05

164 10 0
                                    

*GASHIN ƘUMA*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 5.


Hafsat ta kamo hannuna tana kallona cike da tsantsar tausayi tace. 

Ki yi kundum bala kawai mu shiga, Allah yana tare da ke.

Hakan yasa na dan samu kwarin guiwa saboda na gasgata Allah yana tare da ni, duk da jikina yana bari haka na daure na bi bayan Hafsa data riga ni shiga, gaba daya idonsu ya sauka a kaina na tsaya ina dubansu, zuwa yanzu har fitsari sai da naji kamar zai zubo mini saboda tashin hankali, fuskar baba a matukar daure yace.

Zo nan Humaira.

Jiki na rawa na isa gabansa na gurfana, cikin kakkausar murya yace.

Ashe me mayya ce bamu sani ba? A ina kika samo maita dan mu kaf zuri'armu ba maye sai dai in daga dangin uwarki kika yi gadon shi. Ko ni da nake namiji ina mugun tsoron maciji amma saboda ke mayya ce har kin iya daukarsa kina cunawa mutane kina basu tsoro ko, to yau ni da kaina zan karya wannan maitar taki.

Ya kare maganar tare da daga bulalar wayar wuta ya zabga mini a gadon bayana, sai na saki gigitaccen ihu ina kiran sunan Allah, kamar na kara zugashi ya soma duka na kamar ya samu dabba, ihu nake ina bashi hakuri tare da alkawain bazan sake ba, na shiga gudu a tsakar gidan yana bina yana cigaba dazabga mini bulalar, na isa wajen Inna Hajjo na kama kafarta ina matsanancin kuka, sai ta saka kafa ta cureni ta dauki marfin kwanan langa ta kwada mini, dan nan take kaina ya fashe, saboda azabar da naji ya ratsa kaina na mike a fujajan ina kurma ihu nayi hanyar fita waje da gudu baba yana bina shima a guje, yana zagina tare da zuba mini bulala. Ina fita kofar gida naci karo da mutum wanda yasa ni jiki na rawa na boye abayansa ina rizgar kuka sosai, ganin haka yasa baba yaja danga yana cewa da karfi.

Wlh wannan kadan nayi miki dan sai kin fada mini inda kika samo maita, shegiyar yarinya annoba kawai zaki dawo cikin gidan ki same ni ban gama hukuntaki ba dan ba zaki jawo mana masifa ba sai dai ya kare akanki tsinanniya.

Yana gama fadar haka ya shige gida a fusace, mutane har sun fara taruwa ko wanne cike da takaici, babu wanda ya isa ya tankawa baba dan duk wanda ya shigar mini to fadar zata koma kansa ne aita bala'i sai anyi da gaske fadar ke mutuwa, shiyasa yanzu mutane suka shafawa kansu lafiya suka daina shiga mini fada, sai dai in sun gani suyi Allah ya kyauta da addu'ar Allah ya saka mini. Sai a lokacin Hafsat ta fito idanunta yayi jajir saboda kukan tausayina, jin ta ambaci sunan Bilal yasa nayi saurin fitowa daga bayan wanda nake a boye na isa wajen Hafsat na tsaya ina dubansa, sai a lokacin na fahimci a bayan wanda na boye, fuskarsa a matukar hade saboda bacin rai.

Hafsat kuyi hakuri da abinda zan fada, amma gaskiya mahaifinku mutum ne mara imani kwata kwata bai san darajar mitum ba, yanzu fisabilliahi me Humaira tayi haka da zafi har ta cancanci wannan hukunci mai cike da tozarci.

Kasa magana muka yi gaba daya, Hafsat ce tayi jarumtar ce mini.

Humaira umma tace ki je gidan Inna Amina ki kwana a can da safe zata zo ta sameki anan. Bilal kasan iyaye sai dai muyi hakuri dasu amma laifi tayi aka hukunta ta, yanzu ka je gobe ko jibi in Allah ya kaimu sai ka dawo. 

Hafsat ta kare maganarta ga Bilal, iska yaja ya fesar kana yace.

Muje ki rakata zuwa chemist a wanke mata ciwon dake goshinta, a bata magani.

Laaa daka barshi wlh ai ba wani ciwo bane, in na yi wanka zan ji dadin barci nagode da kulawa.

Nace da sauri dan bana son taimakonsa, ya duba Hafsat zai yi magana ta riga shi tace.

Tunda tace ka barshi kaje kawai mungode.

Duk da haka bazan barta haka ba dole na samo mata maganin da zata sha, dan gaskiya ba zata ji dadin barci ba in bata sha wani abu ba, ku jira ni a can wajen ina zuwa yanzu.

GASHIN ƘUMAWhere stories live. Discover now