12

390 29 1
                                    

Can kuma ya dago kanshi ya fito daga cikin motar,  ya nufi wasu itacen ya tsaya a gurin yana tunanin makomarsa, gida zai koma ya duba jikin mahaifinsa? Ko kuma a nan zai zauna inda be san kowa ba kuma ba shi da komai, and the most annoying part is duk wani abu da yayi amfani da shi na Nimra ne kanwar makiyinsa, tunanin mafita ya saka shi fara tafiya ya koma yar karamar hanyar nan da ya fito, ashe kaddara ke kiransa domin yana tsaka da leke hallitar nan ta da a bayan ya bar gurin ta fito tana dingishi ta nufi gurin shimfidarsa, wani biscuits din ta dauka ta taba ganin irin na dazun ne, kala ce kawai ta banbanta yasa ta jefar ta nufi inda ya aje Gel din da yayi wanka da shi ta dauka tana ta kallon gorar a rayuwarta bayan gorar zuba ruwa irin wanda ake da ice sai kuma ta kwarya bata san wata gorar ruwa ba, hakan ya saka ta daga ta sama tana kallo kamin ta sauke ta fara kwankwasawa can kuma ta kara kunne ta tana saurare, hakan be gamsar da ita ba sai da ta saka dayan hannunta tana shafa gorar, gurin da ta ga an yi hanyar da gel din zai fito ta kai bakinta tana tsotsowa abu ne da saba gani ba, hakan ya saka bata san dannawa ake sabulun ya fito ba, sai kufan da ya rage kawai ta samu a bakinta, abun ka da mutumen daji sai ta hade tana sauraren yadda dandanonsa yake. Jin babu dadi sai wani makaki da kumfa ya saka ta jefar ta nufi gurin ruwan da yayi wanka ta saka hannayenta biyu ta fara debar ruwan tana sha, a take cikinta ya kulle yan hanjin cikin suka murde ya fara mata ciwo. Tun da take a rayuwarta bata taba jin azabar yunwa irin wannan karon ba, a take ta fashe da kuka ta fadi a gurin ta dafe cikinta. Yana daga kafarsa ya kara matsawa gurin da take domin ita bata san ma yana kallonta sai ya ji abu ya dan taba masa kafa dauke kafar da yayi yana dubawa sai ga maciji, wani tsalle ya kara dakawa ya yi baya da sauri.

“Kai....”

Ya furta da mugun karfi wanda hakan yayi sanadiyar zaburar Waira da sauri ta tashi zaune tana kallon inda yake tsaye, babu abun da ya zo a zuciyarsa sai ita, a tunaninsa ita ta turo masa macijin har wani bangare na zuciyarsa na raya masa ita ma din macijiya ce. Da sauri Waira ta fito daga gurin idonta kamar za su fado tsabar kallon tsoron da take masa, ganin yayi baya sosai ya saka ta tsaya tana kallon abun da yake yi ma gudu, maciji ne ba wani babba sosai ba sai dai baki ne dake neman shigewa cikin ciyayin dake gurin, tsoron kwari irin maciji ko bera da wasu kananan abubuwan daji ba ba nata ba ne, domin duk wanda ya saba hawa itacen fruits baya tsoron maciji, musamnan icen ayaba, mango da kuma guava. Da dingishi ta nufi inda macijin ya bi tana lekonsa, ganin be yi nisa ba ya saka ta yi hanzarin bin bayansa, Ameer ya zaro ido yana takowa ya leketa. Dukawa ta yi ta saka hannunta ta cafki macijin da yake kokarin tashi tsaye sai ta rikoshi da hannunta ta mike tsaye.

“Bura'uba, yau na ga bala'i ganin ido”

Furucin da yayi ya saka ta juyo da sauri ta kalli inda yake tsaye, a take zuciyarta ta hau bugawa da sauri kamar zata fado, ta fi tsoronsa fiye da macijin dake hannunta, kamar gwalanniya haka take jin yarensa, a tsorace ta sake macijin da take da zimmar sakawa dutse ta kashe, be sauka a hannunta ba sai da ya cijeta.

“Ashashashash.... Atak Atak gil rièèk bisk...”

Bata san lokacin da ta yi furucin ba, tana yarfar da hannu tana ihu, fuskar mamaki Ameer yayi na jin yaren dake fita bakinta domin shi be taba jin yaren ba.

“Zaki yi kyau da gadi, yadda kike da rashin tsoron nan”

Ya fada sannan ya yayi baya baya yana kallon yadda ta fadi a gurin tana ihu gumi na karyo mata kamar wance aka watsawa ruwa, hannayensa ya daga masa.

“No offense...”

Ya furta tare da juyawa yayi tafiyarsa domin be ga mahadinshi da ita ba balle yace zai taimaka mata, ta ina ma zai iya taimakon wanda be sani ba? Ko mutuwa zai aka ce sai ya taba ta zai rayu be jin zai iya taba sai dai ya mutu din, balle ita ce zai ceto.

“Ahhhhhhh Ashhhh”

Ya dan tsaya yana jin karar da take, zuciyarsa na raya masa maybe ma hadin kai ne so ake ya taba ba, idan ba haka ba miyasa ta je ta taba macijin bayan bata da magani, a dayan bangaren zuciyarsa kuma na raya masa be kamata ya tafi ya barta a gurin a haka ba.

WANI GARIWhere stories live. Discover now