WG_06

486 31 2
                                    

WAIRA POV.

Tun daga lokacin da sarki yayi mata gargadi sai ta rika ware kanta dabam, daman can bata da abokan wasa sai dai tana dan shiga cikin mutane a yanzu kuma ko fita gida bata yi sai dole, Eid din ma da take sakewa da shi sai ta daina, sai dai hakan be saka ya kyale ta hakan be canja komai daga alakarsu idan bata fita ba shi zai zo ya same ta har cikin gidan, wani lokacin zai mata hira ranar da aljanun kwarai suke kanta sai ta amsa masa su yi ta hira yana bata labaran duniyar da ta sha banban da tata, wani lokacin kuma har ya gama abun da zai yi ya tafi ba zata ce masa komai ba. Sai dai tana jidadin idan yana labarta yadda wasu abubuwan suke a wasu garuruwan kuma yana fahimtar hakan a fuskarta domin ya fi kowa sanin halinta, abun da zai faranta mata ko ya bakanta mata rai.

Karar jirgin saman da ya ji ya saka shi riko hannunta ya fito da ita daga cikin dakin da take ya nuna mata jirgin saman, ba a yau ta fara ganinsa ko jin kararsa ba, sai dai yau ne rana ya farko da ya taba labarta mata cewar mutane ne a ciki, kuma tsuntsun yana daukar mutane da yawa har da kayansu, kana ya misalta mata yadda girmansa yake a kasa, ta bude baki sosai tana fiddo idonta waje.

“Kuma mutum ne yake tukawa?”

Ta tambaya tana saka hannunta ta tare ranar dake haska fuskarta.

“Mutum ke tukawa, yana da sauri fiye da tsuntsu”

Ta dawo da dubanta gurin fuskarsa tana murmushi.

“A ina yake sauka?”

Shi ma ya sauko da kansa kasa yana kallonta domin yayi mata tsawo sosai.

“A can garuruwansu, sun tanadar masa muhalli mai girma sosai wandanda za su hau sai an tantance su suke hawa, kuma sai sun biya kudi”

Ta sake juyawa tana kallon inda jirgin ya bi amman ko alamarsa babu.

“Me suke bautawa su? Miyasa komai na su ya banbanta da mu?”

“Saboda sun yarda sun karbi sauyin da duniya ta zo da shi, wanda mu muka kasa haka, na nesa da mu suna da addininai kala kala na kusa kuma na san ana kiransu Musulmai”

Ya amsa mata yana kallonta irin kallon nan dake tafiya da ruhin mai yinsa.

“Ina ma ace an baki damar fita wajen gari, da na bawa idanuwanki abinci, na zaga dake duniya ki ga wata rayuwar data banbanta da taki sai dai an iyakance miki iya cikin garin nan, fitarki a garin nan zai saka ki manta hanya dawowa, hakan kuma na nufi rasa rayuwarki gaba daya”

Ta sauke kanta kasa ta fara tafiya.

“Miyasa rayuwarsu take burgeka?”

“Rayuwarsu tana da kyau, wani abu na su yana burgewa ke ma da zaki leka ki gwada zama a cikinsu da kin jidadin rayuwar”

Bata sake ce masa komai ba har suka isa gurin da dade bata zauna ba saboda gargadin da Sarki yayi mata, zaunawa ta yi a gurin shi kuma ya tsaya yana kallon itatuwan da suka kawata gurin ga ruwan dake gudana gwanin sha'awa.

“Wasu kan kawata cikin gidajensu da irin wannan ruwan”

Ta yamutsa fuska.

“Saboda su yi wanka?”

Ya amsa da kai yana murmushi, a take ta ji ta tsani mutanen domin mutane masu yawan wanka ko son tsabta basa burgeta.

“Bana son zama a cikinsu”

Zaunawa yayi a gurin yana kallon ruwan da take kallo.

“Akwai wanda na taba haduwa da shi, a rana zai yi wanka kamar sau biyar ko sau goma saboda tsabta”

“Kuma baya jin wahala?”

“Baya ji kuma baya gajiya”

Ya juyo ya kalleta sai ya kama hannunta ya rike.

WANI GARIWhere stories live. Discover now