WG-10

378 27 1
                                    

Namra ta matsa kusa da ita ta karbi wayar ta duba hoton, sai gata suna kallon kallo ita da Nimra, sai a yanzu Namra take tuna ta sha ganinsa a media amman how come ta ganshi a fili bata gane shi ba. Nimra ta yi baya ta zauna saman kujera ba tare da tace komai ba, Namra shiru ta yi gudun kar ta furta abun da zai saka jefa yar'uwarta cikin matsala, domin idan Ummi ko Abiey suka san cewar ta bashi motarta za su yi mata fada sosai.
Ummi da wani abu mai kama da kashi ya tsoki kahon zuciyarta saboda ambatar sunan Ameer da na mahaifinsa da Mahmood yayi ya saka ta kasa zama ta kuma kasa motsawa zuciyar sai ciwo take mata.

“Ummi”

Namra ta kira sunanta ganin yadda ta tsaya kamar hoto, da sauri ta kalli Namra irin kallon kamar bata cikin hayyacinta, wani abu take ji mai kamar kuka kuma ba kukan ba, ba zata iya kiran da damuwa ba, haka kuma ba almara ba ce, wata kila mamaki take na sunan da ya zo daya, wata kila kuma wani bangare na zuciyarta gaskiya yake fada mata cewar Ameer dinta ne. Ko shiyasa Abiey yace a bar magana sun yi solving matsalar da mahaifinsa.? Daker ta iya tara yawun bakinta ta jika makoshinta sannan ta juya ta cira kafarta da take jin kamar ta shekara bata taka ta ba, ta fara tafiya.

“Ummi lafiya”

Mahmood ya tambaya domin hankalinsa yana gurinta, Nimra kam nata hankalin yana can gurin wani tunanin na dabam.

“Na'am”

Ummi ta amsa sannan ta juyo ta kalleshi gaba daya a rikece take irin rikicewar abun da kake tsammani ko tsoron ya faru, irin rikicewar wanda hankalinsa ke daf da gushewa, ba kuka take ba sai dai kana kallon fuskarsa kasan akwai tashin hankali a zuciyarta da fargaba.

“Lafiya”

Ya sake tambaya hakan ya hanyo hankalin Namra gareta, Hajiya Zahra ta kasa cewa komai kallonsa kawai take amman hankalinta da tunaninta suna wata duniyar ta dabam, ba tare da ta sake ce masa komai ba ta juya ta fara takawa suka bita da kallo har ta haye sama ta shige dakinta. Sai ta maida kofa ta rufe ta nufi gadonta ta zauna kwakwalwarta na tuna mata da abubuwan da suka faru a baya, yayin zuciyarta take soyuwa da kuskuren da ta aikata. A hankali Namra ta turo kofar dakin ta shigo rike da jakar Hajiya Zahra da wayarta da ta bari a falo.

“Ummi ga wayarki da jaka”

Wannan karon tana dagowa sai hawaye suka sauko mata, a sanyaye Namra ta ake jakar saman gadon ta zauna kusa da ita.

“Ummi lafiya?”

Sai ta yi saurin share hawayenta.

“Tsoro nake kar..... Kar.... Kar... Yaron ya sake yi ma Maleek wani abu....”

Ta fada ba dan komai ba sai dan ta kawar da tunanin Namra akan hawayenta.

“In shaa Allah ba zai sake ba, ko da ba a hukunta shi ba ai ya tsorata da yadda aka dauki abun da muhimmanci kuma kin ji har mahaifinsa ya kore shi”

Ummi ta juyo wasu hawayen na taruwa a fuskarta ta rike hannun Namra.

“Toh idan ya fada wani halin fa, nuna min hotonshi Namra”

“To koma minene ai shi ya jawa kansa, kuma hukuncin da mahaifinsa yayi zai saka dole ya kiyaye gaba”

Ta fada tana daukar wayar Ummi ta shiga google ta kama hotonsa ta nuna Hajiya Zahra. Hannu biyu Hajiya Zahra ta saka ta karba kamar wanda aka bawa sakada, gabanta na wani irin bugawa da ya wuce kima kanta har sarawa yake, hotuna ne da yawa a zube ko wane da kalar style dinsa, hannunta na rawa ta saka yatsanta ta taba daya sai ya bude a babban hoto, zaune yake akan kujera ya saka kananan kaya wando da riga ya dan karkata fuskarsa kadan ya kalli wani wajen dabam. Kamanin Deen ta gani zube a fuskarsa ciki har da hade rai da haske.

“Da gaske sunansa Ameer? Kuma dan Mr Bashir ne?”

Ta tambaya.

“Ummi gashi ma kina gani a rubuce”

WANI GARIWhere stories live. Discover now