11

394 28 1
                                    

Ganin yana kokarin saka babbar rigarsa ta kalleshi tana karasa bude abincin.

“Abun da ka fi so ne na girka”

“Eh na ji kamshi ai, akwai abun da ya taso min na na gaggawa, zan ci abinci a waje”

Ya fada ba tare da ya kalli inda abincin yake ba, da fuskar mamaki ta sake kallonsa.

“Ba ala'adarka ba ce cin abinci a waje, na san na bata maka rai amman ka yi hakuri”

Ya juyo ya kalleta irin duba na manya yana tambayar abun da ta yi masa kamar da gaske be san abun da ya faru ba. 

“Akwai abun da kika min ne? Zan tafi sai na dawo”

Ya nufi kofa yana daidaita tsayuwar hularsa. Ganin haka ya saka ta mike tsaye.

“Ranka ya dade a gafarce ni, idan ba fushi kake da ni ba, me zai saka ba zaka ci abinci ba? Baka yi min irin haka sai idan shaidan yayi galaba akan mu”

Be amsa mata ba be kuma juyo ya kalleta ba har ya fice, komawa ta yi ta zauna ta rufe abincin tana jin wani iri a zuciyarta, ko kadan bata son ganin bacin ran mijinta kamar yadda shi ma baya son ganin bacin ranta, wannan na daga cikin abun da ya karawa rayuwar aurensu karko da dadewa. A bangarensa ta zauna tana ta jiran dawowarsa zuwansa har aka yi magariba aka sauko daga Sallah Isha'i Abiey be dawo gidan, tun abun na normal a zuciyarta har ya fara daga mata hankali, gurin karfe 1 na dare ta kira wayarsa ta shiga tana ringing amman be daga ba, a nan hankalinta ya tashi sosai ba na tsoron halin da yake ciki ba, sai na fushin da yayi da ita, domin be taba fushi ya kaurace mata ba, iyakar fushinsa da ita ya shareta ko ya kauracewa abincinta ko shimfida amman ban da kauracewa gida kuma ta kira shi ya ki dagawa, ba abu ne mai kyau ga namiji mai iyali ya kwana a waje ba, balle kuma shi da yake da manyan yayan da idan suka aikata hakan zai yi musu fada. Sai a lokacin ta fito daga bangare, daman ban tunanin rayuwarta ta baya babu abun da take gaba wunin yau ta ji shi wani iri. Bangarenta ta shigo sai ta samu wutar falonta a kunne Nimra na zaune saman kujera ta rumgume hannayenta, da sauri Ummi ta nufi gurinta domin duba lafiyarta, kusan wannan shi ne karo na farko da ta samu yarta Nimra a farke kuma a falon ba a dakinta ba, ko da tana kaiwa wannan lokacin ita dai bata taba gani ba, Namra ce mai dade wani lokacin bata yi bachi ba, tana kallon ko wani abun na dabam, sai kuma Maleek dake kwakwayar aljannu domin shi daren ne yafi jindadinsa fiye da rana.

“Nimra...”

Ta juyo ta kalli Ummi da idonta dake nuna alamar ba su shirya bata hadin kan yin bachi a yanzu ba. Ummi ta zauna kusa da ita tana fahimtar damuwar dake bayyana a fuskarta.

“Miya hana ki bachi a wannan lokacin Nimra?”

“Ummi ban sani ba, kawai kaina yana dan ciwo kuma bana jindadin rai na”

Lamari irin na uwa mai kula, sai ta danne nata damuwar ta fuskanci yarta.

“Akwai abun da yake damunki Nimra? Karki boye min”

“Ban sani ba, ina jin kamar akwai damuwar na tsoron rasa abun da ban riga na samu ba”

“Are you in love?”

“No, ban ce ina son sa ba, shi ma ba so na yake ba, amman shakuwar da muka fara ne bana son na rasa”

Ta fada idonta na cika taf da kwalla.

“Wani abun kika masa?”

“Shi yana kallon abun a matsayin laifi, amman ni a gurina ba laifi ba ne domin ban aikata dan na bata masa rai ko na cutar da shi ba, shi ya juya min baya yanzu ina ta kiran wayarsa be daga ba”

Be like a best friend to your kids, shi ne abun da Ummi ta yi har ta san damuwar Nimra, sannan ta fara kokarin kwantar mata da hankali.

“Ban san waye wannan Saurayin ba Nimra, amman na san yana da muhimmanci a gareki, domin duk wani abun da zai hana yata bachi a wannan lokacin to abu ne mai muhimmanci, kaurace miki da yayi da kuma fushi hakan na nuna cewar shi din mutum dan'adam wanda ke ma zaki iya yin abin da yayi, saboda haka ki daga masa kafa har sai ya sauko daga fushin, wani lokacin nisantar juna yana da amfani domin mutum zai gane muhimmancinka, kuma zai yi kokarin kiyaye laifin da ya saka aka yi haka agaba, kamar yadda zai bawa wanda aka cutar ko yayi fushi damar hucewa kuma yayi tunani, ki kwantar da hankalinki komai zai daidaita”

WANI GARIWhere stories live. Discover now