WG-01

1.9K 64 5
                                    

©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye

Baya baya ta yi ta lankwasa kamar za ta fadi sai kuma ta yi gaba tare da cira kafarta ta dama sama kafar da ta sha ado da fararen yayan wuri ta buga a kasa cikin tabon lakar ruwan saman dake sauka, ta mika hannayenta duka biyu sama ta ware karan dake hannayenta ta buga su da karfi har sai da suka yi kara, sannan ta fara juya k'ugunta yayan wurin dake daure a kwankwasonta suka fara kara, a take maza da matan dake gurin suka hau tafi, masu ganguna irin na itace suna dukawa sai ta rufe ido tana taka rawar da ta zame musu ta al'adar wanda aka saba gabatarwa sau daya a kowace shekara.

Wata siririyar busar sarewar ce ta rika tashi a tsakanin mazanjen da ke buga gangunan kidan, a take kowa ya fara rausayar da kai domin busa ce dake saukar da natsuwa da annashuwa tare da nishadin zuciyar duk wani mai saurarenta, ciki kuwa har da Sarkin Garin Garuk da yan majalisun masarautarsa da kuma fadawansa. Busar sarewa ce da babu inda zaka taba jin ta a duniya sai a garin Garuk. Ko a cikin garin babu wanda ya iya sarrafa halshe da numfashi ya busa sarewar sai Waira da dan'uwanta Eid, busar sarewa ce da Eid ya kirkireta da tsananin karfin tsafin da babu wanda zai iya busar sai shi da kanwarsa Waira, ita ma kuma saboda ya amince mata ne, busar sarewa ce da ta zama haramun ga jama'ar garen su kwatanta kwaikwayonta ma balle har su gwada yi.

Busar sarewar ce, ke kara mata kuzari da karfin taka rawar da take, yadda take lankwasa da murza kugunta sai ka rantse da Allah babu ƙashi ko daya a jikinta, ruwan saman da ke sauka yana ta wanke datti da tsananin daudar dake jikinta, domin walki ne daure a kugunta sai wani katon ganyen data daura a kirjinta ya rufe breast dinta da a yanzu suke girma, a tsakanin guiwowyinta zuwa kafafuwanta a sake yake, haka ma cibiyarta a waje take, ta saki gashin kanta dake cinkushe ya kwanta har kusan mazaunanta, kunnuwanta na sanye da yan kunnen mai karamin kokon kan karamin tsuntsu kamar yadda wuyanta ma yake sanye da sarkar kokon kan maciji.

Ranar yau rana ce ta musamman ba ga jama'ar garin kadai ba, har ga yar sarkin masafa kuma jikar sarkin masafa na garin Garuk wato Waira.
Ranar yau rana ce da suka kadaice domin yin bikin abun bautarsu, da kuma bauta masa a tsawon ranar har zuwa lokacin gudanar da wannan rawar da Waira take takawa, a al'adar mutanen garin sau daya suke bautawa abun bautarsu a shekara, a ka'idar bikin ko wace shekara da kalar yarinyar da ake zaba a bata damar taka rawa a biki, a bana ma an zabi Waira kamar yadda aka zabe ta a bara, saboda kwarewar da ta yi da kuma yadda ta iya bin salon busar tana motsa jikinta kamar wata hawainiya.
A irin wannan ranar ce kadai Waira take wanka, a irin wannan ranar ce kadai take raba jikinta da duk wani datti da kazantar da suke daukar shekara suna rayuwa a jikinta, wato sau daya tal Waira take wanka a shekara!

Waira matashiyar yarinyar ce yar kimanin shekara goma sha hudu, ya daya tilo a gurin sarkin matsafa na garin Garuk, kuma jika daya tak a gurin sarkin matsafa na garin Garuk, kuma ya daya tak mai jiran gadon sarauniyar matsafa na garin Garuk.
Waira kyakkyawa ce sosai irin kyan da karya mace take ta yi mata duba daya ta kawar da kai balle kuma namiji, fara ce fol irin farin nan mai kyau da ba kasafai kake samunsa a jikin fararen mutane ba sai zababbu, tana da yalwar gashin kai da ya cumuimuye da datti saboda rashin son wanka da tsabta, duk da yake gashi ba abun alfahari ba ne a gurin yan matan garin Garuk domin duk wanda ka duba kanta zaka ganta da gashi daga manya har yara, tun daga kan mazan ma sai wanda ya ga dama ya aske, balle kuma mata da suke ado da shi. Waira kyakkyawar matashiyar budurwa ce mai tasowa, mai tsananin farin jini a tsakanin mata sa'ainta masu tasowa, sai dai tsoron dan'uwanta wato cousin dinta Eid ya hana maza da yawa kusantar inda take. An yi ittifaki kaf a tahirin garin ba a taba yin kazamar yarinya irin Waira ba, ba kazanta ta bangarem abinci ko abin sha ba, kazanta a gurin tsabtace jiki, sam sam sam Waira bata son abun da zai hada jikinta da ruwa da sunan wanka sai a dole, kamar saukar ruwan sama ko kuma a inda ya zama dole sai an shiga ruwa sannan a wuce ta wani gurin, hakan ya saka ta shar'antawa kanta wanka sau daya a shekara, wato kamar dai yadda ake gabatar da bikin abun bautarsu a shekara bayan gama bikin take zuwa ta yi wanka, wannan ya saka ranar ta kara muhimmanci a gareta da kuma duk wani masoyinta.

WANI GARIWhere stories live. Discover now