09

132 9 0
                                    

*GASHIN ƘUMA*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 9.


Da safe Bilal ya farka ne bai ga Abdul ba, da sauri ya mike ya fito zuwa falo nan ma bai ganshi ba sai ya fito farfajiyar gida, a nan ne ya ganshi zaune a kasa ya tankwashe kafa ya yi zugum kamar mai daukar karatu, Bilal ya sauke ajiyar zuciya kana ya isa wajensa ya kamo hanunsa ya mike ba musu, sai Bilal ya jashi zuwa ciki har dakinsa ya hada masa ruwan wanka yace yayi kana ya fito ya bashi waje, Bilal ya je dakin Abdul din ya dibo masa kananun kayan da zai saka, sai ya dawo dakin. Abdul kuwa wasa ya dinga yi da ruwan yana wanke sabulu a cikin ruwan, sai da ruwan ya yi kumfa kafin ya shiga kwarawa jikinsa haka ya fito ba tare da ya cuɗe jikinsa ba, Bilal yana ganinsa zigidir yayi saurin mikewa yana tasbihi, Abdul kam ko ajikinsa dan ya mance da ana daura towel in anyi wanka, Bilal dai shi ya taimaka masa ya shirya kana ya fito da shi zuwa falo shi kuma ya koma dakin yayi wanka tare da gyara bayin dan Abdul ya bata shi, sai ya fito ya shirya sauri sauri zuwa wajen aiki, ya zo falo ya leka kichen ya samu Tani tana ta aikin haɗa abin karyawa, ya ɗiba kunun gyada da soyayyar doya da kwai tare da pepe chicken, kunun s kofi biyu ya zubo shi da Abdul, sai ya fito falo ya ajiye musu a kan carpet ya kira Abdul ɗin ya zo ba musu ya zauna Bilal ya tura masa farantin gabansa sai ya shiga bashi a baki yana karɓa, haka ya taimaka masa ya karya har ya koshi ya ture hannunsa, kafin Bilal din ya samu damar karyawa sai da ya gama ya mike da tire din ya mayar kitchen sai ya koma dakinsa ya ɗaiko jakarsa da waya haɗe da keyn mota, har ya kusa fita daga falon sai ya tsinkayi maganar Abdul yana cewa.

Zan bika.

Bilal ya juyo da sauri yana kallonsa.

Abdul aiki zani amma In Sha Allah zan dawo da wuri saboda kai, kuma zan siyo maka ice cream da shawarma na san kana sonsu.

Um umm bana so, mota da keken wasa zaka siyo mini da kwale kwale.

Yayi maganar kamar yana zumburo baki tamkar wani karamin yaro, abin yaso bawa Bilal dariya ya gimtse.

To naji zan siyo maka har da alawa.

Abdul ya yage baki yana dariya tare da tafi da hannunsa kamar yaro dan shekara uku. Hakika lamarinsa abu ne mai girma yau kuma ciwon nasa ya sauya salo zuwa yin abu kamar ɗan karamin rayo, Bilal girgiza kai kawai yayi idanunsa suka ciko da kwalla yana jin babu dadi a cikin ransa na halin da dan uwansa yake, shi kam yana mamakin wannan lamari jiya ya soma hauka ya kuma ya sauya zuwa halin yara kanana, haka ya shiga mota yana alhini, zuwa yanzu zuciyarsa tafi karkata da aikin asiri ne ke damun Abdul, da tunani barkatai ya nufi wajen aiki.

*******

Humaira.
Na wayi gari yau masha Allah kaina wasai ba sauran damuwa ko ciwon kai, ji nake kamar wata sabuwar halitta dan nayi barcin da na dade ban same shi ba, tun jiya sai wajen goman safe na farka dan har sai da kaka ta fara damuwa akan ko wani abin ne ya sameni nayi barci mai mugun nauyi haka, saboda tasan ina fashin sallah yasa bata tashe ni ba sai dai ta zo gefena ta sanya hannunta a hancina ko ina numfashi, dana farka take fada mini ba karamin dariya nayi ba ni dai nasan me na sha kuma na barshi a matsayin sirrin zuciyata, haka na fito na soma aiki tamkar doki dan wani sabon karfi naji yana kewaye jinina, sai da na gama aikin tsaf kafin na shiga dakin Umma, a nan nake samun labarin wai iyayen Bilal zasu yau niman aurena, ba karamin farin ciki nayi ba domin har a fuskarta hakan ya bayyana, Umma ce ta ke cewa.

Wani hani ga Allah baiwa ce, kinga ribar hakuri ko, gashi ba a je ko ina ba Allah yayi miki maganin matsalarki.

Gaskiya ne Umma sai dai nace Alhamdulillahi. Kaka tayi mini matukar kokari.

Ai wlh Humaira kin yi dace da masoyi na hakika, dan a wannan zamanin ba duk maza za a samu masu zuciyar Bilal ba, ke dai ki kama shi da kyau kuma kiyi masa biyayya.

GASHIN ƘUMAWhere stories live. Discover now