07

143 8 0
                                    

*GASHIN ƘUMA*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 7.


Ko da na fita tsayawa na yi na share hawayena kafin na isa wajen Tukur da yake washe baki, takaici ya cika ni yadda yake jifana da wani irin kallo bai kunshe da zallar iskanci, ya soma magana yana cewa.

'Yan mata sannu da fitowa, to muje daga dan duhu duhun can mana mu zauna dan nan haske ya yi yawa.

Shekeke na kalle shi ga wani irin tsanarsa na ruruwa a zuciyata sai na ce masa cikin zafin rai.

Ɗan iskan banza da wofi ko ance maka kowa irinka ne da zaka ce na je cikin duhu, saboda ka samu damar lalubeni kamar yadda kake lalata yaran mutane, to bari kaji wlh nafi karfinka kuma ka saka a ranka bazan taba aurenka ba sai dai in gawata za a kai gidanka.

Ni kike fada wa haka Humaira? Ke da zan taimaka miki na aureki, ko kin manta da sadakarki Babanki ya ba ni zan rufa miki asiri.

Baban zaka rufawa asiri shi da ya kai maka tallata amma ni kam nafi karfinka wlh, in ko ka dage sai ka aure ni zakaga ruwan bala'i da tashin hankalin da tunda uwarka ta haifeka baka taɓa ganinsa ba.

Rike haɓa ya yi cike da tsantsar mamakina, na san bai yi zaton jin haka daga gare ni ba yadda kowa ya sanni ban da hayaniya balle aga nayi fada da wani, hasalima kowa ya sanni a tsorace nake rayuwa duba da gashin ƙumar da ake yi mini a gida. Tsaki naja masa na tsirtar da yawu na wuce cikin gida kamar guguwa, dakin kaka na shige na rufe kofa na buya a nan dan na san nan ne kadai zan tsira da hukuncin baba. Minti goma da dawowata na ji baba yana kwala mini kira ina ji nayi lamo naki amsawa, Kaka ta kalke ni tana cewa.

Shige uwar daka ki kwanta a gado zanga wanda ta isa ya taɓaki, aure ne dai nace ba za ayi miki na dole ba, in sun takura kuma zan ci mutuncinsu, haba na gaji da wannan cin kashin da ake yi mini kullun, dole zan nuna musu nima ina da iko dasu da kuma ke.

Baba ya iso dakin yana buga kofa yace.

Mama Humaira ko ta shigo nan.?

Eh tana nan na ce ta kwanta, kuma ka ɓace mini daga ƙofar ɗaki tun kafin in saɓa maka, marasa kirki da imani kawai.

Amma mama kinga kuwa wulakancin da ta yiwa tukur? zaginsa ta yi fa.

Ko me ta yi masa kai ka ja, tunda tace bata so a rabu da ita mana ko kai anyi maka auren dole ne, in ba mugunta ba ka wanke Hafsa ka ba shi mana, daga yanzu ma ta dawo nan da kwana babu ɗan iskan da ya isa ya sa ayi mata auren dole. Kuma ka tashi mini daga ƙofa sun kafin in sauke tarin ɓacin raina da kuke kunsa mini kai da Hajjo.

Baba bai iya furta komai ba ya wuce daki sum sum, bai taɓa zaton Mama zata iya tanka maganar ba domin tuni yasa malam na lungu ya rufe bakinta dan ya san itace kadai zata kawo masa cikas, kenan malam bai yi aiki me kyau ba a kanta, duk da yasha yi masa aiki akan yadda ba zata hana shi yiwa Humaira izaya ba kuma aikin yayi amma a wannan karan da alama aiki bai yi ba. Inna Hajjo ce ta fito daga dakinta ta wuce dakin Umma ta kira Baba ya leko tace suje kofar gida suyi magana dan ta kula Kaka zata hana musu ruwa gudu. Suna fita tace.

Kasan Allah sai ka koma wajen malamin nan ya sake sabon aiki dan wlh Mama ba zata bari a yi auren nan cikin daɗin rai na, hmmm ni kaga ai bata cika yi mini musu ba akan abinda na yanke ko nace mata, tun kafin na dawo gidan nan nasa aka yi mini aiki akanta akan duk abinda nake so shine zaɓin da zata bi, kaga ai duk zafinta na zama nice uwar, kasan da banyi haka ba wlh ko zama a gidan nan da nayi ba zata yarda ba.

Hmmmm hakane fa, ai ina ganin da sassafe zan koma wajen malam ya sake sabon aiki.

Yadda nake jin tsanar yarinyar nan Musa, bana son ta yi rayuwar farin ciki kwata kwata bisa babban dalilin da kai ka sani nima na sani.

GASHIN ƘUMAWhere stories live. Discover now