HUZA'IYYA. F.P.9

1 1 0
                                    

*💦HUZA'IYYA💦**




*LABARI/RUBUTAWA*
*KHADIJA S.SAMINU*
*(ƳAR GATAN MAMA)*


            *MARUBUCIYAR...*

   Rayuwar mu.
   A Wani Gida.
   Maganin kar ayi..!
   Rana dubu...
   Wata Duniya.
              nd now...*💦HUZA'IYYA💦.*


*NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYA GA ƊAUKACIN ƳAN ƘUNGIYAR YI DOMIN ALLAH KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YAJA DA RANKU YA ƘARA MUKU FASAHA DA ƘOƘARIN ILIMANTAR DA AL'UMMA,INA GAISUWA A GAREKU*



FREE P.9.


✨✨✨

        Bayan bata bani abincin rana ba haka malamina zaizo yaita ɗuramin karatun da ba fahimta nake yi ba saidai kawai na jishi saboda yunwa,dan so tari idan na karya bayan cikina ya naɗi yunwa amayosa nake yi wanda hakan ke haddasamin galabaita ba ƴar ƙanƙanuwa ba,wannan aman da nayi ba zaisa ta bani wani abincin naci ba sedai idan ina sallah nasha kukana Ubangijina na kallona kuma yana jina sai dai lokacin yayewar ƙaddarata ne baiyi ba,haka zanta kuka har na idar na ɗora daga inda na tsaya dan ko lokacin addu'o'in bayan sallar farilla bana samun yi saidai nayisu a tsaye hakan yasa duk wasu buƙatuna acikin sujjada nake roƙarsu ina mai sakankancewa da zai amsamin duk daren daɗewa.Fuskantar ina jimawa idan ina sallah yasa ta koma zama kusa dani idan zanyi wanda hakan yasa dole nake jan ƙananun surori nayi sauri na sallame na ɗora da bautar da na saba.

Kwatsam ana haka babban ɗanta *FU'AD* ya dawo daga ƙasar waje ya kammala karatunshi.Fu'ad namiji ne har namiji irin wanda duk wata budurwa ke mafarkin samu amatsayin abokin rayuwarta domin duk inda ake son kaiwa Fu'ad! Yakai,yana da tsayi da jikinsa madaidaici ke gabaki ɗayanshi dai ya haɗu iya haɗuwa uwa uba kyakkywan hali da kyakkyawar ɗabi'a,tunda Fu'ad ya dawo ya ƙyalla idonsa a kaina yake shigemini idan yana gidan babu wanda yake kira saini wanda hakan yake ƙonawa Hajiya LAMI rai matuƙa amma bata nuna masa saboda batason ya gane irin tsanar da tayimini dan halinsa ya banbanta da sauran ƴaƴanta,ta rage gasamin aya ahannu domin cikin kaso biyar uku nake yi cikin wahalhalun gidan saidai yanzu ta wajabtamin sanya hijabi ba dare ba rana ke har dare lokacin bacci dashi nake bacci ajikina saboda Fu'ad babu lokacin da baya iya shigowa dan se lokacin baccinmu ya kusa zai shigo cin abinci bazaiciba saiya kirani yace na zuba masa,sannan ya ce nasanya hannu muci,nikam bana cutar kaina haka nake naɗe hannun hijabina naci nayi nak dan dama ba ƙoshin nayi ba akwai ɓoyayyiyar yunwa a tare dani,duk loma idan nakai na ɗaga idona saimun haɗa ido dashi ya kafeni da idanunsa shanyayyu masu ruɗani dan harga Allah ina mugun sonshi tunkafin ya zama namiji kamar yanzu tunkan yabar ƙasarnan yana yawan zuwan gidanmu mu daɗe muna hira da Mamata *AISHA* hakan da yake ba ƙaramin daɗi nake jiba dan shi kaɗaine cikin dangin mahaifina yafito ya nuna yana ƙaunata da gaskiya dan haka nima ya zama wata tsoka dake cikin ƙirjina.Na shiga farin ciki wanda hakan ya ƙuntata Hajiya Lami,bansan ya akaiba kawai kwana biyu malamin da kemin karatu naga ya dena zuwa,se a kwana na ukunne Fu'ad ya shigo gidan hannunsa ɗauke da babbar leda ya miƙomin.

Kallon-Kallo aka shiga yi tsakanin Hajiya da Yaranta dama ni kaina,can dai na kalli ledar tare da buɗewa.

Uniform ne na islamiyyar dasu *SHAMSIYYA* budurwar ƴar Hajiya wadda muke sa'anni da ita suke zuwa kala har biyu da takalma biyu se kuma jaka da kafatanin littattafan da akeyimusu aciki,sedai hijabin na ganshi yaso yafi ƙarfina ma zumbulele dashi.

"Wallahi Fu'ad baka isa ba,cema akayi bata karatu ne? Ƴar amanar tawa zan bari tana fita rana da iska su koɗar da ita,to babu inda zataje agida zatayi karatu har Allah ya kawo miji na nunawa sa'a na auratta"

Hajiyata miƙe tana faɗa cikin ɗaga murya yayin da Fu'ad ya tari numfashinta da cewa...

"Nidai Hajiya na rigada na gama abinda zanyi kuma gobe da safe zata fara zuwa dan bazai yuwu mace kamarta ace wani ƙaton gardi yazo ya sata agaba da sunan karatu ba,nan gaba Allah kaɗai yasan mai zai faru,kuma zancen amana ai muma ƴaƴanko amana ne meyasa Shamsiyya da Auta basu zauna akoyamusu a gidan ba?"

"Rashin kunya zakayimin akan ƴar tsintacciyar mage?"

"Tsintacciyar mage? Wace ce tsintacciyar magan to?kodai abinda ake faɗamin akan gidannan gaskiya ne?"

Ya tambaya fuskarsa ɗauke da bayyanannen ɓacin rai.Hajiya ce ta sauke ajiyar zuciyw ganin zai ɓaro mata ruwa yasa ta zauna tana faɗin...

"Ai saikai tayi ni bazan iya fitinarka ba tunda da faɗa ka shigo,bazaka bani haƙuri ba kashigo da kayan ƙanwarka baka nunaminba dan rashin ta ido"

Dariya kawai yayi tare da kirana nikuma nabi bayanshi aɗarare dan nasan yau da jaraba agidan nikam ko ba komai zan ringa yini awaje nasamu hutu.....

*ƳAR GATAN MAMA✍🏻*

✨HUZA'IYYA✨Where stories live. Discover now