HUZA'IYYAH. F.P.6

1 1 0
                                    

*💦HUZA'IYYA💦**




*LABARI/RUBUTAWA*
*KHADIJA S.SAMINU*
*(ƳAR GATAN MAMA)*


            *MARUBUCIYAR...*

   Rayuwar mu.
   A Wani Gida.
   Maganin kar ayi..!
   Rana dubu...
   Wata Duniya.
              nd now...
*💦HUZA'IYYA💦.*


*NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYA GA ƊAUKACIN ƳAN ƘUNGIYAR YI DOMIN ALLAH KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YAJA DA RANKU YA ƘARA MUKU FASAHA DA ƘOƘARIN ILIMANTAR DA AL'UMMA,INA GAISUWA A GAREKU**

FREE P.6.

.........Duk wasu hidindimu da yake musu basa gani kullum hangen abinda yake yiwa *BAƘURAISHIYA* suke yi,ko yaushe Hajiya Lami sake zuga Mama Hausu take yi akan Ibrahim yazama mijin tace mace ta haifawa dan haka seta tashi tsaye.Mama Hausu kuwa kullum sake hawa take yi wutar tsanar Baƙuraishiya na sake ruruwa azuciyarta.

Duk wata kulawa da mace ta ke nema awajan namiji Baƙuraishiya tana samunta saboda son da Alhaji Ibrahim yake yimata bana wasa bane.Wata rana kwatsam sega Baƙuraishiya da ciki,zo kuga murna gun Alhaji Ibrahim da Alhaji Bello da ke murna samun jika daga ɗansa namiji,yayinda Mama Hausu takaicinma samun cikin take yi dan taso Baƙuraishiya juya ce yadda ɗanta zai saurin tsanarta saboda son haihuwa amma segata zata haihu.

Intaƙaicemiki dai ahaka mamana ta haifeni cikin dangin mijin da basa ƙaunarta basa ƙaunar abinda ya shafeta,tun bayan aurensu bata taɓa zuwa garinsu ba se bayan tayi arba'in ne taimasa maganar zuwa gida Allah yasa ya amince,dan haka tafara shirin zuwa taga ƴan uwanta.Ko da suka isa garin sukaje gidansu se sukaga babu kowa gidanma ya zube kuma da alama andaɗe da barin gidan,ahaka dai suka dawo ba tare dasun samu gamsasshen bayani akan gidan da mutanen gidan ba.

Bayan na shekara uku ne Mamata ta sake ɗaukar wani cikin,cikin yazo mata da wani irin laulayi mai matuƙar wahala bata iya cin komai idan taci se ya dawo,ahaka dai suke rainon cikin ita da Babana cikin so da ƙauna inda gefe nikuma nake wani irin girma najin daɗin rayuwa.Tafi-tafi har cikin ya girma inda wajan haifar wannan cikin Allah ya ɗauki ran Mahaifiyata.Babana yayi kukan rashinta kukan da bayajin ya taɓa irinsa ko kuma zaitaɓa agaba,nikuwa lokacin banson wani zafin mutuwa saidai akai-akai nakan tambayeshi ina mama na saidai yace "Huza'iyya zamu haɗu da ita" kullum dai amsar kenan babu wata tun inayi har na manta.

Bayan lokaci yaja dangin Babana ba yadda basui ba akan ya basu ni amma hakan yaci tura yace cikinsu baiga wanda zai iya bawa ɗansa ba wanda hakan ya kuma sakawa suka tsaneni tsanar da tafi ta Mahaifiyata,tsawon shekara biyu da ɗoriya ya kasa yin aure inda Mama Hausu ta matsamai ko ya samo ko ta samomai wanda hakan ya tilastamasa ya auri wata babbar mace da mijinta ya mutu bata taɓa haihuwa ba ya kawota gidan.Allah ya zuba mata ƙaunata dan ruƙon tsakani sa Allah ta ke yimini, dangin babana sunsha wulaƙantata akaina amma ko a jikinta jina ta ke kamar ƴar cikinta har bata fatan abinda zai rabamu da ita afaɗin wannan duniya.


Bayan shekara goma sha biyu lokacin inada shekaru goma sha bakwai a  duniya Allah ya ɗauki ran mahaifi na ba ciwo ba komai wanda wannan mutuwa ta daki zuƙatan mutane da dama ba kamar matarsa *AISHA* dake ruƙona.

Tayi kukan rashin adalin miji nagartacce wanda yake tausayawa wanda ke ƙasansa,tayimin kukan rashin jajirtaccen mahaifi wanda yafi ubanni dubu wajan kula da ɗiyarsa wato ni,haka nima nayi kuka nakuma kokawa kaina wannan babban rashi domin asanda na rasa mahaifiyata bansan ɗacin mutuwa ba ballantana najishi,wannan kuwa ni kainama abakina ji nake kamar ɗacin mutuwarne aciki saboda yadda nake jin testing ɗinsa bana iya tantance masa dan hatta ruwa ma bason shansa nake yi ba,na saka mutuwar nan araina wadda ita ce nake ganinta mutuwa fiye da ta mahaifiyata dan banson ciwon rashin mahaifiya ba saboda yadda Mamata *Aisha* ta ɗaukemin duk wani kaɗaici da mara uwa araye yake shiga bannemi komai a wajanta na rasa ba,kafin na buƙaci abu tasan da cewar ina buƙatarsa,ci na sha na makwancina duka ta sanya ana kulamin da su yayinda abinda ya zama dole ni zan kula saita sanyamin hannu nake yinshi saboda kasancewar bansaba da aikin wahala ba ko kaɗan.

Haka dai aka gama zaman makoki cikin jimami yayinda dangin mahaifina ta ciki na ciki ne kawai dan an zuga Mama *Hausu* sosai akaina ta sake yimin wata tsanar da tafi wadda take yimin ita da su Hajiya *Lami*. Ko kallonta nayi muka haɗa ido se tayimin wani kallo wanda babu komai cikinsa se zallar tsanata dan acewarta Mahaifiyata *Ƙurainabu* ita ce saboda naci da maita tana lahira ta biyo Mahaifina tazo ta tafi dashi dan dama ya cemata yayi mafarkinta tana wani tafkeken Lambu wanda aka ƙawatashi da korayen furanni masu ɗaukar ido ga wani ƙaton tafkin ruwa fari kar yana kwarara gwanin birgewa yayinda gefensa kuma wata bishiyar dabino ce nunannu tana tsiga tana sha,ko da ta ganshi se ta nufo inda yake hannunta ɗauke da dabinon da tataccen ruwan inibi ahannunta ta iso tana sakar masa wani ƙayataccen murmushi da bai taɓa ganinta da shiba se lokacin,can gefenta wani kyakkyawan jariri ne shima jajur kamar ita yana ta wasa tare da ɗaga ƙafafunsa,ko da ta iso inda yake se ta miƙomin tataccen ruwan inibi tanamai nuni da ya karɓa yasha amma se ya kasa karɓa shi dai kawai kallonta yake yi,ganin bai karɓa ba kawai se yaga ta juya tana wani irin taku na ƙasaita kafin yayi wani yunƙuri tuni tabi wata hanya mai maɗaukakin haske ta ɓace ɓat ya nemeta ya rasa.

Daga wannan mafarki bai sake cewa da ita yayi mafarki ba kawai saijin mutuwarsa tayi dan haka ta ɗora alhakin mutuwar kan *Ƙurainabu* wanda hukuncinta kuma *Huza'iyya* ce zata karɓe shi.Hantara kyara babu wanda bansha ba dukda Mamata Aisha na matuƙar ƙoƙari akaina da bani kariya daga kaidinsu,domin idan tasan zasu zo gidanma cewa ta ke nashiga ɗaki na kulle na shiga da makullin komai za'ayi kar na fito dan batasonma mu haɗu dasu suyimin kallon da raina zai sosu harsu sanyamin wani tabo a zuciyata,ko yaushe bani haƙuri ta ke yi tare da nunamin halin rayuwa tana nunamin nayi taka tsan-tsan kodan gaba domin rayuwa bata da tabbas.

Babana yana da wata huɗu da rasuwa Allah...








*ƳAR GATAN MAMA✍🏻.*

✨HUZA'IYYA✨Where stories live. Discover now