3

169 10 0
                                    

*GASHIN ƘUMA*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 3.


Baba sai ya kara gyara tsayuwarsa yana kare wa Bilal kallo yace.

Yaro daga ina waye ubanka? Sana'ar me kake yi.?

Bilal yaji abin ya yi masa bambarakwai wai namiji da sunan Hajara, ransa ya sosu kwarai dan a ganinsa yafi karfin cin zarafin baba dan ko a me gadinsu bai kai matsayinsa ba sai yace cikin dakiya.

Ni ba ɗan kowa bane hasalima babana ya rasu sunansa Ali mai yatsi shi ne sana'arsa, ni kuma aikin gini nake yi.

Yauwa yanzu naji batu shiyasa ga talauci nan karara a jikinka, to ai ba damuwa tunda Humaira ce kake so dama itama gayyar tsiyar ce, dan haka na baka izini ka fara zuwa zance ku fahimci juna, saboda nine ubanta wanda zai daura mata aure, bayan kwanaki sai ka turo magabatanka a fara maganar aure dan gwara na aurar da ita tunda ta kawo girma.

Nagode baba Allah ya saka da alkhairi.

Cewar Bilal ya fada yana risinawa, Baba bai bi takansa ba ya koma cikin gida, da mugun kallo Bilal ya bishi yana mamakin bakin halin daya nuna masa, ya san ya kawo kansa wajen kaskantattun mutane, sai ya shiga kokwanto anya ma shine asalin mahaifin Humaira dan ya hango akwai tsana a tsakaninsu, ya ja guntun tsaki yana cewa a hankali.

Zaka ga matsiyaci ganin idonka kuwa, mara mutunci banda kaddarar so me zai kawo ni wajen kaskantaccen mutan irinka, kuma insha Allah zan jajirce naga na mallaki Humaira dan gidan naku ma naga ba kaunarki suke yi ba.

Ya karashe maganar yana jan guntun tsaki sai ya wuce yana isa bakin titi ya tari napep ya kai shi wajen motarsa, daya sauka ya biyashi ya bude mota ya shiga tare da cire p-cap, ya fesar da iskan bakinsa yana hararo yadda zai shayar da su baba giyar mamaki, ashe gwara daya je a talaka domin hakan da yayi ya gane waye su, saura Humaira ta ci nasa jarabawar duk da ya hango ita din ba bai zalama bace, amma dai zai jarabata dan yana so ya gina soyayyar giskiya ce a tsakaninsu.

***

Baba yana shigowa gida ya shiga kwala mini kiri, cikin faduwar gaba na fito na gurfana a gabansa da yake tsaye a tsakar gida, jikina har rawa yake yi dan in har yayi mini irin wannan kiran hantar cikita saita kada dan da wuya bai taba lafiyar jikina ba, wata kila Inna Hajjo ce ta kulla mini wani sharrin, cikin daure fuska ya soma magana wanda ya katse mini tunanin laifin da nayi.

Keee, yanzu naga wani saurayi a waje Hafsatu tace wajenki ya zo, to sai ki ba shi hadin kai ku fahimci juna dan na riga na bashi izini ya fara zuwa zance, saboda na gama yanke shawarar aurar dake kawai zanyi na huta ko na samu abincin gidana ya fara yi mini auki. Kuma in har ya kawo mini kararki akan kinyi masa rashin da'a wlh saina karya ki, tashi ki ban waje shashasha ana magana tana sumsum da kai kamar munafuka.

Na mike jiki na rawa na koma dakinmu na zauna, ina jin sadda Inna hajjo ta fito tana cewa. 

Haba Musa ya zaka ce aure zaka yi mata salon ka durkusar dani da neman kudin da take yi mini, ka bari dai na sama abinda na sama sai ayi auren nan gaba.

Yaya Hajjo taya zaki shagala da niman kudin da Hunaira take yi mini, to wlh bari in fada miki gaskiya wannan matsiyaciyar yarinyar ba zata taba iya niman miki arziki ba sai dai ki samu kudin kashewa dan farar kafa gareta, ko baki ganin tunda aka haifeta a gidan nan samu na yayi baya komai namu ya taɓarɓare, to gwara ki sauya shawara dan wannan ba hanya bace mai billewa, aure shine zai rabamu da mugun kaddararta dake bibiyarmu.

Kuma fa gaskiya ka fada, shegiyar yarinya uwa mayya gwara ayi mata auren, ko tabarma da katifa ce ma kaita da ita dan dama ta riga tayi gadon tsiya.

Cewar inna cikin fada, muryar kaka ce ta kashe musu hanzari daga cikin daki tace.

GASHIN ƘUMAWhere stories live. Discover now