15

990 39 1
                                    

Daddy na kokarin mikawa yarsa tea cup din dake hannunsa Momy ta turo kofar dakin ta shigo, tun daga yanayin annashuwar da ya gani a fuskarta ya san akwai labari mai dadi, domin samun saukinsa kawai be isa ya saka ta farinciki har haka ba. Kamin ta karaso inda yake zaune Ameer ya shigo dakin. Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar Daddy a take ya ji kamar ya warke daga ciwon da yake, cikin yanayi na damuwa da halin da Ameer yake ciki yake kallonsa har ya karaso kusa da shi, Kanwarsa ma kallon mamaki take masa domin babu wanda yayi tsammanin dawowarsa so soon haka, duk a tunaninsu sai mahaifinsa yaje nemansa. For the first time Ameer ya ji yana dan jin nauyin mahaifinsa har ya kasa hada ido da shi.

“Ina shirye shiryen zuwa nan ya Hajiya Jamila ta kira ni ta ce gata ita da yaranta sun raka Ameer Airport jirginsu zai sauka 5:30 na tura mota ta dauko shi Airport, ni naje daukarsa da kaina domin na san kai yake son gani”

Momy ce take labartawa Daddy haka tana murmushi, Ameer ya saka hannayensa aljihu.

“I'm just care about you, an fada min jikinka ya tashi”

Daddy yayi murmushin da shi kadai ya san na minene ya ma dansa mazauni a kusa da shi.

“Ba ma iya rabuwa da juna Ameer mutuwa ce kawai ke iya raba ďa da mahaifi, ba zaka iya rayu idan babu a tare da kai ba, haka nima bana jindadi komai idan baka kusa da ni, Allah ya maka albarka ya shirya ka”

Momy da Kanwarsa suka amsa da Ameen, shi kuma ya kara matsawa jikin Daddy kamar wani karamin yaro, they miss each other irin na uba da ďa, a asibitin ya raba dare sannan ya karbi key din Momy ya fita daga Asibitin, family house dinsu ya nufa yana yin horn aka bude masa makeken gate din, ya kunna kai harabar ya faka motar ya fito ya fito ya shiga falon, kamshin gidansu na dabam balle kuma dakinsa da doka ce a saka masa turare sama da kala daya.

“What a blessing”

Ya furta yana jin yadda ya shaki iskar yanci a yanzu kamar wanda ya fito daga gidan yari. Kan gadonsa ya fadi kwance ya ware hannayensa yana jin marmarin macen da addinin musulunci be halal ta masa ba, abun bakinciki kuma babu wayarsa a kusa da shi, Sim din ma sai am masa welcome back domin ba zai iya komawa daukarsa ba he don't think ma idan ya koma zai samu liyin a gurin. Tashi yayi zaune ya nufi gurin da yake aje wayoyinsa ya dauki wanda and ya manta when last yayi amfani da ita ya kunna, sai dai ba shi da liyin da zai yi amfani da shi ya kirata a yanzu, domin liyi biyu yake amfani da su, kuma ya fasa wayar ya bar Sims din a can. Fitowa yayi dakinki ya sauko kasa falon ba kowa daman dare ya raba mutanen kirki duk sun yi bachi. A dole ya zauna akan kujera ya lumshe ya san idan yaje gidanta a yanzu ba lallai ta iya fitowa ta bude masa ba, kuma gashi sisters dinsa duk sun yi bachi balle ya ari Sim dinsu ya saka ya kirata, by this time kuma ya san kowa ya rufe shagonsa. Ba dan Allah ya hakura ba sai dan babu yadda zai yi sai karfe biyu da minti biyar ya tashi falon ya haura sama ya shiga dakinsa, wanka ne first abun da ya fara yi sannan ya saka kayan bachi ya kwanta. Hankali kwance bachi ya dauke shi be farka ba sai da Asuba, gidansu ya shan banban da wasu sauran gidajen da suke Abuja, domin akwai karamin Masallaci a na su gidan ba kamar gidajen sauran masu kudin ba. Da shi aka yi jam'in Sallah Asuba sai dai bangarensa da dabam da yake tsayawa yayi Sallah. Dakinsa ya sake dawowa ya kwanta sai a yanzu yana tunanin ko ya Nimra zata yi idan har yarinyar da ya dauko aka ce ta mutu a motarta? At least ya rage zafi domin ya san zai jefata a matsala, be zama lallai mahaifinta da Maleek da ta hada kai da shi ya bari a hukuntata ba, kamar yadda ya san mahaifinsa ba zai yarda ya bar shi ya amsa sunan kiran kai ba, ko da ta fadi cewar shi ta bawa motar a dole ita za a dorawa laifi, balle kuma shi a yanzu ya shirya karyatata idan har tace shi ta bawa motar.
Kamar an tsikare shi ya tashi ya cire tufafin jikinsa ya shiga yayi wanka ya shirya akansa sai kamshi yake ta ko'ina, key da ya shigo da sho ya sake dauka ya fita, Babu wanda ya san da fitarsa a gidan sai masu aikin da suka farka tun da Asuba suka fara aikinsu Momy bata dawo ba saboda kwana da ta yi Asibitin kanensa kuma duk bachi suke. Motarta ya shiga sanin halinsa ya saka masu gadin suka bude masa gate tun kamin ya iso. Tafiyar awa daya yayi sannan ya isa wani madaidaicin Gida da aka kawata da kayan alatu, tsayawa yayi da motarsa yana kallon yarinyar dake kokarin rufe gate din da ke nuna alamar motar da ta wuce ta gabansa a gidan ta fito, ita ma tsayawa ta yi rike da kofar tana kallonsa hanjin cikinta na kadawa domin ta ga fuskar ko waye duk da kasancewar ba da motar da ta sani ya zo ba. Ji yayi ba zai iya shiga ciki da motar ba sai ya bude ya sauko yana kallonta sai wani sham kamshi yake zuciyarsa na halbawa da mugun karfi, cikin wani irin taku na daukar hankali da gwarewa irin ta yan duniyar da take murza musu kambu yadda suke so, Angel ta je a gareshe tana tarbunsa with surprise.  

Vous avez atteint le dernier des chapitres publiés.

⏰ Dernière mise à jour : May 15, 2023 ⏰

Ajoutez cette histoire à votre Bibliothèque pour être informé des nouveaux chapitres !

WANI GARIOù les histoires vivent. Découvrez maintenant