chapter 1

206 13 0
                                    

🍇MunayaMaleek🍓

https://whatsapp.com/channel/0029Va5o0Gc4o7qU8MCJuN32

_By NoorEemaan_✍️📚

_*All thanks goes to Allah subhana wata ala for giving me the life, ability, and strength of writing Munaya~Maleek. Greetings to ummourh na, my mother, my queen, my first love, Hajiya Mama. My sweet siblings, i love You. my fans ain't  excluded also, ina son ku duka, da barzaku nake taka rawa, my Habibty Saudat i know you won't see this, cos you are not a fan of novels... but get this, i love You so much.*_

*_Ban san yanda zan fasalta muku wanna labarin ba, but it will be the best novel  i have ever written, it's going to be hot hot and hot, Kun san salon labarina, so trust me on this one too guys, sai dana shirya tsaf kafin na kowa muku shi, labarin ya kunshi cin amana, son zuciya, ƙaddara, kunci, mumunan dabi'a, fadakarwa, wa'anzantarwa, da nishadantarwa*.
*And i will be using roman numerals for every chapter, hope you won't get confused? so guys are you ready? Oya let's get started_.*🥰

All my novels are available complete at this platforms, usernames are:
Wattpad @NoorEemaan
Arewabooks:nooreemaan

⚠️*Caution*⚠️
🚫Ban yarda a juyamin labarin nan ta kowacce siga ba, ban yarda  a karanta ko ɗora min shi  a YouTube without my consent ba, ban kuma yarda a maida min shi audio ba tare da sanina ba🚫

*NOTE*
This novel is a total work of fiction, any resemblance of story or life style should be considered as a coincidence please!

In the name of Allah most gracious, most merciful...

i.....
(1)

*Tuesday*
8:00am

Cikin Wata murya mai rarrabewa hadi da rawa tace "Muna! dan Allah karki tafi ki bar ni kadai a gida" yarinya mai shekaru shida dake tsaye a rubabben kofar wani daki ce tayi maganar tana fashewa da kuka mai matukar ratsa zuciya.

Budurwar da aka kira da Muna dake tsaye a soron gidan ta tako cikin sanyin jiki zuwa wajen yarinyar, ta durkusa a gaban ta, tayi matukar kokari wurin mayar da hawayen da suka ciko idanun ta kana tace "Amnah kiyi shiru, bazan dade ba kin ji, saboda ke zan fita fa, saboda samun lafiyar ki nake wahalar neman aikin nan, kin tuna?, ko bakya so ki warke?"

"Inaaa sooo" Amna ta fada tana murza idanun ta, Munaya ta kamo busassu kana sirarran hannun ta tace "toh ki daina kukan bari naje, akwai koko a daki idan kin ji yunwa ki sha kinji? karki je ko ina" ta karasa maganar tana kokarin janyo mata hular kanta gaba wanda kwalkwal din kanta ya bayyana, domin babu gashi ko daya sak'amak'on lalurar yarinyar.

Ta dauki lokaci kafin ta iya haɗa kalaman
"Ni na daina kula su khairat, bayan idan na fita wasa suna ce min mai kan maza" ta kai karshen maganar da  turo labb'anta gaba, Munayan tayi murmushi mai ciwo tace "karki damu da maganar su, zaki warke, har gashin ki ya fito in dinga Miki kitso, kina so ko?"
Amnah ta daga kai alamun eh ta fara murna, hakan ya ɗan sanyaya ran Munaya har ta samu kwarin guiwar mikewa  domin tafiya, nan Amnah ta fara sabon kuka, sai Munaya ta tafi da ita, haka Munaya ta fito daga gidan, tana jin sautin kukan tilon kanwar ta har ranta, amma bata da zabi daya wuce fitan, fatan ta dai Allah yasa yau tayi dace da samun aiki...

****

Da ace ƙarfin iko, kudi, da duk wani ababen more rayuwa yana hannu ko wani ruhi, tabbas da ta fi kowane ɗan adam abubuwan data lissafa ko dan su huta daga kyara da suke fuskanta a wajen mutane, sai dai shi arziki riga ne, wanda Allah yaso shi zai sanya wa,  daga lokacin data yi wayo ta fahimci mafi  yawan mutanen duniya sun fi daraja masu abin duniya ta ji ta kwadaitu da ta zama mai kuɗi,  ba wai dan a daraja ta ba, a'a saboda ta iya dauke duk wata bukata tasu, babban abinda yasa take son samun kudi saboda lalurar tilon kanwar ta, numfashi ta sauke, kana a gajiye ta zauna kan wani dakali dake gefen hanya, ta cigaba da sauke numfashi  a karo na ba adadi sakamakon tafiyar data sha, domin tun safe data bar gida a yawon neman aiki take amma bata dace ba, ita bata matsa ba ko goge-goge da share-share ta samu zata yi.

MunayaMaleek Where stories live. Discover now