chapter 6

63 6 2
                                    

🍇MunayaMaleek 🍓


_by NoorEemaan_📚✍️

Vi...
(6)

Numfashi ta sauke a lokacin data ga likita ne ke tsaye a kofar gidan su, ta taka a nutse zuwa gaban likitan wanda ya ke tsaye kusa da motar sa ya kafe kofar fitowa da ido, da alama sumayin fitowar ta yake.

A sanyaye tace "ina yini" bayan ta isa gareshi.
Cikin sigar wasa yace "Bazan amsa ba, bayan ko sunana ba ki sani ba"
Munaya ta dago fararren idanun ta da Yawan kukan da take yasa ya rine  ta zuba wa doctor, Da ace a lokacin baya ne, da a ce Amnah'n ta na raye da tayi dariya daya ce hakan, sai dai a yanzu farin cikin ta yayi kaura ba kuma ta san yaushe zai dawo ba, tayi kasa da kanta tana murza sirarran yatsun ta.
Doctor kuwa ya fahimci yanayin ta, ya kuma mata Uzuri yasan is not easy manta abu irin wannan musamman ita da akwai shakuwa tsakanin ta da kanwar ta, ya mata Uzuri, amma yana son ya zama silar rage mata damuwa, domin a kallo daya ya mata ya hango tarin ramar da ta yi, ya kuma san har da zaman kadaici ke kara mata damuwa, ya saki ajiyar zuciya a bayyane yace "ya karin hakurin mu?"
Munaya taji kuka na son kufce mata, ta daure tace "alhamdulillah!"
Doctor ya kara cewa "Allah ya jikan ta da Rahama, Allah yasa mutuwa ta zamo hutu a gare ta"
Munaya ta kasa amsa wa, kukan da take kokarin rike wa ya kufce mata, ta saka hijab dinta ta rufe fuskar ta dashi...

Likita ya rufe idanun sa yana yana jin yanda sheshekar kukan ta ke fita na taba zuciyar sa, ya bude idanun sa yace "ooh Munaya kuka kuma? Ki hakuri, Amnah bata bukatar kuka a yanzu, addu'a kadai take bukata daga garemu, kiyi hakuri Please"

Munaya ta shiga jinjina kanta yayin da ta saka hannun ta innocently tana goge fuskar ta.

Tsawon mintuna uku suna a haka kana doctor yace "daman na zo ne domin mu yi magana sosai Ni dake, sai dai har Yanzu na ga You re not your self, so zan bari next idan na zo sai muyi maganar"

Munaya ta jinjina masa kai alamun "toh" ya bude seat din bayan motar sa ya fito da ledoji guda biyu  ya mika mata na farkon mai dauke da tambarin *amrish delicious snacks* yace " ga wannan kayan kwalama ne na taho Miki da shi" Munaya ta girgiza kai hadi da cewa "Nagode"
Ya bata rai sosai yace "ai ba roko na kika yi ba, kuma in dai Kin dauke ni yayan ki kamar yanda na dauke ki kanwata toh ki karba" ya karasa hadi da mika mata ledar... Bata da kuzarin jayayya da mutum a halin da take ciki hakan yasa bata ƙara cewa komai ba.
Ya mika mata dayan leda da fadin "wannan kuma kudin ki ne wanda kika bari a office dina"
Kirjin Munaya ya buga sosai a lokacin data yi tozali da ledar data zuba kudin asibitin Amnah a ciki, taji tamkar an fama mata ciwon da ke ranta, ta daure ta karbi ledar tana jin wani tukuki a ranta, ta juya a sanyaye ta nufi cikin gidan, tana daf da shiga gidan ta ji Muryar likita yace "amma Munaya ina kika samu kudi mai yawa haka cikin kankanin lokaci?"
Wani murmushi daya fi kuka ciwo ta saki, hawayen da take ƙoƙarin rikewa suka balle mata, ba tare da ta juyo ba tace "i sold my virginity doctor,  budurcina  na siyar domin samawa Amnah lafiya, soyayyar kanwata ya rufe min ido har na manta cewa Allah shi ke rayawa ya kuma kashe, tsananin son da nake wa Amnah  da kuma burin ganin ta rayu dani yasa na manta cewa babu wanda ya isa ya samawa bawa lafiya fa ce Ubangijin daya hallice shi, i so much hate my self, na tsani kaina doctor, ina kuma rokon Allah ya yafe min laifin dana aikata" Munaya ta karasa cikin kukan mai karfin sauti daya taho mata kana ta nufi cikin gidan da gudu. Bata da kowa, babu Wanda zata fadawa damuwar ta domin taji sauki a ranta, amma a Yau data samu ta fadi wani abu, she felt a bit relieved. Sannan bazata iya masa karya ba, toh karyar me zata yi da zata gamsar da shi dalilin samun kudi har 3.9m a cikin abinda bai fi awa biyu ba?.

Doctor ya fi mintuna goma a tsaye cikin matukar mamaki, lallai bai taba jin abinda ya daga masa hankali irin abinda Munaya ta fada masa ba, yaji ransa ya kai kololuwa a ɓaci, yana jin tamkar kanwar sa ta jini ce abin nan ya faru da ita, a fusace ya shiga motar sa ya tayar ya bar layin.

MunayaMaleek Where stories live. Discover now