01

489 24 6
                                    

*GASHIN ƘUMA*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 1.

*Gargad'i*
_Ban yarda ayi afmani da wani b'angare na wannan labarin ba ko kuma satar fasaha, ko a daura min shi a wata kafa na media ba tare da izini na ba, dan Allah a kiyaye_

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Karfe uku da rabi na yamma ana gab da kiran sallar la'asar, tsaye nake a cikin kitchen zan juye ruwan wanka dan na watsa ko zan samu saukin gajiyar da na kwasa, Indo ce ta fado kitchen din da sauri ta isa murhun tana kokarin juye ruwan, da sauri na katse mata hanzari.

Indo ya zaki juye mini ruwa ko baki ganni bane a tsaye? to yanzu zan juye sai ki maida naki.

Dalla matsa mini da gani, idan kin isa ki hanani juyewa banza mai fuskar mayu.

Cewar Indo sai ta daga tukunyar zata juye, da sauri na bige hannunta sai ta saki tukunyar ruwan ya kware a kafata, nan take na saki gigitaccen ihu saboda azabar zafin ruwan daya ratsa kwanyata, na shiga buga kafar a kasa jikina yana kakkarwa, Indo taja tsaki tana masifa.

Uban waye yace ki gwada mini karfi, ai gashi kin kona kanki a banza shashasha.

Tana gama fadin haka ta fice daga kicin din tana surutai, umma da sauri ta fito tana kwala mini kira tare da tambayata ba'asin ihuna, sai na fito daga kicin din ina jan kafata tare da matsar kwalla nace.

Indo ce ta kwara mini ruwan zafi a kafa dan nace ba zata juye min ruwan wankan dana saka ba.

Subhanallahi! haba Indo meyasa bakya rike girmanki ne, ai wannan zalunci ne tunda kin san ba zaki hada karfinki da Humaira ba.

Cewar Umma sai ta nufi wajen bokintin kullun koko ta saka hannu ta dibo mai kauri ta zo ta shiga shafa mini a kafar, a nan ne Inna Hajjo ta fito tana cewa.

Karyar banza karyar wofi wato Humaira sharrinki ya motsa ko, to ina daidai da duk wani salon iskancinki, yar iskan yarinya mai mugun hali. To bari kiji wallahi dole sai kin fita da awara nan kin soyata dan ba zanyi asararta ba, ga shi nan na gama yankata maza ki shirya ki fita dandalin kwadayi kuma sai ta kare tas zaki dawo.

Hawaye ne ya wanke mini fuska kiri kiri ina ji ake danne mini hakkina amma ban isa na yi magana ba, umma zata yi magana Inna Hajjo ta tare ta.

Saude babu ruwanki karki sake ki tsomo mini baki, domin ina da ikon hukunta Humaira, ki daina yi mini shsshigi da munafurci a harkata in ba haka ba zansa Musa ya yi mini iyaka da ke.

Ran Umma in yayi dubu to ya baci, amma sai bata ce komai ba ta girgiza kai ta koma daki saboda bata son rikici, ni kuwa Inna ta daka mini wata uwar tsawa wanda yasa na gigice na dauki buta da sauri na shiga bayi dan nayi tsarki da alwala, ina jin kaka daga daki tana mata fada, Inna Hajjo tana mayar mata akan ta daina saka baki in tana yi mini fada in ba haka ba sai na rainata a banza. Ko da na fito da sauri nayi alwala na shiga dakinmu na tada sallah, bayan na idar ne Hafsat ta shigo tana cewa.

Mu je na tayaki daukar kayan suyar sai na hada miki wutar na dawo gida, idan na gama girkin dare zan zo na kama miki tuyar.

Murmushi nayi dan ina matukar jin dadin yadda nake samun kulawar Umma da Hafsat, suke sanya naji ina da sauran gata. Sai na mike da sauri ina cewa.

Dan Allah in kin kammala girkin ki dafa mini ruwan wanka inna dawo zanyi komin dare dan ba zan iya yin barci ba in ban watsa ruwa ba.

To Hafsat tace mini, sai muka fito tare ta daukar mini kaya da suke a hade cikin katon farantin silba, ni kuma na dauki bokitin awara duk da kafata tana yi mini zafi, danma Allah ya taimake ni bai tashi ba saboda ruwan ba tafasasshe bane, na leka dakin kaka nace mata sai na dawo tace a dawo lafiya, kana na yiwa umma sallama tayi mini addu'a tare da fadan na kula da kaina sosai kamar yadda ta saba tunatar da ni, Inna Hajjo kuwa cewa tayi.

GASHIN ƘUMATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon