04

178 12 1
                                    

*GASHIN ƘUMA*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 4.


Abdul yana isa asibitin kunne wanda yake yin aiki nan kusa da poly, shi cikakken likitan kunne ne yanada ilimi sosai dan a ABU zaria yayi karatu, shekara biyu kenan da fara aikinsa a nan. Abdul yayi parking ya fito tare da jan kafafunsa da suka yi masa nauyi, Nurse Abida ce ta tare shi suka gaisa sannan ta daura da cewa.

Ai munyi zaton yau ba zaka fito ba, har doctor Idris yana cewa anjima zai je gida ya duba ka.

Bazan iya zaman gida ba shiyasa na fito ya aikin.? Da akwai marasa lafiya kuwa.?

Aiki Alhamdulillah, kasan weekend ba a cika samun out patients ba.

Abdul yace hakane kana suka rabu ya wuce cikin reception, ita kuma ta wuce wani bangare na asibtin. A rayuwar Abida tana mugun kaunar Abdul sai dai kullun nunawa yake bai san tana yi ba, kuma ya san tana sonsa kawai dai yaki bata fuska ne domin shi baya ra'ayin aurenta, shi a rayuwarsa bai damu da mata ba ko Fadila ma hada su Momy tayi kuma aka yi dace Fadilar tace tana sonsa domin Abdul mutum ne mai kyau da kwarjini, yafi Bilal kyau nesa ba kusa ba kana ganinsa yayi kama na mutanen chadi kamar shuwa araf, ya samo asalin kyansa daga mahaifiyarsa ne duk da baida wani haske sosai amma fatarsa a murje take cike da hutu, Bilal ya fishi haske sai dai shi baida wani kyau dan guntun hanci gare shi da katon lebe kama da Abba yayi sosai kamar an tsaga kara. Yana shiga ciki suka gaisa da mutanen da ke wurin, sai ya wuce office dinsa yana budewa yaji kansa yayi mugun zarawa kamar an buga masa guduma, nan take ya fara gumi kamar mai jegon data sha turirin ruwan zafi, yaji kafarsa yayi masa mugun nauyi da kyar ya jasu ya rufe kofar yana isa tsakiyar office din yaji wani gigitaccen kara wanda yasa zuciyarsa tayi mugun bugawa kuma ta tsaya cak da aiki nan take, sai ya zube a wajen rai a hannun Allah.

********

Humaira.

Tunda gari ya waye na shiga yin ayyukan dana saba yinsu, Ashiru ne ya fito daga hanyar bayi yana kwarma ihun maciji, wanda yaja hankulan mutanen gidan da suke daki duk suka fito suka yi cirko cirko ga baba ya fita kasuwa, Umma ce tace Ashiru ya kira mazan layi suzo su fitar mana da shi, sai ya fita da gudu ni kuwa sai na tsinci kaina da son zuwa inda macijin yake na ganshi, ina zuwa kuwa na ga ya faso kai yana ganina ya sauke kansa kasa ya zaro harshe, cikin wani irin jarumta dana ji shi tun dafa zuciyata zuwa gabobin jikina yasa na tunkareshi na sauke masa hannuna ina yawo da shi tare da yi masa wasa, nan take ya fara hawa hannuna ya nade jikinsa tunda guiwar hannuna zuwa yatsuna, ya zuro kansa akan yatsuna sai kawai na fito tsakar gida, suna gani a suka fasa ihu, umma tana yi mini fadan idana hankali zan dauki maciji, ni kam kamar an toshe mini kunne ana tunzurani na yi wajen da Inna Hajjo ke tsaye ma mika mata hannuna da macikin ke kai saura kadai ya kai mata sara, sai ta saki ihu tayi faduwar yan bori tana kurma ihu, ban yi kasa a guiwa ba na kara cuna mata data zaki wani irin kara sai ga ruwan fitsati yana malala a inda take zaune, da mugun sauri ta yi rarrafe ta fada dakinta ta rufe kofa jikinta babu inda baya rawa, ganin haka yasa Umma ta ruga daku da gudu tana cewa.

Humaira, Humaira ki ajiye macijin nan.

Nayi kunnen uwar shegu da ita, ina jin kaka da take daki itama tana mitar na ajiye shi kar yayi mini illa ban kulata ba, a lokacin Hafsat da Indo suka dawo daga islamiyar safe, suna gani na da maciji suka yi mutuwar tsaye, ni kuwa ina ganinsu sai nayi kansu a guje, Hafsat ce ta samu damar fita waje Indo kuwa taci tuntube da bokiti ta fadi kasa, ai nan take na cuna mata, da ta saki uban uhu sai ta sume, nan na shiga kwasar dariya raina fes dan naji dadin hakan, kila dalilin haka na samu sassauci, a lokacin ne samarin unguwar suka shigo rike da buhu suna ganina suka ja tunga suna kallon ikon Allah sai a lokacin nace.

GASHIN ƘUMAWhere stories live. Discover now