Chapter 3

93 5 2
                                    

🍇MunayaMaleek🍓


_by NoorEemaan📚✍️_

iii
(3)

*MALEEK*
Bayan ya gama aikin da bai samu karasa wa a office ya rufe system din sa hadi da ture shi gefe, ya kwanta rigingine, yana fatan bacci ya dauke shi, amma ya san baccin bazai zo ba, domin duk daren duniya ya kan so yayi bacci, kamar yadda ko wani dan adam ke yi, amma hakan baya yuwa, saboda an riga an raine shi da Barasa tun yana dan shekara uku a duniya, har ya girma ya fara nema da kan sa, har ya zamana he's so addicted to it da idan bai sha ta duk dare kafin ya kwanta ba, ya kan ji kamar ya haukace.

Kamar yanzu yana kwance idanunsa tarr babu alamun bacci, duk da kasancewar yanzu karfe biyun dare, ya mike kamar an tsikare shi ya nufi wardrobe din sa ya bude ya dauko wani box madaidaici, ya dawo bakin gado ya zauna, ya daura box din a cinyarsa ya danna wasu numbers, dan akwatin sirrin sa ya bude, take kananun kwalabe masu ɗauke da giya suka bayyana, ya mika hannu ya dauki guda daya mai suna *Mr dowell's whiskey* ya kafa baki ya shanye duka, sannan ya kara daukan Wani ya shanye, take idanun sa suka kada suka yi jajur, ya rufe dan akwatin kana ya mike ya mayar da shi cikin wardrobe ya dawo ya kwanta rub da ciki, ya lumshe kyawawa kuma rikitatun idanun sa, cikin abinda bai fi mintuna biyar ba bacci ya dauke shi.

***

*MUNAYA*

_5:30am_

Abu mai dumi data ji ya zuba a kirjin ta, ya ratsa ta rigar ta har ya taba fatar ta shi yayi sanadiyar tashin ta daga baccin daya dan dauke ta.

"Amnah!" Ta faɗa cikin sauri ganin tana amai sosai, sai dai zallar ruwa take amayar wa, Amma ta kasa ko da motsi, saboda mutuwar jiki, sai aman dake fita a bakin ta, ta tashi da ita a jikin ta cikin sauri, ta jinginar da ita jikin gini, Amnah ta tafi luuu zata kwanta domin babu kwari a jikin ta ko daya, Munaya tayi saurin tareta ta kwantar da ita, kana cikin sauri ta fita zuwa tsakar gida ta dauro alwala ta dawo cikin daki ta sanja kayan jikin ta, ta yi saurin tada sallah, tana jin yanda amnah ke fitar da nunfashi da kyar, sam ba a nutse tayi sallar ba, ko azkhar bata iya yi ba, ta saka ɗaya daga cikin hijab din ta data siya, ta lalubo wa Amnah atamfa doguwar riga daya kode ta sanya mata, kana ta dauki ragowar kuɗin da Shakur ya bata dubu goma sha huɗu ta dauki Amnah rungume a jikin ta, cikin sauri ta fito daga gidan, ko rufe kofar langa langan su da kusan rabi ya cire daga bango bata yi ba saboda sauri, burinta ta kai Amnah asibiti, domin jikin kara rikicewa yake a ko wani dakika daya na agogo, gudu-gudu sauri-sauri, ta dinga tafiya har ta iso bakin titi, ta ga babu wasu ababen hawa, kasancewar garin bai ida wayewa ba gashi lokacin sanyi ne, ta tsaya har na mintuna biyar bata samu ba abin hawa ba , sai ta fara tafiya cikin sauri, tana yi tana kallon fuskar Amnah da yayi fayau, idanunta sun shige ciki sosai, ramar ta ya fito muraran, kiris ya rage basu zube a kasa ba, sakamakon kallon da take wa Amnah, ta yi saurin jan tunga ta tsaya, ta cigaba da tafiya tana waigen bayan ta ko zata ga abin hawa, ta ɗan jima tana tafiya sannan ta ji dan sahu na mata horn daga baya tayi saurin juyowa, ta shige dan sahun, cikin rikicewa, fuskar ta a kacame da hawaye tace "muje asibiti ɗan Allah"
mai dan tsahu yace "wani asibiti?" ta kira sunan asibitin da Umma ke kai Amnah ya ja suka tafi, mintuna daya biyu ta kira sunan Amnah, amma shiru ba amsa, Munaya na tsoro, tsoron rasa tilon kanwar ta, bata son rasa Amnah, kaf duniya ita kadai ta rage mata, ita ce sanyin idaniyar ta, Amnah bata ko iya magana, sai numfashin ta dake fita da sauri tamkar zai fasa dan kirjin ta ya fito, sai juyi take a jikin Munaya alamun tana cikin zafin ciwo, wanda hakan ke saka kirjin Munaya lugudan bugu.

"Mun iso asibitin" mai dan sahu ya fada yana waiwayo ta, cikin sauri Munaya ta sauka, ta bashi dubu daya cikin kudin dake hannun ta, ya girgiza kai da cewa "ki barshi, Allah ya bata lafiya" ta kasa ko da magana balle godiya, ta yi cikin asibitin da gudu, mai dan sahu ya girgiza kan sa, tayi matukar bashi tausayi, domin ya hango damuwa mai tarin yawa a tare da ita, a bayyane yace "ko ina iyayenta suka bar karamar yarinya da wanna wahalar, domin ko shakka babu wanna yarinyar bazata iya haifar mara lafiyan ba" ya sake Girgiza kai, yana tada Babur din sa, ya Kuma gode wa Allah daya wadata shi da lafiya, Domin idan kana tunanin kana cikin halin kunci ko kana fuskantar wani kalubalen rayuwa, toh idan ka ga wanda kafi sai kayi godiya ga Allah da yayi maka wanna ni'imar, ba dan kafi wasu ba,sai dai ko wani bawa da tashi kalar ƙaddarar.
Cikin asibitin kuwa a gagauce suka karbi Amnah, aka mata fixing drip, domin babu karfi ko daya a jikin ta, Munaya na gefe tana kuka sosai, bayan likita ya gama duk wani abu daya dace yayi wa Amnah ya juyo ga Munaya yace "ina maman ku?"

MunayaMaleek Where stories live. Discover now