11

148 4 0
                                    

*GASHIN ƘUMA*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 11.


Bilal.

Bilal da haushin Abdul ya bar gida ya tafi wajen aiki, ji yake ko maganarsa baya so ayi masa, tsantsar tsanarsa yake ji sosai wanda kuma ba zai ce ga hujjar yin hakan ba, shiyasa ya yakice damuwarsa ya cigaba da sabgoginsa. Ko da ya dawo gida bai bi takansa ba sai ma maganar shirye shiryen bikinsa da ya yiwa momy. A cikin kwanakin Abba ya ba shi kudi masu yawa ya ce ya haɗa lefe da kuma sauran shirye shiryensa, sannan ya ce a cikin gidansu zai zauna saboda ɓangaren bai da gyara fanti ne kawai za a sake yi masa, Bilal ya so Abba ya bashi ɗaya daga cikin gidajensa ya zauna, Abba yace bai yarda ba yafi so ya zauna a nan cikin gidan suga kamun ludayinsa, wani sashi ne daga gefen nasu Momy wanda Abba ya ginawa mahaifiyarsa kakan su Abdul a cewarsa zai ɗaukota daga kauye ya dawo da ita nan da zama, sai dai kuma kash! Allah bai nufa ba saboda ta rasu a can kauye dama dana fama da ciwon hawan jini shi ne ya tashi mata har ya yi ajalinta, to side ɗin a rufe yake tun lokacin sai yanzu da batun auren Bilal ɗin ya tashi Abba yasa a gyara wajen a zuba funitures wanda suka yi oder ɗinsa daga companyn MG Furnitures dake nan kaduna. _MG FURNITURES COMPANY nayin kaya kala kala kama daga dangin gado, kujeru, show glass, center table, dinning, kitchen kabnet da sauransu. Kayanmu akwai inganci da kyau tamkar daga kasar waje, zaku iya samun mu a show room dinmu dake No. 3 Ali Akilu Road (inside freetime house), Kaduna Nig. Ko kuma a tuntuɓemu a number waya 09034940106, whatapp ko kira. Dan Allah sai kun tabbatar da kun shirya zaku nime mu. Sai kun zo._

Dan haka Bilal ya mayar da hankalinsa wajen haɗa akwati da sauran yin invitation card, duk da bikin ba shiri amma kuma yana so yayi abin da zai yi armashi saboda bikinsa ne kuma a matsayinsa na babban yaro dole ne yayi abinda zai burge, duk da bai da ra'yin yin wani party amma ya shirye wa abokan shaye shayensa wata liyafa isu isu. Abas shi ne ƙarfin shirin biki dan duk wata zirga zirga tare suke yi kaɗan ne Bilal ke yi da kansa. A haka dai kuma Bilal yake samun leƙa Humaira suyi zance duk da tarin busy da yayi, har ana gobe sallah daya samu yaje hira kuma sai suka samu saɓani akan maganin da take sha yayi fushi bai sake zuwa ba har yanzu da bikin yayi saura sati ɗaya. Yau tunda ya wayi gari yake jinsa da kasala saboda jiya ya kwana a club sai gabanin asubahi ya dawo gida shi ne ya samu barci bai farka ba sai wajen karfe goman safe, silin yake kallo tunanin Humaira ce ya cika masa zuciya wanda yake jin yau dole sai yaje ya ganta, daga nan su tattauna maganar bikin nasu daya kusa, ya ji me take shiryawa, sai dai ya ɗauki alkawarin ja mata kunne akan shan maganin barcin nan dan ba zai yiwu ya ɓata rawarsa da tsalle ba, shima karan kansa yana so ya daina kasawa yayi saboda abin ya shiga jikinsa sosai, kuma duk lalacewarsa shi na mijine yana ganin yadda shaye shaye yake yin illa ga mata, dan haka dole ne ya nuna mata ɓacin ransa sosai dan ta daina gaba faya, yana tunanin ma in ta dawo gidansa komai zai yi dai dai, sannan ma yana so ya kaita gidan Abas yasa matarsa ta kaita wajen gyaran jiki dan yasan tsinannun mutanen gidanau babu abinda zasu yi mata. Da wannan tunanin ya tashi yayi wanka ya sanya boyel fari ya saka hula bakar dara da takalmi baki ya feshe turare tare da ɗaukar key mota zai je gidan Abas akwai maganar da yake so suyi daga nan ma sai ya yiwa matarsa Bilki maganar kai Humaira wajen gyaran jiki. Yana fitowa falo ya tadda ana bawa Abdul magani sai turjiya yake yana kuka da furzar da maganin, Bilal ya daka matasa wata uwar tsawa yana cewa.

Zaka tsaya ka sha ko sai na haɗa maka jini da majina, ɗan bura'uba ana nima maka sauki kana iskanci.

Nan take Abdul jikinsa ya ɗauki rawa domin bai manta dukansa da Bilal din yayi ba, ya tsaya yana shan ruwan maganin da yake jin duk lokacin da ya sha tamkar ana ƙara ruruta azabar daya ke ji ne a jikinta kuma cikinsa sai ya dauki zafi kamar ana hura wuta, sha kawai yake yi hawaye yana malala a kuncinsa, dama Musa ne ke bashi Jabiru yana rike da shi, momy ce ta fito daga ɗaki tana tambayar ko sun gama bashi? Jabiru ya amsa mata da eh sai suka mike suka fice daga falon, Momy ta zauna tana duban Bilal.

Kai kuma ina zaka je ko Humaira ce ta yi kira.?

Gidan Abas zani, Humaira kuma sai dare zani.

To madallah, na ce ya batun lefe yaushe za a kai musu.?

Momy ai nace musu ba lefe kuma sun yarda, kawai dai in sun zo ganin ɗaki sa gani a nan bangarenki, dan wlh bazan aika musu lefe ba su kwashe kayan, saboda waɗan nan mutanan azzalumai ne na karshe, shiyasa ma nake so na fesa mufu gumar mamaki dan har yau basu san ko ni waye ba.

To Allah dai ya kyauta shiyasa ni wlh bana son harka da ƙananan mutane, dan dai kawai ka dage kana sonta ne amma sam yarinyar bata dace da kai ba.

So ne ya ja mini Momy, hakanan za muyi hakuri na aureta ta zo gidan nan a matsayin surukarki.

Ya faɗa yana dariya momy tayi masa dakuwa tana murmushi, yace shi zai wuce momy tayi masa a dawo lafiya har ya fara tafiya ya juyo da kallonsa ga Abdul.

Shege kana kallona sai kace maye to ka ci kanka wlh, ni fa Momy na fara zargin anya Abdul ba ƙungiyar asiri ya shiga ba yayi musu bore bai kawo abinda suke ce suna so ba sai suka mayar da shi haka.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, kai ubanka nace maza ɓace mini da gani in ba zaka yi masa addu'ar samun lafiya ba ka daina yi masa mugun fata.

Bilal ya fice da sauri dan ya ga Momy ranta ya ɓaci, Abdul kuwa yana jin duk abinda yace hawaye ne suka shiga bin kuncinsa yana faɗi a ransa.

Shima an raba ni da shi. Allah kana sane da ni kai kaɗai na barwa lamarina.

Sai ya miƙe ya koma ɗakin da ya zame masa dole ya zauna a ciki, dan har ya saba da bakar izayar daya ke sha duk lokacin daya kasance a cikinsa, Momy da ido ta bishi cike da tsantsar tausatawa tana yi masa fatan samun lafiya. Zuwa yanzu Abdul ya saba da halin da yake ciki hankalinsa yana nan garau bai gushe ba yana gane komai sai dai kawai wani lokacin yana samun kansa da surutu shi kaɗai, sai kuma in ya fito farfajiyar gida yayita tsince tsince yana ci ko kuma ya tara kwalaye da gwangwanin madara yana jera kaya wai yana wasa sai kace yaro dan shekara biyar, sannan wani lokacin ana firgitashi, iyayyaku dai kala kala yake yi sannan zuwa yanzu ya tabbatar da maganin da ake yi masa aikin banza ne domin kamar ƙara masa ciwo ake yi, Abba kuma yanata iya ƙoƙarinsa wajen kawo masa magani daban daban ana gwada masa domin a dace, sai dai har yau dai ciwon ba sauyi, babbar damuwarsa ba a barinsa fita amma da ya samu damar nimawa kansa lafiya, kawai gani suke in ya fita ɓacewa zaiyi dan suna yi masa kallon mara hankali.

********

Humaira.

Na damu sosai da rashin zuwan Bilal, gashi ni ba waya ba balle na kira shi na bashi haƙuri, Addu'a kawai nake yi akan Allah ya huci zuciyarsa yasa ya zo na nima yafiyarsa. Haka na tashi sukuku kamar mara lafiya saboda na fara koyan yadda zan daina shan wannan maganin da yake niman zame mini matsala, sai dai ga dukkan alamu zan sha matuƙar wahala kan abin ya bar jikina, saboda jiya da ban sha ba to ban samu barci ba haka na wayi gari da mugun ciwon kai ga kasala da kuma rashin kuzari a jikina, har Hafsa tana yi mini tsiyar wai ko na fara kewar gida ne tun ba a daura ba, nan ta dinga yi mini surutu dai naki kulata dan gaskiya a dame nake, da ta ga nayi banza da ita sai taja bakinta tayi shuru. Ni kaɗai nasan yadda nake azabtuwa, dan haka yasa na yanke shawarar zan sha maganin ko guda ɗaya ne da rana na samu ɗan sukuni, ina ganin dai shan maganin faraɗ ɗaya abu ne da zai jawo mini wani sabon ciwo, wanda kuma a dai dai wannan lokaccin bai dace ba, dole zan cigaba da sha zuwa bayan bikinmu sai na bar sha kwata kwata, da wannan shawarar na ajiye aikin sharar da nake na koma ɗaki na ɗauki maganin guda ɗaya na afa a bakina na taune na haye gado, yanzu saboda kwarewa ko ruwa ban cika sha ba in na haɗiye maganin, da yake barcin yana damuna yi din ne na kasa cikin ikon Allah sai ya figeni. Bani na farka ba sai bayan sallar la'asar, kaka tayi ta yi mini faɗa akan yawan barcin da nake tana cewa haka za a kaini gidan miji na riƙa barci, ai wata rana saina kona abincin da nake dafawa ko kuma na samu matsala da mijin, ni dai toshe kunne na nayi na fice na ɗauro alwalar sallar azahar da banyi ba na haɗa da la'asar. Dana idar ne na nima abinci na ci, domin fa da zarar na farka da ga barcin nake tashi da wata uwar yunwa, daurewa ma nayi na samu yin sallah kafin naci abincin.

_Yau ayi mini uzuri ba yawa saboda wayata ba chargy._

Rahma ce Maman Saltan da Samha.

GASHIN ƘUMADove le storie prendono vita. Scoprilo ora