chapter 16

217 6 1
                                    

🍇MunayaMaleek🍓

𝓫𝔂 𝓝𝓸𝓸𝓻𝓔𝓮𝓶𝓪𝓪𝓷📚✍️

Wattpad@NoorEemaan
Arewabooks: nooreemaan


Xvi...
(16)

"Dan Allah ka saurare ni, na san an cuci Munaya, cuta mafi muni, ka fada min inda take, wallahi muna neman ta, tun ranar data dawo da kuɗin nan muke neman ta, but she's no where to be found, karka duba zafin abinda dan'uwana yayi, saboda Allah ka nuna min inda take, na dade ina neman ta domin in bata hakuri,  but trust me brother dina baya cikin hankalin sa ya aikata abinda yayi da ita wallahi, You may not believe" doctor abbas ya kara jinjina sauki kai da sanyin hali irin na Shakur, domin sam daukaka ko arzikin su bai rufe masa ido ba , yayinda haushin Maleek ya cika shi, ganin ko kala mai bai ce ba bare bada hakuri, shi  da yayi laifi amma ya kasa bada hakuri sai wanda ba ruwan sa ne ya damu, ya lura Shakur na matukar son dan'uwan sa sosai, ba kuma zai yarda cewa Maleek baya hayyacin sa ya keta wa Munaya haddi ba, mahaukaci ne da shi da bai san abinda yake ba ko mene, kawai ya yarda da abinda Hausawa suka ce so so ne amma son kai yafi yawa.

"I don't think zaka samu Ganin ta yanzu, domin bata ma san nazo nan ba,  tace bata bukatar ganin dan'uwan ka, ni kaina bana son  ciwon ta ya tashi...." Doctor Abbas ya kara maimaitawa domin yana son ran Maleek ya ƙara ɓaci.
Cikin sauri Shakur ya katse shi da cewa "ni zaka kai, nice nake son ganin ta Please"

Numfashi Abbas ya sauke, mutuncin Shakur ya saka yake kasa yi masa musu, ya ce "zaka ganta but not today, lemme have your contact, zan mata bayani first, idan na ga babu tashin hankali sosai a tare da ita zan kira ka muje gidan na su" cikin sauri Shakur ya shiga karanta masa lambar wayar sa, sannan suka yi musabaha, Shakur ya jaddada masa cewa ya kira shi ɗan Allah, kallon daya doctor Abbas ya kara watsawa Maleek mai cike da jin haushi hadi da kishi kana ya fita.

Bayan fitar doctor Abbas Shakur ya kalli Maleek dake tsaye har yanzu fuskar nan tayi ja jijiyoyin kansa sun fito rudu-rudu, kai tsaye mutum bazai iya fassara yanayin na sa, a zahiri Shakur ya fishi shiga damuwa sai dai from the inside, Maleek kadai ya san abinda yake ji, tsabar jarumta ce irin ta sa.

" You kept quiet, You didn't say anything Maleek, meke damun ka ne, ka san irin tawayar da ka yi wa yarinyar nan kuwa,, and yet ka yi shiru baka ce komai ba, duk abubuwan nan sun faru amma ka zabi boye min wasu daga ciki sai yanxu nake ji, na kasa yarda dan'uwana ya aikata wanna munana ayyukan, Maleek what came over you?"

"Is that why kake bashi hakuri? meyasa zaka bashi hakuri, who is he da zai zo ya fadi abinda ya ga dama wa mutane, yaje ya kai maganar duk inda zai kai, i don't bloody care!"

Tsabar haushi Shakur ya dauki ƙwallin serviette   dake kan table ya jefi Maleek da shi ya daki kirjin sa, a fusace ya isa gareshi yace "You still have mouth to talk huh? Kana da bakin magana bayan tarin rauni da tawaya da ka yi wa diyar mutane, dan ka ga bata da kowa ko me, toh ka sani in dai maganar nan yaje kotu i will back Munaya, ko kana tunanin dan kana jinina zan goyi bayan karya, no i won't, da kuma dukiyar ka zan diba in bi mata hakkin ta"

Idanun Maleek suka sake kadawa, yace "You know I'm not afraid of anything in this world right, ko ina zaku kai ni ka san bana jin tsoron komai, ba kuma zan fara kan wannan maganar ba"

"Eh na san cewa zuciyar dutse ce dakai baka shakkar komai, amma ka shirya yi wa mummy da Daddy bayani? Ni ne na yarda da cewa baka cikin hayyacin ka kayi wa Munaya haka, kana tunanin kowa zai yarda da hakan? Huh tell me" Shakur ya faɗa kamar zai kai mishi duka.

"Tun ranar farko da yarinyar nan ta shigo rayuwar mu na san ba alkhairi a tare da ita,  gashi ta haɗa mu fada, abinda Bama yi, raina ya sosu da har za ka bar ni jininka ka goya wa wata can baya, taya bazan tsani yarinyar nan ba? kamar yadda ta tsane ni, haka nima i hate her, more than she does" yana gama fadin haka ya fice daga office din domin har an fara kiran magrib, basu taba kaiwa wanna lokacin a office ba, Shakur ya ɗan ji ba dad'i, musamman kalaman Maleek din ya ɗan saka jikin sa yin sanyi, shi ma ya san fadi yake kawai, tabbas bazai bari Munaya ta Cutu ba, ba kuma zai bar gefen dan'uwan sa ba, tun yarinta suna tare, ba kuma zasu rabu ba sai mutuwa in sha Allah"
A sanyaye ya fita shima yana fatan Allah ya warware musuz matsalolin su.

MunayaMaleek Where stories live. Discover now