06

51 6 2
                                    

*ALHAKI...*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 6.

Habib yana fita daga gidan malam ya wuce ofishin 'yan sanda. Yana isa ya samu Bashir yana nan sai ya shiga har office ɗinsa suka zauna kana suka gaisa, Bashir ya kara yi masa gaisuwar Hibba, kana Habib ya ɗaura da cewa.

Yallaɓai ya maganar bincike ya kwana? an gano wanda yayi wannan aikin kuwa?

Wlh Habib muna kan aiki ne, har yanzu babu wata shaida ko hujja da muka samu, domin na karɓo binciken jinin da muka gani a gidan da likita ya ɗiba domin aga ko na mutum biyu ne amma duk jini ɗaya ya bayar, kuma mun ta tambayi mutanen unguwar tare da binciken ko anga gilmawar wani ya shiga gidan tun dare zuwa safiyar da abin ya faru da Hibba, amma har yanzu ba wani abu da muka fahimta. Wato ka gane ko Habib wanda ya aikata wannan aikin ya daɗe yana tagetin ɗin yin haka shiyasa daya samu damarta ya aikata mata fyaɗen ba tare da ya bar hujja ko kwaya ɗaya ba.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, dan Allah da son annabi ku tsaurara binciken nan, domin kama wanda yayi wa Hibba fyaɗe shine zai saka iyayenta su gane na ɗauki lamarin da muhimmanci su gane cewar basu ne kaɗai suka rasa Hibba ba hatta mu mun ji zafin rashinta, kuma gatan da zamu nuna mata kenan aka kama wanda ya yi mata haka kotu ta hukunta shi.

Gaskiya ne, to sai ku cigaba da sakamu a addu'a Allah ya bamu ikon kama mai lafin.

Habib ya amsa da amin tare da share guntun hawayen da ya ciki masa ido, ya yiwa Bashir sallama ya wuce zuwa gidansu Batul.

*****

Batul.

Tunda su Umman Habib suka zo mama ta sanar dasu zubar jinin da nake yi, Umma tace to in Habib ya zo dole zamu je asibiti a duba a gani, da haka suka yi shuru da zancen muka cigaba da karɓan gaisuwa. Kusan minti talatin da zuwansu Umma sai ga Salamtu ta zo niƙi niƙi da kayana, bayan duk an gaisa ne take ce mini.

Batul ga kayanki nan yaya yace na kawo miki yace zai je wani waje ne ana jiransa da zarar ya gama abinda yake yi zai zo.

To kawai nace mata na shiga duba kayan da zan saka data ajiye akwatin a gabana, na zaro atamfa riga da zani na cire kayan jikina na saka su, abinda ya bani tsoro kayan dana cire duk ya ɓaci da jini, hakan yasa hankalina ya tashi dana gama sanya kayana na zauna ta ɗauko wayata a jakata da aka kawo mini na shiga kiransa amma sai da nayi masa kira sama da biyar bai ɗauka ba hakan yasa naji haushi na soma cewa mama.

Na kira shi bai ɗauka ba, mama ina ganin zamu je asibiti da Inna Kadi tunda akwai kuɗi a hannuna, wlh har yanzu jinin zuba yake yi har ya ɓata mini kayan dana cire yanzu.

To shikenan idan Habib ɗin yazo sai a sanar dashi, Hadiza tashi ki rakata dan bai dace ta zauna da ciwo a jikinta ba.

Salamatu kema tashi ki yi musu rakiya Allah yasa ba wani babbar matsala bace.

Cewar Umma suka amsa da amin sai Salamatu tace.

Umma Aliya ta bisu saboda wlh nayi aikin gidan Batul na gaji.

To ke Aliya sai ki bisu ɗin.

Umma tace kana Aliyar ta miƙe muka fita tare da Inna Kadi, a ƙofar gida muka ga su Baba suna zaman makoki ganin mun fito yasa duk mutanen dake wajen zuba mana ido, na gaishesu tare da ƙara yi musu gaisuwa suka amsa cikin kulawa kana Inna ta miƙa musu gaisuwa itama sai ta daura da cewa Asibiti zamu je saboda bana jin daɗin jikina, suka yi mini fatan samun lafiya sai muka wuce zuwa bakin titi muka hau napep ya wuce damu wani asibitin private dake can sama, dan layi huɗu ke tsakaninmu. Muna isa bamu sha wuyar ganin likita ba saboda ba mutane sosai, nan na bada kuɗi aka siya kati ba jimawa suka ce mu shiga ɗakin likita da suka nuna mana, Inna tace Aliya ta jiramu sai muka shiga mu biyu, dattijo ne Likitan ya dubeni muka gaisa kana ya tambayi matsalar na shiga bashi labari, dana gama sai ya riƙa yi mini wasu tambaya wanda ya shafi jinin al'adata ko nayo ɓatan wata, duk na sanar dashi komai sai ya saka ni na hau wani gado yace zai yi mini scanning, nan ya fara aikinsa Inna tana kalon mu har ya gama sai ya ce na sauka na koma wajen zamana shima ya gama abinda zaiyi ya koma nashi mazaunin, yayi rubuce rubuce kana ya ɗago yana dubanmu ya soma bayani kamar haka.

ALHAKI...Where stories live. Discover now