13

131 10 0
                                    

*GASHIN ƘUMA*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 13.


Momyn Bilal da wasu mata har da Hauwa yayarsu Bilal ne suka fito suna yi musu lale maraba. Su Umma jiki a sanyaye suka fito suna ɗar murmushi, Momy tace.

Sannunku da zuwa, to ga ɓangaren amarya Humaira can mu je ku gani, daga bisani sai mu je namu ɓangaren mu gaisa.

Mu ba nan gidan Bilal ya ce a kawo mu ba, kamar an yi ɓatan hanya.

Cewar Inna Hajjo. Momy ta yi murmushi tana cewa.

Ni ce mahaifiyar Bilal kuma nan ne gidansu, duk abin da yayi da sanina ne kuma ya ɓoye muku ne saboda ya jaraba yarinyar ya tabbatar tana sonsa don Allah ne ba dan arzikinmu ba. Dan haka ku cire shakku nan ne gidan amaryanku Humaira.

Ikon Allah wannan al'amari akwai ɗaure kai da jijiyoyin jiki.

Cewar Umma, sai suka shiga bin bayan su momy zuwa part din Humaira, mai gadi da Musa suna bin bayansu da kayan da suka zo dashi. Hauwa ce ta buɗe ƙofar da yake key yana hannunta sai ta matsa gefe tana cewa bisimilla su shiga, Inna Amina ce ta fara shiga da sallama sauran ma suka rufa musu baya, wani irin sanyin ac da kamshin turare yake dukan hancinsu, nan kallo ya koma sama kowa wanne ya shiga bawa ido abinci, wato wani irin aljannar duniya suka gani, falo ne mai matsakaicin girma amma kuma an zuba masa dukiya mai tarin yawa, kujerun royal ne gasu nan sai sheƙi suke, ga wani dan korido da aka saka show glass turarukan wuta da humra ne a ciki harda ma ɓangaren perfumes na Bilal dana Humaira, ga katon tv nan irin wanda yake tsayawa da ƙafarsa a kasa ga kuma sauran kayan dish nan, tiles ɗin mai irin zanen manyan fulawa ne fari da baki sai sheƙi yake, falo yaji pop komai masha Allah , ɗaki uku ne a ciki na Bilal ɗaya sai na Humaira aka buɗe musu nan ma royel bed ne ga tv a a jikin bango wanda mutum yana kwance yana kallo, ga waton waldrop nan da mirro a gefe wanda mutum zai riƙa kallon kansa tun daga kasa har sama, suka buɗe toilet shima masha Allah komai na zamani ne a ciki, sai suka fito suka shiga kitchen nan ne suka ƙara kashe kwarkwatar ido da kayan electirc na zamani kala kala ga food womers nan kala kala, jugs da su plate ba a magana hatta cokula abin kallo ne, komai a kwai a ciki, sannan suka buɗe wani ƙofa daga ciki sai suka ga store ne an zube kayan abinci har su doya da dankali komai da shi a ciki sai dai a diba ayi amfani da shi, ga katon deep frezer nan mai dauke da nama, kifi, ganda, dasu kaji a ciki duk sunyi kankara suna jira a dibesu a fara amfani dasu, Inna Hajjo har sai da ta haɗiye miyau tana kissima ina ma Indo ce a wannan matsayin tabbas da ta gama rabauta a duniya, baƙin cikin ta ɗaya ace wai Humaira ce zata kwashi wannan ragadadar arzikin, sai taji wani tuƙuƙin baƙin ciki ya turnuketa wanda har ɗaci ɗaci take ji daga maƙoshinta, haka suka dawo falo suka zazzauna a kujeru suna kissima santinsu ga ɗakin Humaira, Umma ji tayi kamar ta saki guɗa ta tashi ta taka tare da sakin habaici ga Inna Hajjo, sai dai babu damar yin haka saboda su Momy na tare da su, dole suka yi kokarin kama kansu dan kar su yi abin kunya, su kuma su momy sunki basu waje ne domin Bilal ya gama fada musu halin 'yan uwan Humaira, yace su tsaya dan kar a samu wacce zata yi musu sata. Hauwa ce ta katse hirar da suke yi akan ƙayatuwar ɗakin, tace suje ɓangaren Momy su sha ruwa, haka suka fito suna sambarka domin kuwa Allah ya tsamo Humaira daga huƙuba ya dawo da ita aljannnar duniya. Suna isa sashin Momy nan ma kallo suka shiga yi domin ƙayatuwar Falon, suka zazzauna a cushing suka shiga gaisawa su Umma suna zuba godiya bisa kokarin da suka yi akan Humaira, Momy ta kaɗe baki tace.

Ai mu Humaira 'ya ce a wajenmu kuma duk abinda Bilal ke so muma dole mu taya shi so, sannan duk abinda muka yi mata bamu faɗi ba domin kunyi mana kyautar 'yarku da ba zamu iya biyanku ba.

Hakane amma kam kunsha hidima Allah ya ƙara arziki da rufin asiri.

Cewar Inna Amina, duk suka amsa da amin, a nan ne aka fito musu da kayan motsa baki, kaji ne soyayye a wani katon farantin silba an rufeshi da farar leda, sai kuma kwalin Donot da kuma cake da suka yi musu oder kusan ko wanne 100pcs, ga katon ɗin drink nan guda uku dana ruwavbiyu. Aka gabatar musu dashi akan su ci, Inna ta yunkura zata taso Umma ta katse mata hanzari da cewa.

GASHIN ƘUMAWhere stories live. Discover now