chapter 2

105 2 0
                                    

🍇MunayaMaleek🍓

_by NoorEemaan_📚✍️

ii
(2)

Kankame jikin ta tayi waje daya cikin tsananin tsoro. "Maleek!" Shakur ɗaya shigo yanzu ya yi hanzarin kiran shi, hakan kuma ya hana Maleek isa wajen Munaya da niyyar huce haushin sa, domin ya ki jinin kazan ta, sam baya kaunar ganin datti, ya kuma lura yarinyar nan is fun of abinda baya so.

A zafafe ya juyo ga Shakur yace "kaga abinda ka janyo ko? You see what I'm telling you"

"Relax Maleek, calm down please" Shakur ya fada yana dan bubbuga kafadun sa.

Cikin bacin rai Maleek ya cire hannun Shakur yace "don't tell me to calm down, who knows ko ta zuba min infection da germs a toilet"

Shakur  ya juyo ga Munaya da jikin ta ke rawa yace "meyasa kika shigar masa toilet?"

"Al...alwal alwala na shiga yi"  tace Cikin k'ak'arwan murya.

Ya Girgiza kai, sanna ya taka zuwa cikin toilet din ya danna wani madanni yayi flushing fitsarin da ta yi, sannan ya fito, ya nufi wajen tebur din Maleek ya dauki *pager* Wanda wireless telecommunications ne da aka yi connecting da loudspeaker, musamman an tanade shi Domin sanarwa ma'aikata wani abu, a maimakon a je kiran wani. "The cleaner to the CEO's office, the cleaner to the CEO's office urgently" Shakur ya faɗa kana ya ajiye telephone din.
Munaya da ta ji yanda Muryar Shakur ya karade ko ina tayi wiki wiki da ido, kanta a kasa ko dagowa ta kasa yi.

Mintuna biyu kacal ma'aikaci mai sanye da fararren kaya ya shigo dauke da mopping stick da mopping bucket ya shiga aikin sa, shakur kalli Munaya yace "biyo ni na nuna miki wajen sallah" kafar ta na hardewa ta bi shi, yayinda take jin idanun Maleek na bin ta da kallo na wulakanci da idanun sa masu kaifi"

***

"Kin ji aikin da nace zaki dinga masa ko? don't cross your limit ki kula,  Zaki zo karfe  tara na safe ki tashi hudu na yamma, albashin ki dubu talatin da biyar duk wata"

Cikin farin ciki mara mistaltuwa Munaya ta washe jerarrun haƙoran ta, sosai taji dadin samun wanna aikin, ko aikin dubu goma bata taɓa saka ran samu ba, amma gashi Allah ya dube ta, ya Mata fiye da abinda ta saka ran samu.

Ta saci kallon Maleek dake danna system cikin kwarewa fuskar sa a dinke tsaf, har ranta ta so Shakur zata yi wa aiki, domin Maleek kam na bata tsoro, musamman kallon da yake mata a duk lokacin da suka haɗa ido, tana hango rashin haɗuwar jini ko tace tsanar ta a idanun sa, amma zata yi matukar kokarin ta wajen kiyaye abinda zai sa ya kara jin haushin ta, ko yasa ta rasa aikin ta.

" Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Munaya ta faɗa tana dan rissinawa.

"Ameen ga wanna, ki samu wasu kayan ki siya saboda zuwa aiki, always look good and neat" Shakur ya fada yana mika mata kudin

"Thank you, Allah ya saka maka da gidan aljanna" ta faɗa wasu kwallan dad'i na zubo mata, wanna shine karon farko data fara rike kuɗi masu yawa a rayuwar ta.

"Zaki iya tafiya, but make sure kin yi resuming aiki at 9:00am gobe"

"In Sha Allah, Nagode sosai" ta ce tana barin office din domin zuwa gida.

"Mtsss, i don't think zan iya aiken yarinyar nan ko ina, zan dai bar ta  ne saboda farin cikin ka, amma maganar gaskiya, bana son ganin ta" Maleek ya fada cikin iyakar gaskiyar sa.

"Tana da shiga rai, You will like her One day, zaka ce na fada maka Maleek"

Maleek ya dago kansa ya zabga masa harara, Shakur ya kwashe da dariya.

***
*MUNAYA*

Cikin kuzari data rasa rabon data samu irin sa tayi sallama cikin gidan su, hoping to see Amnah ta zo yi mata oyoyo, amma shiru, ta kara yin sallama, ta nufi dakin su, nan ta tarar da Amnah a kwance, cikin sauri ta karasa wajen ta, tace "Amnah! Amnah!!"
Cikin zafin ciwo Amnah ta fara lalube da hannun ta har ta taɓa fuskar Munaya kasancewar idanun ta na lumshe ne. "Muna, kaina ciwo sosai"

MunayaMaleek Where stories live. Discover now