01

210 10 0
                                    

*ALHAKI...*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 1.

*Gargad'i*
_Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a ɗaura min shi a wata kafa na media ba tare da izini na ba, dan Allah a kiyaye_

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

BATUL.
A duk lokacin da na tuna mijina Habib sai na ji na fi ko wace mace sa'a a rayuwa, shekararmu huɗu da aure sai dai ban taɓa haihuwa ba, mun je asibiti an tabbatar mana da mahaifata ba tada matsala kawai lokacin haihuwar ne Allah bai kawo ba,  amma saboda ƙaunar da Habib yake yi mini sai bai nuna damuwarsa ba dan shi ne ma ke kwantar mini da hankali a duk lokacin da na soma kukan rashin samun juna biyuna, sannan ya zame mini katangar jingina domin yaƙi bada ƙofar da kannensa zasu raina ni balle su rika yada mini magana, haka ma ɓangaren mahaifiyarsa ta riƙeni tamkar 'yarta bata taɓa nuna mini damuwar ban haihu ba, shiyasa inna duba kaina a kullun nake ganin nayi dace da miji nagari. Habib shine ya tsamoni daga ƙangin talauci ya raya rayuwata na zama mai cikakken 'yanci har ma yan uwana suke raɓar inuwar da Allah yayi mini, duk da ba wani kuɗi yake samu sosai ba amma yana kokarin hidimtawa dangina, saboda Babban shagon ɗinki gareshi, yana ɗinkin maza ne na manyan mutane dan kusan faɗin kaduna an sanshi, kuma shike yiwa 'yan siyasa da wasu manyan 'yan kasuwa ɗinki. Allah yana ƙara buɗa masa sosai saboda kyautatawarsa ga mahaifiyarsa da kuma ni. Dalilin daya saka kenan na ɗauko ƙanwata Hibba dan ta zauna tare da ni a gidana, saboda ina so ta samu karatu mai kyau tayi ilimin zamani dana addini dan ta fita zakka a gidanmu, dan kaf gidanmu babu wanda ya samu karatu mai kyau saboda duk a gantale muka yi shi, babu wanda yayi saukar Al-Qur'ani, boko kuwa wasu a primary suka tsaya wasu kuma j.s, ni da yarinyar Yadikkonmu ne kawai muke da satifiket na kammala sakandiri, shima ba wani ilimi ne damu ba sai yawan talla da niman kuɗi kuma sani, turancin zamani ko zo in kasheka ban sani ba har na gama secondary sai da na auri Habib ne ma ya dage mini akan yana so yaga na waye na iya turanci kodan saboda yaran da zamu haifa nan gaba, shine ya nimo mini wani makarantar koyan turanci dake nan tudun wada na je na koya na shekara guda, ba laifi yanzu kam ina jin turanci duk da ban gama fahimtar fassarar wasu kalmomi ba, wannan yasa na dage Hibba ta dawo hannuna dan bana so tayi rayuwa irin wacce na yi a baya, saboda mahaifiyarmu bata gidanmu dan mu biyu kawai ta haifa Allah ya kawo rabuwarsu da mahaifinmu ya saketa ta koma ƙauyensu Sabo, a can ta ƙara samun miji take aure, ita kanta tana bukatar taimako tunda zaman kauye da bambanci da rayuwar birni, da ina da yadda zanyi da itama na rabota da kauyen ta dawo gidana da zama, sai dai ba ni da ƙarfin yin haka, amma a kullun damuwata na cika mata burinta akan na riƙe Hibba da kyau na inganta rayuwata, dan ta san a wajena ne kaɗai zata samu wannan gatan. Shekara biyu kenan da ta dawo wajena, tana zuwa makarantar boko private mai kyau haɗe da islamiya, yanzu haka tana zana waec exam ne wanda in sun gama za a haɗe walimar fitarsu dana saukar Al-Qur'ani da ta yi, ba ƙaramin shiri nake ba domin naga na fita kunyar mutanen da zan gayyato bikin walimar.

Na sauke gauron numfashi tunawa da wasu ɓangare na rayuwata da nayi, na dafe gefen kaina saboda ciwo da yake yi mini mai tsananin gaske sakamakon gajiyar tafiyar ƙauyen Soba da na kwaso. Biki na je a garin mahaifiyarmu wanda ƙanwarta ce take aurar da ɗiya, na shafe kwana uku a can saboda a gama komai da ni, duk da hankali na yana kan ƙanawata Hibba dana bari ita kaɗai saboda jarabawar waec da ya hana naje tare da ita, taso ta bini dan da kuka muka rabu akan tana jin tsorin kwana ita kaɗai, shiyasa kan na tafi na shiga gidan maƙotanmu wajen Maman Zeena nace dan Allah Zeena ta riƙa shiga wajen Hibba su kwana tare har na dawo saboda shima Habib ya tafi kano baya nan, ta amince sai nayi mata godiya na koma na faɗa wa Hibba, hakan yasa naji ɗan natsuwa muka rabu cikin kewar juna. Habib ya rigani tafiya ma dan da sassafe ya wuce akan wani aiki da yake fafutukar nima dan yana so ya samu aikin gomnati ya haɗa biyu da sana'ar ɗinkinsa saboda hidimomi sunyi masa yawa, shine babba namiji a gidansu sauren ƙannensa mata ne su Uku duk sunyu aure, kuma babansu Allah yayi masa rasuwa, shike kula da duk hidimar gidansu ga kuma nawa hidimar da ya ɗauke na Hibba. Na fesar da iskar bakina na sauka daga Adaidaita-sahun da ya ƙaraso da ni ƙofar gidana, na sallame shi kafin na ɗauki jakar kayana na nufi ƙofa na tura na samu a buɗe hakan ya tabbatar mini da Hibba tana ciki, sai na wuce falonmu na shiga tun daga nan na soma kwalawa Hibba kira dan ta san na dawo, amma naji shuru sai mamaki ne ya kewaye ilahirin farfajiyar zuciyata, dana ga falon a hargitse sai sannan ne naji gabana ya yanke ya faɗi na soma tunanin ko an shigo anyi mana sata ne dan ƙila sun kula da bama nan, tsananin ƙaguwa da son ganin me ya haifar da wannan hargitsin falon namu ya sa na tura ƙofar bedroom ɗina dana gan shi a buɗe na shiga cikin azama. Nan fa na ƙara kurɓar ruwan tashin hankali sa'ilin da na ci karo da Hibba kwance malala a kan tiles ga jini dana gani a saman gado da kuma inda Hibban ke kwance, tuni kwanyata da ke adana sako ta yi caraf da hasashen da zuciyata ta hasko mini, nan take kaina ya yi wani irin juyawa, hankalina in ya yi dubu to ya tashi, gumi ya rufe ni tamkar mai jegon da ta sha turirin ruwan zafi, zuciyata tana wani irin bugu tamkar ta faso ƙirjina nan take na saki ihu na yanke jiki na faɗi, numfashina yana sama yana ƙasa, tashin hankali gobarar gemu! Hawaye mai zafi ya gangaro a kuncina, a daidai lokacin Maman Zeena ta faɗo gidan domin ihuna shine ya sa ta shigowa, tun daga falo nake jin muryarta tana kiran Hibba, amma bata ji an amsa ba lokacin da ta shigo bedroom ɗina a daidai lokacin numfashina ke barin jikina.

ALHAKI...Donde viven las historias. Descúbrelo ahora