15

279 11 2
                                    

*GASHIN ƘUMA*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 15.

              *Last free season 1.*
_Domin samun cigaban wannan labari sai mu haɗu a season 2 wanda sai kun biya kuɗinsa N300 kafin zaku cigaba da samunsa ɗoɗar har zuwa ƙarshensa. N300 ne ba yawa, dan Allah ku mara mini baya._

Pay N300 to 0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card N300 a 09034940106, masu so ta pc su tura N600. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.

Ta shi na yi na adana kwandon a gefen gadona, na shiga toilet na tsaya ina kallon kayan alatu, sai da na ɓata lokaci a ciki ina kauyenci, kafin na kunna famfo na yi alwalar sallar isha'i, na fito na gabatar da sallar, na idar kenan ina naɗe ɗan kwakina dana yi salla akai naji sallamar shigiwar su Bilal sai nayi saurin zams a gefen gado tare da jawo hijab dina na rufe fuskata, ba jimawa sai ga Bilal ya turo kofa yana cewa na fito na gaisa da abokansa, cikin sanyin jiki na mike ba tare dana ce komai ba na biyo bayansa, na same su a falo na zauna a ɗaya daga cikin one seater na gaishesu suka amsa kana Abbas ya buɗe taro da addu'a daga nan suka ɗaura da nasiha da tunatarwa akan zaman aure, ni dai ina saurarensu har suka gama, wani me suna Jafar da Bilal ya ambata ya ce cikin zolaya.

Amarya ga kuɗin siyan baki nan duk da mun saki kinyi magana kafin mu biya, ki kula da ango sosai kar ki rika barinsa yawon dare dan wannan yadda kika san ya ci kafar kare.

Kasa munjaye dan ni da kai duk kanwar ja ce.

Cewar Bilal daya bashi amsa, sai duk suka saka dariya suka mike suka yi mini sallama sai suka fita, ni kuma bin kuɗin da suka ajiye mini a hannun kujera nayi da kallo ina murmushi, wato ni fa yanzu Allah ya kashe ya bani nice da kudi dumi dumi a hannu halak malak ɗina sai yadda nayi dasu, gaskiya aure yayi sosai ba karya, yanzu ma aka soma dan Allah kaɗai yasan irin duniyar da zan samu a gidan nan, Alhamdulillah Allah ka ƙaro mini kwanciyar hankali, na fada a zuciyata ina murmushi, a haka Bilal ya dawo ya sameni sai ya ce naje ɗakina na ɗauro alwala nace to sai na koma ciki, nasan ina da alwala amma duk da haka sai da na sake na fito falo na zauna, ba jimawa ya fito sanye da jallabiya fara hannunsa ɗauke da dadduma, nan ya shinfida mana da yake daddumar babba ce duka muka hau ya jamu sallah, raka a biyu muka yi muka idar ya kama kaina yayi min addu'a kana ya mike ya ɗauko wata leda ya shiga kitshen ya dawo da babban plate ya juye kazar dake cikin ledar guda biyu ne ya mayar da ɗaya, ya koma ya ɗauko mana drinks masu sanyi da ruwa, nan muka zauna kan carpet bayan mun daga daddumar, yace mu ci, ni dai murmushi nayi ina sunne kai amma har ga Allah sai haɗiye miyau nake duk na kosa na jishi a bakina tsabar ina kwaɗayinsa, Bilal ya soma ci yana cewa.

Nasan kina tare da yunwa kici ki koshi, in kuma kin ki to zan cinye duka na barki.

Wasa kawai nake yi da yatsuna ina murmushi, haka yaci sosai ina kallonsa naki ci har ya kora da ruwa ya mike yana ce mini bari ya watsa ruwa yana zuwa, gyada masa kai nayi ban iya cewa komai ba, ina jin ya rufo kofar dakinsa na jawo plate din na soma cin kazar nan kamar wata mayunwaciyar zaki, ci nake hannu bibbiyu, ina yi ina kora fanta drink har saida na kusa tada wanda Bilal ya bar mini kafin naji na koshi, nayi wata gauron gyatsa nayi saurin toshe bakina dan kar yaji, na mike na hada kayan gaba daya na kai kitchen, na tsaya ina niman ruwan wanke hannu gadai famfo na sink din wanke wanke amma ban iya kunnawa ba sai sauran ruwan gorar na wanke hannua da shi na fito na zauna a kujera. Ba jimawa ya fito saye da wando tree quater da kuma singlet, kallo daya nayi masa na kawar da kai ya wuce kitchen yaga yadda na ajiye kayan, sai ya kwala mini kira na mike da sauri na iskeshi a can, ya kalleni yana ɗar murmshi.

Hajiya Humaira da haka zaki fara yiwa kitchen ɗinki tarba? Sauran drink din da ban sha ba ki saka a fridge wannan naman kuma ki kai store ki saka a freezer da safe sai ki dumama mana mu ci, sauran kayan ki saka a nan sink wajen wanke wanke ki kifesu in ba zaki wanke yanzu ba da safe saiki wanke. Kinga kin maida komai a muhallinsa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 11, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GASHIN ƘUMAWhere stories live. Discover now