13

470 29 3
                                    

Wani sabon tunanin ne ya zo masa hakan ya saka shi canja shawara, gefen hanya ya rika bi har ya samu wani Karamin shagon siyar da kaya, wani almajiri ya samu ya aika shi kiran mai shagon kasancewar akwai glass sai an bude za a shiga, ba shigar ce matsala ba rashin talkami da kuma rigar jikinsa ce matsala domin baya son ayi masa kallon mahaukaci. Almajirin na isa sai gaai shagon ya fito ya biyo bayansa. Tun kan ya isa Ameer ke masa kallon kasa da sama.

“Riga nake so wacce ta fi ko wace tsada, sai talkami idan kuna da su”

Shi ne abun da ya fada ya mika masa Atm din hannunsa tare da fada masa code.

“Akwai amman ba mu da machine din cire kudin, sai dai makocina shi kuma sai ya cire carjin dinshi”

“Ba matsala”

Ya fada ba tare da ya kalleshi ba, domin mutane kazanta suke ba shi a yanzu, Waira ma dake bayan motar jin yake kamar tana saman jikinta ne, kazantar dake jikinta ta lake masa a zuciya ya kasa manta abun da ya gani. Yana ji yana gani ya bata minti talatin a gurin kamin mutumen dake shakar Ameer ya kawo masa rigar da talkamin, domin jikinsa na bashi ba Ameer ba mutumen kwarai ba ne ganin sabuwar mota da aka buge gabanta gashi babu riga a jikinsa kuma babu talkami hakan na nuna sato motar yayi ko kuma wani abun dabam. Kallo daya Ameer yayi ma rigar da talkamin ya san ba ajinsa ba ne, sai dai babu yadda zai yi dole ya saka a haka, sai da yayi tsaki sannan ya karba tare da ATM din, a gaban mutumen ya saka rigar sannan ya ja motar yayi gaba, tafiya mai nisa yayi sannan ya saka talkamin ya faka motar gafen titi ya fita zuwa gurin wani mai shagon POS ya mika masa ATM din.

“300k nake so”

“Ranka ya dade ba za su samu ba, sai zuwa anjima sai dai 100+ idan kana so”

“Ba ni”

Mutumen ya fara aikin saka ATM din, dayan dake taya shi aiki kuma ya fara karga kudin, fuska babu annuri Ameer ke fada musu pin din, in less than 20min aka ciro kudin aka bashi ya karba, be damu da saka su aljihu ba ya riko su a hannu domin sun masa kazanta kasancewarsu tsofin kudi wasu ma sun yage sa'arsa daya sun saka masa su a leda. Bude motar yayi ya shiga ya dauki hanyar Kano sai da ya kusa isa gurin da police ke bada Hannu sai ya samu guri gefen titi ya faka motar inda ba za su hango shi ba, ya fita ya zagaya bayan motar da ya bude ya saka hannunsa ya warware nadin da yayi mata da carpet fuskarta ta fito, hakan nan ya samu kansa da tsaya yana kallon yadda hawaye suka bushe a fuskarta ga gashin kanta ya kara yamutsewa, abun ka da marar juriya sai amai ya sake cika masa baki da sauri yaja baya ya fara kwara amam dake fitowa daker domin babu komai a cikinsa sai yunwa, ya amayar da dan abun da ya ci jiya, gashi yau be saka komai a cikinsa ba. Cikin motar ya koma ya dauko gorar ruwa ya wanke bakinsa da fuskarsa, after that ya tuna ya taba abubuwa da yawa da be kamata hannunsa ya kai a fuskarsa ba tare da ya wanke ba.

“Ohhhhhh”

Ya furta yana jin wani irin bakin ciki, a sake ya bar motar kamar yadda ya bar bayan motar ma a bude, ya dauki kudin dake ledar ya bar ATM din da komai a ciki, ya fito daga gurin zuwa gurin babban titi tafiya yayi mai nisa a kafa sannan ya tsallaka dayan side din da zai maida shi cikin KT yana tafiya yana taron mota har ya samu wanda bata da mutane da yawa ta tsaya, one after the other ya rika bin mutun biyu da suke bayan motar da kallo kamin ya kalli direba da yake ganin idan ya shiga motar kamin su isa KT ma mutuwa zai yi, domin irin motar nan ce da bata da Ac glass din motar ma a harfice yake balle kuma mutanen ciki.

“Ku tafi kawai”

Bayan ya gama bata musu lokaci, be tsaya jin abin da za su fada ba yayi gaba abunsa, can kuma ya sake taron wata motar, yayi haka ya kai sau biyar sannan ya samu wanda mutun biyu ne kawai a gaban motar bayan babu kowa, sai dai ita ma bata da Ac kuma motar kasuwace irin mai rawa din nan idan ana tukawa, hakan na dai ya daure ya shiga yana jin wani zazzabin wahala na taso masa, tasha ya fada masa za su kai shi he can pay ko bawa suke so shi dai bukatarsa ya ganshi a tasha.
  Kamar yadda ya bukata haka suka kai shi har cikin tashar KT suka ce zai ba su 3k saboda lura da suka yi da alamar yana da su, ba musu ya bude ledar ya cire kudin da za su fi haka ya mika musu, sannan ya saka ragowar kudin aljihun wandonsa guda biyu ya bude motar ya fita.

WANI GARIWhere stories live. Discover now