chapter 8

62 5 0
                                    

🍇MunayaMaleek🍓


_By NoorEemaan_📚✍️

Wattpad: NoorEemaan
Arewabooks: nooreemaan

xiii
(8)

Munaya da tunda ya matso kusa da ita taji kamshin turaren sa na hawan mata kai, ta dinga jin tashin zuciya, sai dai ta cigaba da daurewa, a gefe daya kuma tana mamaki, domin ita din ma'abociyar son kamshi ce, duk da bata taba samun kuɗin mallakar turare na kan ta ba, amma tana son jin kamshi ko da wani ne ya saka, ta cigaba da daurewa yayinda take jin jiri jiri tamkar zata fadi, sai dai yana kai karshen maganar sa ta ji amai ya taho mata, ta yi saurin durkusawa bakin kwatan dake wajen tana kwarara amai sosai... Gabanta yayi mummunar bugawa a lokacin da take ƙoƙarin tuno wani abu, sai dai jirin da take gani yasa ta kasa haɗa tunanin ta waje daya. Bugun zuciyar ta ya cigaba da karuwa, murya a mugun raunane ta samu hada kalmar "Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un"  ta karasa wasu hawaye masu zafi na biyo kuncin ta...
Doctor Abbas da hankalinsa ke tashe yana mata sannu ya yi saurin buɗe motar sa ya dauko mata ruwa hadi da mika mata, Munaya ta kasa karba, gaba-daya komai ya tsaya mata cak, ta rasa abinda ke mata dadi, kana ta rasa wani irin tunanin ya kamata tayi, ta mike a hankali ta juya zuwa cikin gida, taku uku tayi ta ji wani duhu ya gilma ta idanun ta,  wani mugun jiri ya sake dibar ta, ta tafi luuu ta zube, cikin sauri doctor Abbas ya karaso inda take, ya shiga kiran sunan ta "Munaya! Munaya!!" Amma ta gagara amsa wa, hankali a tashe ya dauke ta zuwa wajen motar sa, da hannu daya ya bude murfin motar ya sanya ta a ciki, ya zagayo ya shiga gaban motar ya tayar da ita da saurin gaske ya bar layin, duk bayan seconds biyu sai ya juyo ya kalle ta, maimakon ya nufi asibitin su  sai ya nufi wani asibitin dake kusa sosai,  musamman daya fahimci cewa tana bukatar taimakon gaggawa...
Mintuna biyar kacal ya kawo su asibitin, ya dauke ta cikin sauri ya nufi cikin asibitin, nurses dake kan duty suka yi saurin karban ta, sannan ya nuna musu ID card din sa,  hakan yasa suka bar shi ya shiga, sosai likitan asibitin ya shiga duba Munaya, tsawon mintuna sittin ana abu daya, domin har test ya yi mata running domin ya fahimci matsalar ta kana a ƙarshe ya daura mata drip domin babu karfi ko digo a jikin ta, yana mikawa nurses kayan da yayi amfani da su ya kalli doctor Abbas yace "see me in my office doctor" ya karasa hadi da ficewa, doctor Abbas ya bi Munaya da kallo, sosai zuciyar sa ta karye, ba sai an fada wa mutum ba kallo daya za a mata a fahimci tana cikin halin rayuwa, numfashi ya sauke, yana fatan Allah ya sa ba wata Matsala ce babban ke damun ta ba...
  
"Ban san ya kuke da yarinyar daka kawo ba, may be your sister, neither your wife, ba hurumina bane lallai sai na sani, i won't say anything much tunda kai likita ne, You re already
into the system ka san komai, that girl is in a critical condition, nayi mamaki sosai da har karamar yarinya kamar ta jininta ya hau har haka, sannan the worst part is she's 6weeks pregnant, banason shiga hurumin da ba nawa ba, amma yarinyar nan tayi kankanta da haihuwa gaskiya...." Ya dan yin shiru kamar mai tunanin Wani abu sai kuma ya kara da cewa "any way ga drug's da za a siya mata" ya kai karshen maganar da rubuta masa magunguna.

Doctor Abbas was so speechless at first, ko kusa bai taba kawo hakan a ransa ba, Banda innalillahi babu abinda yake maimaita cikin ransa, sosai maganganun likitan suka dake sa, tausayin Munaya mai yawa ya sake rufe shi, yasan Munaya tayi wauta, ta kuma yi kuskure da laifi mai yawa, amma ya mata uzuri, musamman idan aka yi duba da karancin shekaru ta, ya mike a sanyaye ya fice zuwa siyo mata maganin.

_WASHEGARI_
A hankali ta fara bude idanunta da suka bata awanin a rufe, a kallo daya da ta yi wa inda take kwance ta fahimci asibiti ne, komai daya faru da ita a jiyan ya shiga dawo mata, bugun kirjin ta ya fara bada sautin dim! dim! dim! Har tana jiyo sautin sa tamkar zai fasa kirjin ta ya fito, hawaye suka zubo mata, can kasan makoshi ta furta "ya Allah kasa ba abinda nake tunani bane, ya Allah ka yafe min na tubaaa!" Ta karasa wanna karon cikin dan karfin sauti yayinda ta fashe da kuka....

MunayaMaleek Donde viven las historias. Descúbrelo ahora