02

61 4 0
                                    

*ALHAKI...*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 2.

Suna isa wajen taron Safeena ta fito da farin tabaronta ta saka kana suka nufi cikin hol ɗin, Jamila tana hango su ta bar mutanen da take tare da su ta rugo ta rungume Safeena tana cewa.

Haba besty sai yanzu? Kusan kece kika tsara yadda za ayi taron nan amma sai yanzu zan ganki.

Beb aiki ya rioeni, kin san harka da bank sai hakuri, amma gani nazo dan haka mu je a cigaba da gashi.

Jamila tayi dariya ya kamo hannun Kubura tana cewa.

Me ciki da alama kin kusa kiranmu suna, hop zaki haihu kafin bikina, dan kin san kune amara ƙirjin biki.

Haba zan sauka kan lokacin. Muje ni na samu wajen zama dan ƙafata a rike take.

Cewar Kubura, sai suka ɗunguma suka karasa can gaban hol ɗin Kubura ta samu wajen zama, Jamila kuwa ta kama hannun Safeena suka wuce can wani ɗakin da abinci yake ta nuna mata. Sai wajen biyar da rabi Safeena ta sulale daga hol ɗin ta fito tana duba Kubura da tun ɗazu ta fito tana jiranta, can jikin motarta ta hangota sai tayi azama ta isa ta sameta ta buɗe motar suka shiga, Kubura tana mitar da ta kara minti biyar bata fito ba sai dai ta samu ta wuce, Safeena taja guntun tsaki.

Na fiki gajiya fa ke dai nauyin ciki ke damunki, dan aikin ki bai kai nawa stress ba.

Haka dai zaki ce. Ni dai mu je ki sauke ni a gidana dan Ibrahim yana gabda shigowa kaduna, so nake nayi sauri na haɗa masa juice ɗinsa na birne layar kafin yazo.

Uhum Safeena ta faɗa tana yamutse fuska bata ce komai ba dan sam bata son wannan mallaka da Kubura keyi, gani take duk macen data san kanta tafi ƙarfin niman mallaka, dan ba tada lokacin ɓatawa akan irin wannan shirmen. Sai da suka hau titi sosai kafin ta ɗauko wayarta ta kira Namir, ringing biyu ya ɗauka tana ce masa.

Beb Love gani a hanyar gida zan biya rastaurant nayi mana oder ɗin abinci, yau me kake so na siya maka.

Sakwara miyar agushi sai farfesun naman rago da kunun aya.

Ok ni tuwon shinkafa zan ci. Yau zaka sha local drink kenan?

Eh na gaji da shan na kanti. Nima gani zan fito daga office sai mun a haɗu a gida.

Ok beb love.

Cewar Safeena tana ƙare maganar da yi masa kiss, shima reply ɗin daya yi mata kenan suka aje wayar, Safeena ta ƙara kama kan motar, Kubura ta yi mata wani kallo tana cewa.

Wai ke har yanzu ba kya yin girki Safeena, ya kamata zuwa yanzu ki gane cewar ke cikakkiyar matar aure ce.

Har gobe ba zan fasa oder ɗin abinci ba, dan Namir ya amince mini da haka banga wanda zai sauya mini ra'ayi ba, ke ko bai amince ba wlh ba zan girka ba. Ai malamai suna fadar maza ya kamata su girka su bamu, kuma da gajiyar aiki zanji ko girki, sannan dare ya naniƙeni ya sakar mini wata gajiyar, ke nifa ba a halicceni dan wahala ba.

Da kyau Safeena wlh kina bani mamaki, komai naki daban yake da na sauran mata, wasu suna son su girka su bawa mazansu suci dan su yaba amma ke ko a jikinki, banga laifinki ba dan da Namir bai daure miki gindin yin haka ba ba zaki yi ba, tunda yaron da kika haifa ma kin kasa ɗaukar ɗawainiyarsa ki kula da shi saboda son kai.

Kubura kin matsa mini da yawa wai rayuwarki ko nawa, haba ki sakar mini wuya na tsaki iska mai kyau, Abdul-Kareem ɗana ne kuma yana hannun Momy na ce ita ke kula dashi yadda zata kula dani haka zata yi masa dan haka banga abin ƙorafi ba, hasalima Namir shiya bani damar na kaishi gidanmu ya cigaba da zama can saboda aikina ba zai bani damar kula da shi ba. Bana son irin abin nan da kike mini dan haka fitar mini a mota tunda na kawonki gidanki.

ALHAKI...Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ