🍇MunayaMaleek🍓
_by NoorEemaan_📚✍️
All my books are available a waɗandanan platforms din, usernames are:
Wattpad @NoorEemaan
Arewa books:nooreemaan
Please follow me, and also vote my stories, thank you.❤️ix....
(9)*Su waye MunayaMaleek?*
*Menene Tarihin Rayuwar MunayaMaleek*?
_Let's find out.!__Abuja_
*Unguwar Masaka*Unguwa ce ghetto, amma akwai manyan gine-gine a cikin ta, a takaice dai unguwar ta hada da talaka da masu hannu da shuni.
Alhaji Dawood Bulama na daya daga cikin masu hannu da shuni a unguwar, domin gidan sa shine gida mafi kyawu da girma a unguwar, yana da arziki domin harkar man fetur yake, wanda ya gaji sana'ar ne a wurin mahaifin sa, yana da gidajen mai guda hudu a yanzu haka mai suna *Dawood and son's Nig LTD* duk da wanna arzikin nasa, wanda zai iya yin, ko siyan gida a unguwar zallar masu kuɗi, amma hakan bai sa ya bar ghetto ba, domin shi Mutum ne mai son zama cikin jama'a sosai, ya kan ce jama'a rahama ne.
Asalin sa ɗan nan garin Abuja ne, wato yan *Gbagyi* wanda Hausawa ke ce masu *Gwari* asalin su a nan Abuja yake, kuma yan Gbagyi ko nace yan Gwari sun fi ko wanne kabila yawa a Abuja domin nan din nan asalin su, kuma tushen su, sai yan kabilar *koro* wanda su ma ba laifi suna da dan yawa, da kuma sauran wasu kabilu. Iyayen sa sun rasu, yana da yayye biyu Laraba da Isma'il inda shine ya kasance Auta.
Sai dai Alhaji Dawood har yanzu bai yi aure ba, dangi kuwa sun gaji da magana sun zuba masa ido, Shi kansa yana son yin aure, amma ya kasance irin namijin da bai san yanda zai tunkari mace da sunan yana so ba, gashi bashi da isasshen lokaci na kansa.A yau juma'a yake kai ziyara wa yan'uwansa, domin mutum ne mai zumunci, duk da bashi da isasshen lokaci, amma da zarar da samu lokaci komai kankantar sa yana Amfani da ita domin samun lada, gidan yayar sa laraba ya fara zuwa inda take aure a unguwar Gwarinpa, bayan y'a'yan ta sun gama murnar ganin sa, yaya Laraba ta gabatar masa da abin motsa baki yayi godiya, sai ta fara masa zancen dake cin ta cikin Yarensu na Gbagyi "yanzu Dawooda haka zaka cigaba da zama, ba zaka yi aure ba, bar ganin kana da tarin dukiya, ba fata ba, ace a yau ka fadi ka mutum bayan an gama jimamin mutuwar ka Labarin ka zai gushe na har abada, sai dai mu yanuwanka na jiki ne bazamu manta ka ba, amma idan kana da ƴaƴa, a duk lokacin da wani da ya san ka ya ga yaran zai ce Allah Sarki Rayuwa, ga ƴayan Dawooda nan, Allah ya jikan sa, haka zalika y'ay'anka zasu na maka addu'a, amma idan babu y'a'yan fa, saurin mantawa za a yi da kai, shin Kanina bazaka so ƴay'anka su maka addu'ar samun rahamar Ubangiji ba?" Shiru yayi, jikin sa yayi sanyi sosai, tabbas it's about time daya kamata yayi aure, amma wa zai aura? Shi bai taba soyayya ba, ya budi baki zai yi magana, sallamar wata budurwa ya karade kunnuwan su, ba tare da ta jira ba ta dage labulan falon ta shigo, domin gidan ba bakon ta bane, cak ta tsaya, sakamakon kyakkyawan mutumin data gani zaune, saurin juyawa tayi da gudu ta bar falon, domin bata san maman Abdallah (yaya Laraba) ta yi bako ba.
Cikin mamakin abinda budurwar tayi, da kuma dariyar da yaya Laraba ke yi daya kara masa mamaki, hakan yasa ya gyara zaman sa yace
"wacece ita, kuma me yasa ta koma yaya?"Yaya Laraba ta dakatar da dariyar da take yi, tace "sunan ta Bilikisu, gidan su ne yake kallon namu, marainya ce, mahaifiyar ta ta rasu, kishiyar maman ta ke cigaba da kula da ita da nata y'a'yan, yarinyar kirki ce, su Abdallah ma sun saba da ita sosai, kunyar ka ta ji, bata san kana nan ba da bazata shigo ba, shiyasa kaga ta gudu"
Numfashi ya sauke bayan ya gama sauraran yayar tasa, ya shiga shawara da zuciyar sa, can kuma ya ce " yaya Laraba na baki zabi, ki min Mata"
Yaya Laraba ta washe baki cikin jin dadin tace "Madallah Dawooda, kamar yadda ka bani zabi, bazan baka kunya ba, Zaka yi farin cikin da zabi na, Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
" Ameen" ya amsa fuskar sa babu yabo babu fallasa.

YOU ARE READING
MunayaMaleek
General Fictionread MunayaMaleek, for you will gonna fell in love with it, saboda tsananin soyyaayar ta ga kanwar ta yar shekara shida mai lalurar brain Cancer ta siyar da budurcin ta, Sai dai ta manta cewa Allah ke rayawa, ya kuma kashe a sanda ya so, Me zai faru...