƴan uwan Mahaifina da Kakata da yake ta fama da jiki baya iya komai sedai ayi masa,murna kam nashata a wannan ranar dan gani nakeyi kamar ma ankaini gidansa ne saboda sanya ranarmu da akayi wata uku masu zuwa...

Sannu-Sannu bata hana zuwa sai gashi lokacin biki yayi gaf dan har kayan lefena ankawo kaya na alfarma da ke daga gidan wayayyu aka kawo komai se Masha Allahu dan sedai baƙar hassada amma kowa yazo sedai kaji yana faɗin "Huza'iyya ansha kaya,gaskiya yayi ƙoƙari".Haka aɓangaren Mamata Aisha tana ta shirye-shiryen biki na dan gyara take yimin bana wasa ba ko yaya na zauna a waje na tashi sena bar ƙamshi na a wajan dan wata ƴar maiduguri ce ta gyara ni gyara mai suna gyara,babu abinda ba'ayiminba abinka da farar mace se ɗaukar ido nake yi kamar ka sace ni inka ganni,nayi wani irin kyau da ni kaina idan na kalli madubi se nayiwa Ubangiji tasbihi daya kyautata halittata.

Shi kuwa Mu'azzam da yazo ya ganni kusan zaucewa yayi saboda gani na yayi kamar hurul'ayn danshi cewa yayi ko a aljanna aka bashi mai iya kyawuna yasan yafi maza sama da dubu,idan tazo daƙyar nake iya guduwa danshi baiƙi mukwana yana kallona yana faɗin nayi kyau ba.

Saura kwana uku a ɗaura aure wani tashin hankali wanda bazan taɓa mantawa sa shiba ya same ni wanda har seda yayi barazanar rabani da numfashi na.

Duk wani masoyi na yashiga cikin tashin hankali babu kamar Mamata dannikam banma san meke faruwa ba dan tuni na.....






*ƳAR GATAN MAMA✍🏻.*

✨HUZA'IYYA✨Where stories live. Discover now