chapter 7

82 6 0
                                    

🍇MunayaMaleek🍓

_by NoorEemaan_📚✍️

Wattpad@NoorEemaan
Arewabooks@nooreemaan

https://www.facebook.com/groups/1346404966270527/?ref=share_group_link
(Kuyi following sabon account dina please)

https://whatsapp.com/channel/0029Va5o0Gc4o7qU8MCJuN32
(Follow my WhatsApp channel domin samun update )

*Gaisuwa ta musamman zuwa ga makarantar NoorEemaan, bazan iya rubuta yawan ku ba, amma ina muku son so*❤️

Vii
(7)

A ranar da Munaya ta sanar da likita cewa budurcin ta ta siyar Kafin ta samu makud'an kuɗaɗen nan bai runtsa ba, sosai zuciyar sa ke kuna tamkar ciki daya suka fito da ita, a ransa kuma yana ji tamkar har da laifin sa yasa hakan ta faru, a matsayin sa na likita ya kamata yayi la'akari da cewa Munaya karamar yarinya ce, bai kamata kai tsaye ya sanar Mata cewa komai zai iya faruwa da Amnah idan ba'a yi saurin yi mata aikin ba, yana ji a ransa cewa har da kalaman sa gareta yasa ta tsorata har tayi saurin bada budurcin ta, Amma  yanzu ya ɗauki darasi a rayuwa, zai kiyaye yanda zai yiwa duk  wanda ya Kawo patient magana da ma patient ɗin, zai kwantar musu da hankali ko da yasan cewa shi Mara lafiyar na dab da rasa ransa, ko dan gudun abinda ya faru da munaya ya sake faruwa ga wata, kila daya kwantar wa Munaya hankali duk da halin da kanwar ta ke ciki na halin rai ko mutuwa da kila bata rasa abubuwa biyu masu matukar muhimmanci a rayuwar ta ba, da kila ta tsira da daya, amma abin ciwo da takaicin, babu Amnah, Babu budurcin Munaya! Ya sake juyi kan gadon sa cikin damuwa, yana ji kamar yaga mara imanin daya aikatawa Munaya haka da tabbas sai inda karfin sa ya kare, qwarai abin ya tsaya masa a zuciya.

***
Bangaren Maleek kuwa tun bayan da suka dawo daga neman Munaya ya rasa meke damun sa, mintina daya zuwa biyu tunanin ta ya fado masa rai, sai dai ya alakanta hakan da managar da Munaya ta faɗa masa bayan ta watsa masa 3.9 million din sa, yayi tunanin zata dawo aikin bayan wasu kwanakin zuwa goma haka amma sai ya ga lokaci na dada ja ba tare da ko mai kamaninta ya gani ba, shi dai yasan bai bata muhimmanci ba saboda ita din ba komai bace a gareshi, kawai yana takaicin abinda ya aikata da karamar yarinyar da take basa kyama, sai kuma maganar mutuwar yarinyar (Amnah) da ya dake sa sosai, sai yake jin wani *quilty conscience*, bai taba nadamar shan giya ba sai ranar daya kusanci Munaya cikin maye, ko da  yana cikin maye shi din tsayayyen namiji ba,  sai dai bai san abinda yasa a ranar ya kasa controlling  kansa ba har ya afka mata, ya mike tsaye  hannun sa sanye cikin aljihu ya taka zuwa ga dogon window'n glass din office din, tarr yake ganin mutanen da suke wucewa kan ababen hawa da masu haɗa haɗar su cikin kwanciyar hankali, ya jima a tsaye idanun sa a wajen yana kallo, sai dai ba kallon yake ba, yayi nisa a tunani ne, sai daya bata lokaci tsaye a wajen kana ya dawo ya zauna kan kujerar sa, can kuma kamar an tsikare shi ya mike zuwa dakin hutun sa ya shiga, tun ranar da abin nan ya faru ya daina barin masu aiki shiga Wajen, daya tashi zai rufe kofar da kansa, yana shiga jinin daya bata farin sofan na nan bai goge ba, ya sauke  idanun sa masu rikitarwa kan sofan yana kallo, ya dauke idanunsa daga kallon jinin ya sauke kan mataciyyar ribbon din ta daya tsufa sosai ya ga har da silin dogon gashin ta daya manne da ribbon din, ya dauke idanunsa daga nan ya zauna kan kujera, ya dawo da cctv Cameran baya zuwa ranar da abin nan ya faru, ya dinga kalla daya bayan daya, sai dai daya zo kan inda komai ya kankama sai ya yi saurin kashe wa, domin haushin kansa yake ji, he hate his self for what he did, Sam baya nadamar zinar daya aikata, sai haushin kansa da yake ji da aikata hakan da yarinyar da ya tsana, ya furzar ga iska mai dumi daga bakin sa ya shaki kamshin mouth spray ɗin a hancinsa.

***
_8:00pm_

Cikin farin ciki mummy take yau, zata samu cikar burinta, motsa coffeen dake cikin kyakkyawar wani mug take, bayan ta gama ta nufi hanyar dakin ta, ta san Maleek yana shigowa zai shanye coffeen, domin baya wasa da coffee, Shakur ba sha yake ba tunda shi ba masoyin sa bane, yafi ganewa shayi, ta shiga daki ta shirya cikin had'add'en nighty tana jiran sa, domin an tabbatar mata da kansa zai shigo ya neme ta bayan ya shanye.

MunayaMaleek Where stories live. Discover now